← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 61

Sashe 9

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amman kuma me yasa in zurfin cikin naka ya tashi har ni da nake mahaifiyar ka, kake boye min."

Kai ya sunkuyar,
"Mamah kiyi hakuri."

"Ni kawai ka fada me ke damun ka."
"Mamah ni ba abinda ke damuna aiki ne kawai."

"Shikenan Sabir, tinda haka ka zaba ai shikenan. Nidai zan ta tayaka da addu'a Allah ya, yaye maka abinda ke damun ka."

"Ameen! Mamah nagode Allah kara girma."
"Ameen! Abincin fa zaka ci yanzu ko sai anjima?"

"Mamah ban dade daci ba, sai dai in anjima."
"To shikenan."

Ya mike yayi dakin sa.

Kanta ta girgiza tana jinjina zurfin cikin Sabir da ko ita, bazai fadawa damuwar sa ba.

Ta dauki a niyyar sashi a addu'a Allah ya yaye masa koma me ke damun sa.

Sabir dan gidan, Alhaji Marzuk ne, da matar sa firdausi, yana aiki a ma'aikatar lafiya ne dake jigawa.

Inda ita kuma matar sa ke aiki a ma'aikatar ilimi. yayan su uku. Biyu mata daya namiji.

Rukkaya ita ce babba wacce, tayi aure a Lagos ya'yan ta uku. Maza biyu daya mace Maryam

Sai me bi mata, Mufidda wacce take, aure a nan kano. Ya'yan ta biyu.

Sai Auta Sabir, wanda yake babban likita a nan asibitin Aminu kano. Yanzu haka an dauki contract ne inda yake lecturing.

Mahaifin Sabir na son Sabir haka ma maman sa da yan uwan sa. Basu da buri sai na suga yayi aure.

Mamah sa tayi, tayi yayi aure yace lokaci ne beyi ba. Ba kalar matan da bata kawo masa ba amman sam ko kallo bai isar sa.

Dan yanzu haka ta bashi lokaci indai bai yadda ba zata hada shi da koma waye.

Zaune suke, da kwalbar giya a gaban su. Wacece in ba Munasha da Bilkis ba.

Aminan juna wanda harkar su take iri daya kuma hali ma iri daya wannan ya kara hada aminan takar tasu.

"Munasha, Jibson ya kawo karar ki, wai kin ki ki bashi hadin kai."

Fuska Munasha ta hade, tare da zukar tabar dake hannun ta.

"Bilkis Amman na fada miki, cewar tin ranar da na hadu da yaron nan duk kan bukata ta da sha'awa ta, ta koma kansa."

"Amman dai nasan kina shan azaba dan kin saba da rayuwa da maza, yanzu nasan kina cikin tashin hankali."

Idanun ta ta dago wadan da suke jijir dasu.
"Haka ne, amman zuciyata ta, tafi wajen wani can."

"Ki daure kije gare shi ko kya samu nutsuwa."
"Kina ganin beyi zuciya ba."

"Tayya zaiyi zuciya dake bayan yasan matsayin ki da irin zumar da kike shayar dashi."

Ido ta juya,
"Amman kice lalashi na kika yi."

"Daman mana."
"Ok jeki."

Ta mike tayi benen wajen.

Kwabar da ke gaban ta ta dauka ta zuba giyar dake ciki a kofi.

Sha ta farayi, tana lumshe ido sai kace me shan wani abin dadi.

*Wacece Munasha*

Munasha, suna ta na ainihi Maimuna, mahaifin ta Malam Anas, Sai Mahifiyar su Sadiya. talakawane dan mahaifin ta itace yake siyar wa.

Basa dai taba rasa abinda zasu ci, haka nan sutura duk shekara yana dinka musu ita kala biyu ko daya.

Mahaifiyar ta aikato take yi a wani gida dake unguwar su, anan take samar musu yan kwancen kaya, da dan abinci.

Munasha, ta kasance me kwadayi da son abun duniya.

