Sashe 10
Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi yayi, ya gyara kwanciyar sa. Yana kara fuskan tar ta.
"Alkawari na rike miki kuma koman wuya bazan rabu dake ba kinji."
"Nagode!"
Kallon ta yayi yana kashe mata idanu kamar me jin bacci.
Kasa tayi da kanta.
"Wallahi rabuwar mu abu ce me wuya dan mun zama hanta da jini. Ko 'da da uwa."
Dariya ta saka tana girgiza kanta. Shima dariyar yake.
"Wallahi da gaske nake. Na fada miki duk abinda kika ji na fada daga zuciyata yake. Abinda zuciya ta take ji kenan baki na ya furta miki."
"Na yadda da kai Yayanah. a zuciya ban da kamar ka komai nawa ya zama naka. Amman dan Allah kar ka yadani ka kula da soyayya ta. Dan kai dai na aminta dakai kuma na yadda da kai. Mun shaku mun saba Ya Aslam abin da ya rage kawai auren mu ne."
Ta fada yana rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta.
"Oo please kicire kunyar nan cigaba da narka min zuciya mana."
Ido ta zaro
"tayaya zan cigaba da narka maka zuciya. Yanzu ya zanyi in na narka maka zuciya."
"Sai muyi amfani da taki ko?"
"A'ah muyi amfani da taka dai."
"To cigaba ina jinki."
"Kai Ya Aslam"
Kunnen sa ya kama yace,
"Yana jira zai kaiwa zuciyar ki abinci taci."
Dariya ta saki.
"Ya Aslam kenan!"
"Allah yunwa take ji fa."
"Toh Zan kasance me share maka hawaye a duk lokacin da zasu zuba zan hana su zuba. Zan kyautata maka in faran ta maka."
"Allah tabbatar mana da Alheri, sannan nikai na bazan taba barin ki kiyi kuka ba."
"Nagode!"
"Ba godiya a tsakanin mu."
Murmushi sukayi gaba dayan su.
"Tashi kije kiyi Alwala kizo kiyi addu'ar bacci."
"Toh!"
Ta fada tana tashi. Ban daki taje tayo alwala.
Addu'a tayi, yana jin ta har ta gama.
Wayar ya kashe, sannan ya kirata. Kamar yadda ya saba yi mata kissa Annabawa haka ya farayo mata har bacci ya dauke ta.
Washe gari ya kama asabar dan haka tin da ta tashi da asuba tayi sallah.
Ta fara gyara dakin ta, tin daga karkashin gado har su durowar ta duk da ba datti amman sai da ta gyare ta goge ko ina.
Sannan ta fita madafin su (kitchen) ba kowa a ciki wannan ya tabbatar mata da Mami na can gyaran daki.
Dan duk karshen sati sai sun gyare gida ko ina da ina tsab.
Wake ta auna tayi waje dashi. Ban garen masu aiki tayi.
Baba Lami ta sama zaune. Gaishe ta tayi, sannan ta tambaya ko Lubabatu na nan.
Kiran ta Baba Lami tayi. Lubabatu na ganin *Asam'u* ta saki murmushi.
"Ina kwana?"
"Lafiya lou."
"Dan Allah daman waken nan zaki surfa min saboda kar na makara zan je isilamiyya."
"Bakomai kawo."
Ta mika mata. Ta juya ta fita.
Kunun gyada ta dama musu, sannan ta hau gyaran kitchen din nasu.
Sai da tagama gyara sannan Lubabatu ta kawo mata markaden.
Kayan hadi ta zuba sannan ta fara soya kosai.
Kosan kuwa yayi kyau dashi ya tashi abin sha'awa.
Tana gamawa ta gyara falon su, sannan ta jere kayan karin nasu a inda suke cin abinci.
Kitchen din ta gyara ta wanke duk abinda ta bata.
Dakin ta ta koma tayi wanka sannan ta shirya cikin riga da siket yan kanti.
Sai ruwan tokar hijab da ta dau wanda yake a wanke a goge dashi.
Dakin Dady tayi, ta gaishe dashi sannan suka sauko kasa, Mami ce ta sauko da Ya Buhari, suka gaisa. Sannan suka fara karya wa.
Suna gamawa ta mike ta haye sama. Hijab din ta! Ta saka wanda yake har kasa. Sai nikaf da ta saka kafar ta da safa.
Jakar ta ta dauka, ta fito.
"Mami da Dady na tafi sai na dawo."
"To a dawo lafiya Allah bada sa'a"
"Ameen!"
Ta fice.
Yan uwa ya daren?
Toh sai Allah ya kaimi gobe in muna da rai da lafiya.
Nagode
*INDABAWA*:
[1/18, 14:10] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
ASMA'U HUSNAH
By *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
DEDICATED TO *MY UMMU NAH*
*Ummah farin cikin zuciyata. abar alfahari na.*
*51-55*
An Ruwaito Daga Cikinsa, Daga *Abi-Darda'i (ra)* Daga *Annabi (ﷺ)* Yace: "Duk Wanda Yace a Kowane Rana Yayin da ya Wayi Gari da Kuma Lokacin da Yayi Yammaci: *{Hasbiyallahu Lã'ilaha Illah Huwa Alaihi Tawakkaltu Wa Huwa Rabbul Arshil Azeem}³*, Sau Bakwai, Allah Zai Isan Masa ga Dukkan Damuwarsa ta Duniya da Lahira"._
________________________
Asma'u sai sha biyu da rabi ta dawo. a gajiye ta dawo ga rana.
Tana shigowa gida Mami ta tare tana
"oyoyo 'yar ta"
Murmushi tayi ta karasa gun Mamin ta, ta zauna a gefen ta. ta ce,
"Mami sannu da gida!"
