Sashe 21
Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon ta ya tsaya yi tin tana kallon cikin idon sa, har ta gaza kalla dan wani abu take ganin yana shiga cikin nata.
Lumshe idon tayi matsowa yayi kusa da ita. Ya ce,
"Asma'u ki riken Alkawari na kar ki taba bari na in dai ina cikin duniyar nan ina son ki yi min alkawarin ke tawa ce."
Idon ta, ta bude wanda suka canja kala zuwa ja, ta ce,
"Wallahi Yaa Aslam na maka wannan alkawarin bazan taba barin ka ba. Sai dai in kai ka bukata."
Ido ya lumshe samnan ya ce,
"Ni kuwa tayaya za'ai na bukaci rabuwa da rayuwa ta."
Murmushi tayi ta ce,
"Bare kuma ni."
Yayi murmushi.
"Bari naje na kwanta!"
Kallon ta yayi ya ce,
"Kamar mu kwana tare."
Murmushi tayi ta ce,
"Allah kawo ranar da zamu kwana taren."
"Ameen!"
Ya fada yana mikewa. A kofar dakin ta suka kara tsayawa sun dauki kusan minti ashirin suna tsaye sannan sukai sallama ta shiga.
Tana shiga daki ta fashe da kuka. Rasa kukan me take tayi amman ta san cewa ba zai rasa nasava da tafiyar Yaa Aslam ba.
Sai da taji kiran sa a waya sannan tai saurin shiga bayi tai wanka ta fito ta shirya sanann ta kira sa.
"Baby na kin kwanta ne?"
Ya tambaya daga can site din.
"Eh yanzu na kwanta."
ta bashi amsa.
Ya ce,
"To kiyi addu"a sai da safe."
Ta ce,
"Allah tashe mu lafiya."
Ta fada tana kashe wayar.
Washe gari tin asuba ta tashi ta yi duk abinda zata yi.
Wanka tayi ta koma gado tai kwanciyyar ta.
Sai karfe sha biyu sannan ta mike ta kara watsa ruwa ta shirya cikin wani tissue pink material wanda akai mata dinkin fitetgown, batai kwalliya ba.
Hoda da man lebe kawai ta shafa sai kwalli da ta saka a idon ta.
Falo ta fito ba kowa a sama a kasa ta dinga jin maganar su.
Sauka tayi a hankali ba ta kalle su ba sai da ta shiga kkitchen.
Ruwan zafi kawai ta hada ta fito falo. Sai da ta gaishe da Yaa Aslam da Yaa Buhari sannan ta nufi daining.
Zama tayi ta kasa shan tea din ma. Yaa Aslam ne ya mike ya shiga kitchen ya dafa mata indomie sai ya soya mata kwai.
Daining ya nufa ya zauna a kujerar dake facing tata.
Kallon sa tayi ta sakar masa murmushi.
Plate din hannun sa ya tura mata gaban ta. Ya daga mata gira alamar 'ta ci.'
Ja tayi ta saka spoon tana ta wasa da shi.
Amsar spoon din yayi ya fara bata a baki. A hankali a hankali har ta ci mai yawa sannan ta ce ta koshi.
Falo suka koma suna hira da Yaa buhari ita kuwa tai shiru sai dai ta kalli.wannan ta kalli wannan.
Kiran sallah aka yi wannan yasa kowa ya tafi dakin sa.
Alwala su Yaa Aslam sukai suka wuce massalaci.
Ita kuma a daki tai sallar tinda ta idar ta kasa tashi daga inda take har karfe biyu tana zaune.
Yaa Aslam ne ya shigo dakin cikin shirin tafiyar sa.
Yana sanye da Milk din wando sai maroon kalar riga mai dogon hannu.
Takalmin kafar sa ma maroon ne. sai tashin kamshi yake.
Tana ganin sa ta mike ta saki fara'a shima murmushin yayi ya kamo hannun ta suka fito.
Mami na falo suka tadda ta. Sallama yai mata suka fice tare.
Yaa Buhari ta gani a cikin mota yana jiran su.
Bayan mota suka shiga daga ita har shi har lokacin hannun ta na cikin nasa.
Wata zoben azurfa ya fito dashi daga cikin jakar sa. Ya zura mata a yatsan ta take hannun ya kara gaske yai mata kyau.