Duk kokarin da Mahaifin ta yayi mata, abu bata taba ganin ya mata sai rainuwa haka nan abinci, in anyi shima sai ta ga damar ci.

Ya sanya su a makarantar boko da arabi. Bokon dai dayaya aka gama ta. Hakan yasa tana yin candy ta fara bin maza.

Dan a duniya tana son ta ganta da kudi wannan yasa, ta fara bin maza. Ganin mahaifin ta zai hana ta fita yasa a cikin Yan iskan su, tasa wani yazo, a zuwan ya dauki nauyin karatun ta.

Mahaifin Munasha yaji dadi da wannan abin wannan yasa Munasha ta samu kafar fita. Dan wani lokacin ma haka tace ta koma hostel da zama.

Nan kuwa ba a hostel din da take in ba club ba sai, sai gidan samarin ta.

Munasha, ta zama babba a harkar karuwanci,

muje zuwa dan cigana da jin lbrin Munasha.

*INDABAWA*
[1/18, 14:09] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
 ASMA'U HUSNAH

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJWO* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

*46-50*

Dedicated to my love mother. *Momy nah*

Really love u

An Ruwaito Cikin Littafin Ibn Sinni, Daga *Anas (ra)* Lallai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: "Shin 'Dayanku Zai Gajiya Ya Zamo Kamar Abi-Damdama?" Sai Sahabbai Sukace Wanene Abu-Damdama Ya Annabin Allah? Sai Yace: Ya Kasance Idan Ya Wayi Gari Yana Cewa: *{Allãhumma Inni Qad Wahabtu Nafsi Wa Irdi Laka, Falã Yashtumu Man Shatamahu, Wala Yazlimu Man Zalamahu, Wwala Yadribu Man Darabahu}*

*KARASHEN LBRN Munasha*

A cikin kawayen ta mutum daya ce ta arxiki. Wacce tun fara bin mazan ta take mata fada akan irin samarin da take kulawa.

Dan ke daga ganin samarin ma xaka san yan iska ne, bare in suna mu'amala suyi ta taba ta. Ko ace za'a tafa.

Ko in tana bukatar abu sai dai tace saurayi yayi mata.

Rashida yar gidan masu hali ce, dan sau tari takan bata kudi kashe wa. Sannan in an mata kaya kala uku zata dau daya ta bata.

Amman sam Maimuna bata godewa Allah. Ita burin ta tagan ta ta kula me kudi wanda zai na kashe mata kudi.

Bayan yawancin samarin yanzu basa yin abu dan Allah sai dai in zasu fansha.

Rashida takan mata fada.
"Haba Maimuna, yanzu da hankalin ki, kike kula wadan nan mazan.
Shin me yan mata memukeso muzamane, ina hankalin mu yake ina tunanin muyake ne, Shin iyayen mu me suka gaza yimana muke nema mudorawa kan mu akan hanyar da baza ta bulle da mu bane. Duk kokarin da Baba yake, amman kike son daurawa saurayi duk buqatar ki.
Haba yar uwata ashe kinyadda saurayinki xemiki abunda iyayenki baxasu yimiki, Maimuna ki nemo hankalinki da nutsuwar ki6oye son abun duniyarki badon komaiba sedan kitsira da martabarki taki ta 'ya mace.
saurayi nagaskiya shine wanda yake sonki da aure baya neman komai daga gareki burinsa yaga kin tsira da mutuncinki.
Saurayi mayaudari shine Wanda yake miki hidima ba don Allah ba sedan kibashi gishiri yabaki manda.
Mace wadda akasanta da kunya, tarbiyya, mutunci, Jan aji, kamala, sanin yakamata, amman kin manta dacewa yanxu xamani yasanja wasu daga cikin samari sundena abu dan Allah sedan samun riba.
wallahi Maimuna, idan saurayi yafuskanci ke kinada kwadayi akwai matsala ta hanyar haka xesamu damar isar da qudurinsa, wallhi saurayi bashida abun duniyar daxe rudeki yaxubar miki da mutuncinki bashida abunda xemiki wanda iyayenki xasukasa.
Alokacin bakida damar hanashi duk abinda yanema domin shi kika fara mora. kinsan ko farce yata6a miki yacuceki dan Allah Mainuna ki kula."

