← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 61

Sashe 20

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fada yana girgiza kai. Ya ce,
"Dan ma Allah yasa na saba da wani zaki aura da na tausaya miki dan kafin ya saba da rigimar ki ko?"

Murmushi tayi ta ce,
"Shiyasa a ko da yaushe nake godewa Allah ya hadani da Yaya na. Yayan na ma wanda yafi so na. Wanda yafi kula dani wanda yasan komai nawa."

Murmushi yayi ya ce,
"Yarinya kin min wayoo nima zanje na samo wacce tasan ni."

Fuska ta bata ta ce,
"Akwai wace tasan ka ne sama dani. Kaga ni kanwar ka ce, zaka iya hukunta ni duk abinda nai maka Mami da Dady baza su ce komai ba. Amman kaje ka samo wacce mahaifin ta zai zo ya zane ka in ka taba masa 'yar sa."

Dariya yayi ya ce,
" *Husnah* kenan ina kaunar ki kaunar ki baza ta taba bari na ba. Da ita zan mutu."

Asma'u ta ce,
"Ya Aslam na maka alkawarin bazan taba barin ka ba zan kasance da kai a duk halin da kake ciki. Zan baka duk kan kulawa wacce ta rataya a kaina."

Yaa Aslam ya ce,
"Nima nayi miki alkawari...."

Da sauri ta katse shi da
"A'ah ni ba sai kayi ba."

Ya ce,
"Saboda me?"

Ta ce,
"Na yadda da kai zaka kula dani. Nasan ko ba aure a tsakanin mu zaka kula dani. haka kuma nasan zaka kasance dani. Wannan ma nasan zaka iya. Wanda zaka fada bana son yazo be faru ba shine kace baza kai min kishiya ba."

Kallon ta yayi ya ce,
" *Husnah* kenan baki yadda dani bane."

Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah na yadda da kai. Ai ba mu san yadda Allah ya kaddara mana ba. Su wadan can nasan ko ba aure zamu kasance tare "

Murmushi yayi ya ce,
" *Husnah* Nai miki alkawari bazan guje miki. In dai soyayya tace kin gama samu, kuma insha Allahu babu kishiya."

Murmushi tayi jikin ta a sanyaye ta ce,
"Toh Ya Aslam. Amman ina tsoro wallahi."

Ya ce,
"Ki bar tsoro, ki sanya a ran ki za ayi auren mu. In Allah ya yadda zamuyi rayuwa, matsayin ma aurata za muyi shakuwa. Ba gudu ba ja da baya sonki zan tayi zan zauna dake har karshen rayuwa."

Kanta ta sunkuyar ta ce,
"Allah yasa."

"Ameen!"
Ya fada yana dago kanta.

Murmushin yake tai masa. Fuska ya bata ya ce,
" ki fadan damuwar ki?"

Murmushi tayi ta ce,
"Ina yawan jin faduwar gaba Yaa Aslam kuma nafi alakanta haka da soyayyar mu. Ya Aslam ina tsoro. Tsoro ma ba kadan ba."

Murmushi yayi dan shima ta sanyayar masa da gwiwa. Ya ce,
"Kinsa dai ki kadai ce a Cikin rai na ko? Wallahi *Husnah* ke kadai ce buri na da muradi na ban da burin samun wata mace in bake ba. filin zuciyata ko ta ina kece bake, ba sauran wajen da wata zata shigo shi to kwantar da hankalin ki."

Fuska a dan marairai ce ta ce,
"Kallon ka kadai nayi da ido nishadi yake sanya ni. Kai ne muradi na. farin ciki na abin alfahari na. Dole ina tsoron rasa ka da kai kadai na yadda na aminta da kai na fara soyayya dakai nake son kare ta in har na rasa ka ya kake zaton zan kasance."

Ya ce,
"Allah ma zai sa ke *tawa ce* "

Ta ce,
"Allah yasa."

Ya ce,
"Ameen!"

Shiru sukai ya ce,
"Kinsan me?"