Sumbatar hannun yayi yana kallon cikin idon ta.
Lumshe idon tayi tana mai yin murmushi.
Suna zuwa airport din Yaa Buhari ya fita a motar.
Kallon ta yayi ya ce,
"Baby na zan tafi ki kular min da alkawari na."
Asma'u Ta ce,
"To Yaya nah Allah kiyaye hanya, kar ka manta da alkawari na nima kaji."
Ya ce,
"Insha Alalhu bazan manta ba!"
Yai mata kiss a goshi sannan ya fita.
Ta taga ya leko ya ce,
"Ki zauna ba sai kin ffito ba. Kai ta daga masa sai kuka kuma.
Kuka sosai take ba shiri ya koma cikin motar ya jata jikin sa yana lallashin ta. Amman kamar kara zuga ta yake.
Ya jima yana lallashin ta da kalamai masu sanyaya rai yaji ta daina kuka.
Bai daina shafa mata bayan ta ba da kwantar da hankalin ta. Sai da ya dauki minti goma a haka sannan ya dago dan ya ga me take.
Bacci yaga tana yi sai ajiyar zuciya take saukewa.
Murmushi yayi ya kwantar da ita sannan ya kara kissing nata a goshi.
Waya ya dauko ya dauki pics din ta sannan ya fita a hankali.
Yaa Buhari ya gani suka karasa ciki. Basu jina ba ya tashi. Dawowa mota Yaa Buhari yayi ya ganta tana ta baccin ta.
Motar ya tayar suka tafi gida a hankali yake tukin duk dan kar ya tashe ta.
Yana tausaya musu yana musu addu'a akan Allah ya mallaka musu juna su. Dan son da sukewa juna su shi gani yake kamar yayi yawa.
Kuma yana tausaya musu dan kar wani a bu ya faru bai san wane hali zasu shiga ba.
Har ya isa gida bata tashi ba. Daukar ta yayi ya kaita dakinta samman ya sanar da Mami sun dawo.
Sai magariba ta tashi. Tana bude ido taji idon ta a kumbure.
Taba su tayi sai kuma ta tuna da abinda ya faru dazu.
Wani kukan ta kuma saki ita kadai tayi iya yin ta sannan ta mike ta shiga ban daki.
Wanka tayi tayo alwala ta fito ta saka kayan bacci ta tada sallah tana idar wa ta kwanta anan inda take
Wani bacci ya kuma sace ta. Sai tara saura ta farka.
Bandaki ta shiga tai alwala ta fito tai sallah zata hau gado kenan sai ga Mami da Dady nan sun shigo.
Mami rike da katon tire a hannu. Gefen ta Dady ya zauna ya ce,
"Wannan shakuwar taku Asma'u tayi yawa. Yanzu inda Yayan naki yai aure ai sai Antyn ki tana jin haushi kiyi hakuri da kin gama karatu zaki je ki musu hutu kinji."
Kai ta daga tana masa murmushi sannan tai masa sannu da zuwa.
Abinci Mami ta zuba mata sai da ta ga taci ta koshi sannan suka fita daga daki
Kan gado ta koma ta kwanta kiran sa ne ya shigo.
Dagawa tayi cikin sanyin murya. Ta ce,
"Yaya nah ka isa lafiya yasu Momy da Dady?"
"Duk suna lafiya ya na baro ku?"
"Lafiya Alhamdulilah."
"Wallahi ina kewar Baby na."
Murmushi tayi ta ce.
"Nima haka."
Daga haka suka fara hirar su kamar yadda suka saba.
Sun jima suna hira sannan sukai sallama kowa ya kwanta.
*Uhmmm*
*INDABAWA*
[1/18, 14:19] Maryam S Indabawa🥰: *Asma'u Husnah*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*
Dedicated to *My Lovelly Momy*
Allah kara budi Allah ya daukaki. Ameen.