Duk lokacin da Rashida tai mata fada takan dauka.

Amman da ta hadu da yan harkar ta zata manta.

In kuma Rashida tai musu fada gaba dayan su, sai suce dan ita Rashida din yar masu Hali ce shi yasa bata san halin da suke ciki ba.

Tin asali Yayan Rashida ke son Maimuna, amman tafiyar sa karatu malesia, shi ya sa soyayar ta ja baya.

Duk da a cikin zuciyar sa bai da burin da ya wuce ya kamala karatu ya dawo ya tai maki rayuwar Maimuna da mahaifin ta ba.

Itama a zuciyar ta shi take so, dan Nasir namiji ne wanda ya amsa sunan namiji, ya hada komai kyau ilimi da gayu.

tinda ya tafi be dawo ba duk da suna waya amman karatu yana dauke hankalin sa. Ba dan baya son ta yafi bawa karatu lokacin sa ba. A'ah sai dan son da yake yaga ya kammala karatun sa ya fito da sakamako me kyau.

Maimuna kyakyawa ce ajin karshe, fara me kyaun sura. Amman duk ta zubar da mutuncin ta.

Har Kungiya ce, da ita wace take daukar yara ta kaisu wajen manyan Alhazai.

Wanda har a cikin makaranta ma, akwai wadan da suka daure mata gindi.

Yanzu haka Munasha ta zama kwarariya dan ta kama naira a hannu.

Yanzu haka da taga saurayi yayi mata zata san yadda zatayi ta ja hankalin sa.

Har wajen malamai take kai mutum a janyo mata hankalin sa. Munasha babbar yar duniya ce wcce idon ta ya gama budewa.

Ba kasar da bata fita.

A harkar karuwanci dai ta fita zakkah. Amman duk da haka, son Nasir na cikin ranta.

*-*-*-*-*-*-*-*-*

Kwance take a kan gadon ta, sanye take da hijab fuskar ta, tayi kyau da ita.

Sai futar da annuri take, allon wayar take kallo. Wannan yasa na mika kai dan ganin abinda take yi.

Aslam na gano kwance akan katon gadon sa, yana sanye da blue (ruwan omo) din T-shirt, da blue din wando, da alamar kayan bacci ne a jikin sa.

Magana ya ke fada mata kunne na kasa ina sauraro.

"Ke na bawa zuciyata *Asma'u*, ki adanata dan nasan zaki mata gata,"

Murmushi *Asma'u* keyi. Sanna tace,
"Hmm Ya Aslam. Gakiya kam zan kula maka da ita fiye da yadda zan kula da tawa."

"Nima na sani. na baki ita ne saboda bana son kowa ya taba ta. Duk wanda zai shiga ke zaki bashi izinin shigar ta"
Murmushi tayi.

Ya cigaba da magana
"Dake na fiso muyi soyayya, sannan dake nafi son muyi rayuwa. Dan Banda kamar ki a duniya, wannan yasa na mallaka miki zuciya ta"

"Kai Ya Aslam!"
Ido ya kanne mata ya ce,
"Ke ta daban ce. Shi yasa kullum yabon ki nake. Ke nake son ki kasance a kusa dani. Dan kece kadai farin ciki na."

Shiru *Asma'u* tayi tana sauraron sa, tare da lumshe idanun ta.

Kallon kyakyawar fuskar ta yake yi.
"Ke ce Taurruwa ta. ke kika hasken zuciyata. Kin kawar min da dukkan damuwa ta. Ban da bakin magana gare ki ban san irin godiya da zan miki ba. Ban san kuma me kike son na miki ba."

Idon ta, *Asma'u* ta bude, ta kira sunan sa.
"Ya Aslam!"

Kallon ta yayi kafin ya amsa da
"Na'am Baby nah!"

Ta ce,
"Alkawari nake son karike min koman wuya kar mu rabu kaji."
Chapter 9 · 0% Book details