Kai ta girgiza masa. Ya ce,
"Ina bude ido na farka a bacci ba wanda nake son na gani a dama na sai ke. Shi yasa da na tashi hoton ki shi nake fara kalla. Bana gajiya da kallon kyakyawar fuskar ki."

Murmushi tayi ta ce,
"Yaa Aslam ina rasa a cikin mu wa yafi son wani."

Ya ce,
"Kinsan me?"

Ta ce,
"A'ah!"

Ya ce,
"Ki bari sai munyi auren anan za a ga wanda yafi son wani. Ni dai nai alkwarain bazan taba saki kuka ba. zan ta faran ta miki zan kula dake insha Allahu."

Dariya tayi ta ce,
"Nima nai maka alkwaraiin kula da kai da sauke maka duk hakkin da ya hau kai na. Zan kasance mace ta gari me son farin cikin ka mai gusar maka da bakin cikin ka."

Hannun ta ya kamo, ya ce,
"Oya Alkawari."

Dagowa tayi ta kalli cikin idon sa ta ce,
"Nai maka alkawarin bazan taba daina son ka ba. Kuma zan kasamce mace ta gari a tare da kai kuma bazan taba guje maka ba."

Murmushi yayi ya ce,
"Nima na miki alkawarin bazan taba guje miki ba haka nan zan ta son ki har karshen rayuwa ta zan kasance mai saki farin cikin ki."

"Allah yasa."
ta ce,

Ya amsa da
"Ameen!"

Ta ce,
"Yaa Aslam duk abinda nake aka ce kai ko sai na saurare shi."

Murmushi yayi ya ce,
"Bajin dadin labari in ba naki ba, ba shauki ke ko acikin taurari kin yi daban. Kaunar ki nake yi kullum a cikin zuciya ta."

"Hmm Ya Aslam! Kenan"

" *Husnah* komai nawa naki ne ban da burin da ya wuce naki. Kume naki burgeni yake yi. Surar ki tamkar ke kika tsara ta ina matukar kaunar ki."

Ido ta rufe da hannayen ta. Hannun nata ya kamo ya ce,
"Dan Allah kalli yatsun ki abin sha'awa."

Janye hannun ta tayi da sauri. Fuskar ta ya kalla ya ce,
"Kalli fuskar ki me kyau."

Ido ta bude ta kalle shi. Ya ce,
"Kalli idanun ki masu kyau da girma da birkita tunani. Ina kunar su."

Baki ta dan turo, ya ce,
"Ya salam ai sai kisa nayi abinda ban shirya ba. Ina son bakin nan naki."

Kafa ta buga a kasa ta ce,
"Kai Yaa Aslam!"

Dariya yayi ya ce,
"Wallahi komai naki burge ni yake. Komai. komai nake nufi."

Mikewa tayi ta ce,
"Ni mu shiga ciki magariba ta taho."

Mikewa yayi ya bi bayan ta rike da littatafn ta.

Suna shiga ta haye sama dakin ta. Kan gado ta fada ta lumshe ido.

Dakin ya shiga ya ajiye mata littafan sannan ya kuma gefen ta yana kallon ta.

Jin ido na bin ta, ya sa tai ssaurin bude ganin shi tayi a gaban ta ya tsura mata ido.

Mikewa tayi zaune ta ce,
"Ya dai?"

Murmushi yayi ya mike ya ce,
"Ji kiran sallah amman kika zo kika kwanta ko? Ko bakya yi ne?"

Kai ta gyada masa, mikewa yayi ya ce,
"Bari nai alwala."

Ya shiga bandakin ta. Alwala yayi ya fito ya ce,
"To na tafi sallah. Ya kamata kiyi lazumi ko ki karanta alkur'ani tinda ba sallah zakiyi ba."

Kai ta gyada masa. Dan ya saba sanin in ba yin sallah take ba.

Ita wani lokacin tana daukar sa tamkar Yaa Buharin ta ne.