*111-115*
_Har Wayau An Kar6o Hadisi Ingantacce Daga *Jabir (ra)* Yace Yaji *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa:_
*{ﻋَﻦْ ﺟَﺎﺑِﺮِ ﺑْﻦِ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ، ﺳَﻤِﻊَ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲَّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ , ﻳَﻘُﻮﻝُ : " ﺇِﺫَﺍ ﺩَﺧَﻞَ ﺍﻟﺮَّﺟُﻞُ ﺑَﻴْﺘَﻪُ ﻓَﺬَﻛَﺮَ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋِﻨْﺪَ ﺩُﺧُﻮﻟِﻪِ ﻭَﻋِﻨْﺪَ ﻃَﻌَﺎﻣِﻪِ , ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥُ : ﻻ ﻣَﺒِﻴﺖَ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﻻ ﻋَﺸَﺎﺀَ ، ﻭَﺇِﺫَﺍ ﺩَﺧَﻞَ ﻓَﻠَﻢْ ﻳَﺬْﻛُﺮِ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋِﻨْﺪَ ﺩُﺧُﻮﻟِﻪِ , ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥُ : ﺃَﺩْﺭَﻛْﺘُﻢُ ﺍﻟْﻤَﺒِﻴﺖَ ، ﻭَﺇِﺫَﺍ ﻟَﻢْ ﻳَﺬْﻛُﺮِ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋِﻨْﺪَ ﻃَﻌَﺎﻣِﻪِ , ﻗَﺎﻝَ : ﺃَﺩْﺭَﻛْﺘُﻢُ ﺍﻟْﻤَﺒِﻴﺖَ ﻭَﺍﻟْﻌَﺸَﺎﺀَ [مسلم:٢٠١٨]}*
'''Fassara:''' _An Kar6o Daga *Jabir bn Abdullah (ra)* Yace: Naji *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa: *"Idan Mutum Zai Shiga Gidansa Sai Ya Ambaci Allah Yayin Shigansa, da Kuma Lokacin da Zaici Abinci, Sai Shaidanu Suce (da 'Yan Uwansu Shaidanu): Baku da Wurin Kwana Kuma Baku da Abincin Dare. Idan Kuma Ya Shiga Gidan Be Ambaci Allah Ba a Yayin Shigansa, Sai Shaidan Yace (da Yan Uwansa Shedanu): Kun Samu Wurin Kwana. Idan Kuma Be Ambaci Allah ba Yayin Cin Abinci, Sai Shaidan Yace da Yan Uwansa Kun Samu Wurin Kwana da Abincin Dare".* (Muslim)
Haka rayuwa ta cigaba dan gashi har Asma'u sun fara exam.
Murna suke dan baza su dawo skul ba asibiti zasu tafi su zama student doctor.
Sun gama Exam lafiya. Inda suka koma gida suna shan hutun su.
Dady kuwa har ya dawo an gama hada mata asibitin ta.
Bangaren Yaa Aslam kuwa sai wata kulawa da ya dada bata.
Dan shakuwar su ta koma yawa yanzu haka ma zai zo wani aiki zai yi sati daya a kano.
Murna gun Asma'u kamar me?
************
Bangaren Sabir kuwa, duk ya damu bama da akai hutun nan baya samun damar ganin Asma'u.
Mamah ta rasa me yake damun sa dan ba karamin sauyawa yayi.
Duk yadda Mamah taso ya fada mata damuwar sa ki yayi sai dai ya ce ba komai.
Zaune yake akan kujera dake garden din gidan su.
Idonsa a lunshe sai sake saken yadda zai ga Asma'u yake.
Can ya mike zaune da sauri yana lalubar number wayar Maryam.
Kira yayi sai da ta daga suka gaisa sannan ya ce,
"Daughter number wayar *Husnah* nake son ki bani."
"Ohk bari na turo maka."
Ta katse wayar tana murna dan tin da taga Asma'u taji tai wa Uncle din ta sha'awar ta.
Nan da nan ta tura masa, tana addu'ar Allah yasa ta zama matar sa.
Yana ganin number yai saving din ta da. *My Hussy*
Ya jima yana kallon sunan sannan ya tafi kira.
Tana tafiya zai yi sauri ya katse kiran.
Yayi haka fin sau goma sannan ya hakura dan ya rasa me zai ce mata in ta dau wayar.
Ya jima yana tunanin abinda zai ce mata.
Sako ya tura mata da wani sabon sim din sa. sannan ya ajiye wayar.
Can kuma ya dau wayar ya shiga whatsapp din sa.
Searching sunan ta yayi sai gashi yayi appearing.
Nan da nan ya shiga ciki. Last seen nata bata dade da sauka ba.
Profile picture din ta ya bude, Hoton Asma'un ya gani tana tsaye a garden din su.