*INDABAWA*
[1/18, 14:18] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*

*Gaskiya ina jin dadin yadda kuke kkokari wajen zaman lafiya da kula da juna. Ina gaishe lu yan kungiyar mu. Allah kara muki basira da daukaka.*

Dedicated to *My Lovelly Momy*

*106 - 110*

*Karanta Alkur'ani a gida*
*Yana Daga Cikin Dalilan Dake Nuna Haka Hadisin *Abi-Hurairah (ra)* Inda *Manzon Allah(ﷺ)* Yake Cewa:_

*{ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﻫُﺮَﻳْﺮَﺓَ ﺃَﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻬﻢ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ ﻟَﺎ ﺗَﺠْﻌَﻠُﻮﺍ ﺑُﻴُﻮﺗَﻜُﻢْ ﻣَﻘَﺎﺑِﺮَ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥَ ﻳَﻨْﻔِﺮُ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺒَﻴْﺖِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺗُﻘْﺮَﺃُ ﻓِﻴﻪِ ﺳُﻮﺭَﺓُ ﺍﻟْﺒَﻘَﺮَﺓِ [مسلم:٧٨٠]}*

'''Fassara:''' _An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa: *"Kada Ku Mayar da Gidajenku Kamar Makabartu, Lallai Shedan Yana Gudu Daga Gidan da Aka Karanta Suratul Baqara a Cikinsa".* (Muslim: 780)_

*Lallai karata Suratul bakara a ggida yana da amfani. Dan akwau wata Mamanah in ta saka a gida har tsorata ta ake. Da ta tambayi wani malami ya ce ta cigaba da sakawa insha Allahu ta daina gani.*

*Ko kunsan cewa in da wani sihiri a tare da kai ko al jannu karanta suratul bakara ko saka karatun ta yana baka kariya.*

*Mu daure da karanta ta ko da aya kadan ke daga ciki*
*Mu daure da son karanta alkur'ani*

Watan Yaa Aslam daya ya fara shirin tafiya.

Asma'u ji tayi kamar me, dan kuka ta sha shi tinda ya ce mata zzai tafi.

Ranar Asabar ya saka tafiyar tashi. Ranar juma'a ya dauke ta ya kai ta shopping yai mata siyayya mai yawan gaske.

Amman duk jikin ta a sanyaye yake da ka kalle ta zaka san bata da walwala.

Haka suka dawo gida duk yadda yaso ta sake kasawa tayi sai dai ta dan yi masa murmushin yake.

Da dare bayan sun ci abinci ta shiga dakin sa dan taya shi hada kaya.

Shima yana kwance ya fito da kayan ya ajiye akan gado.

Tunanin shima rabuwa da ita yake. Kallon sa tayi ta wuce wajen kayan ta fara zuba masa a cikin akwatin sa.

Motsin ta da yaji shi ya sa shi bude idon sa. Kallon ta ya tsaya yi hada masa kayan take cikin sanyin jiki.

Jin idon sa akan ta yasa ta kalle shi, Murmushi ta sakar masa, ta cigaba da abinda taken.

Mikewa yayi zaune ya zura mata ido. Ko kiftawa baya yi.

Har ta gama bai dauke idon sa daga kallon ta ba.

Takalman sa ta fara hadawa ta gama ta koma gefen sa ta zauna.

Kallon sa ya dawo da shi kan ta, murmushi ta kara sakar masa.

"Yaya nah lafiya?"
Ta tambaye shi.

"Baby nah bana son ganin ki a damuwa,"
Ya fada yana kamo hannun ta.

Hannun ta. ta zare ta ce,
"Yaya nah naji sai kuma me?"

"Bansan menene ba. Amman bana son barin ki Asma'u bana son nima na tafi. Ki yadda nayi magana ai mana auren kinji."

Kasa tayi da kanta sannan ta ce,
"To Yaya nah yanzu in mukai auren karatu na fa. Kaga nazo gangara ka bari nan da wata shekara sai muyi aure ko?"

Kai ya gyada ya ce,
"Haka ne, amman bana son na rasa ki bana son nayi nesa da ke."
"Haba Yaya nah kar ka manta fa dazu kai ka gama lallashi na akan nayi hakuri muna tare ko?"

Hannun ta ya kamo ya matse shi a cikin nasa. Ido ya lumshe, sannan ya bude.
Chapter 20 · 0% Book details