"Yauwah Asma'u ya makarantar?"
Asma'u ta ce,
"Lafiya Alhamdulillah!"
Mikewa tayi ta ce,
"Mami bari naje na watsa ruwa."
"Toh!"
Tayi sama, tana shiga ta ajiye jakar ta, ta cire kayan ta ta sakale su ta shiga bandaki.
Ta jima tana watsa ruwa sai da taji sanyi sannan ta cuda jikin ta.
Tana fitowa ta saka wata doguwar riga mara hannu.
Hijab ta saka ta tada sallah. Sai da ta idar sannan ta shafa mai ta shafa hoda.
Wayar ta dake ta kara tin tana bandaki ta dauka.
Yaa Aslam ne dan haka da sauri ta dauki wayar ta kara akunnen ta.
Sai da yai sallama ta amsa sannan ya tambaye ta ya makaranta. Dan yanzu ya kira Mami ta ce yanzu ta dawo.
Da wayar a kunnen ta, ta sauka kasa dan samar abu me sanyi.
Ice cream ta dauko a firij din dake kitchen din su, sannan ta dawo falo inda Mami take.
Wayar ta kashe tana kallan Mami ta ce,
"Mami Zafi bai yiba wallahi."
Mami ta ce,
"Ranar da kika kwaso ce kinsan sha biyu lokacin tafi budewa."
Ice cream din ta fara sha tana lumshe ido har ta EMgama ta kwanta.
Ta ce,
"Mami bari na dan yi bacci kafin anjima dan nagaji."
Mami ta ce,
"Ai gara kina huta wa."
Cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ta. Mami na zaune a gefen ta, ta zuba mata ido.
Mami bata san saboda me ba. Amman Asma'u na yawan bata tausayi.
Yanzu da tana baccin ma kallon ta kawai take tana dada jin kaunar 'yar tata.
Asma'u ba dai hazaka ba sam ina ta tashi tin safe sai goman dare zata kwata. In kuma ta tashi da asuba bata kara rintsawa ga karatun su mai wahala. Amman kuma komai nata yana tafiya dai dai. Sai dai wani lokacin in karatu ya sako ta a gaba har ramewa take yi dan ko lokacin cin abinci bata samu.
Kafin la'asar ta tashi tayi sallah sannan ta dawo falo ta zauna tana danyin chatting a wayar ta.
Tana zaune taji sallamar Zainab da gudu ta mike tana rungume ta.
"Ah lallai yau Zee ce a gidan namu."
Hararar ta Zainab tayi ta ce,
"Ke dallah a gaban Mamin."
Ta dan daura mata hannu akan leben ta.
"Mami na kitchen bari na kirata ku gaisa mu tafi sama zaki fi sakewa."
Hanyar kitchen tayi tana kwadawa Mami kira. Mami ta fito ta ce,
"Lafiya?"
Asma'u ta ce,
"Mami, Zainab ce ta zo."
"Allah sarki sannun ta da zuwa ina zuwa."
Ta koma kitchen din ta rage gas sannan ta fito.
A falo ta same su. Zainab na ganin Mami ta sauka daga kan kujera tai kasa da kai tana gaishe da Mami cikin girma mawa. Mami na tambayar ta su Maman ta.
Sai da suka gaisa Mami ta koma kitchen sannan suka koma sama.
Suna zama yar aikin su Asma'u ta kawo mata ruwa da lemo hadi da snacks.
Suna hira tana ci har basu san magariba tayi ba sai kiran sallah da sukaji kawai.
Ido Zainab tayo waje dasu ta ce,
"Nashiga uku salar me?"
Dariya Asma'u tayi ta ce,
"Mene magariba ce."
Duka takai mata ta ce,
"Shine kike min dariya ko?"
"Sorry ta tashi muyi sallah ko?"
Ta mike ta shige ban daki alwala tayi sannan ta fito ta tada sallah.
Asma'u ma bandaki ta shiga tayo alwala tai sallah.
Suna idar wa Zainab ta mike. Kallon ta Asma'u tayi ta ce,
"Ai kya bari dai kici abinci Yaya ya dawo mukai ki gida ko?"
"Rufan asiri dare ai sai ya karayi."
Hararar ta Asma'u tayi ta ce,
"Da yake a jeji kike ko? To in na fadawa Momin taki ana zaki kwana fa."
Dariya Zainab tayi ta dauki jakar ta ce,
"Ni tashi muje."
"Allah sai kinci abinci."
Ta fada tana fita daga dakin.
Kitchen ta shiga ta hado mata abincin da sukai.
Tuwon semo ne miyar agushi taji nama sai kamshi take.
Sai lemon ginger da Mami ta hada musu. Diba tayi a babban faranti tayi daki dashi.
A zaune ta tadda Zainab tana shiga Zainab ta amshi kayan ta dire ta fara zubawa dan tai sauri ta gama su tafi.
Sai da taci ta koshi sannan ta mike ta wanke hannu. Kiran sallah isha'i taji wannan yasa tana fitowa ta tada sallah. Tana idar wa kuwa ta mike tayi waje.
Asma'u tabi bayan ta tana cewa,
"Ai kya bari nayiwa Mami magana ko?"
Tsayawa tayi ta na kallon Asma'u, kallon ta Asma'u tayi ta ce,
"Ga kujera ki zauna man."
Zama tayi ita kuma ta shige dakin Mami. Mami na zaune tayi kwalliya kamar yadda ta saba ta tarbar Dady.
"Mami zata tafi!"
"Au har ta fito."
"Eh!"
Asma'u ta bata amsa.
Leda Mami ta nuna mata ta ce,
"Dauki wacan ki kai mata ki dauki dubu biyu, ki bata kisa Baba ya kai ku ki rakata."
"To Mami Allah kara budi da girma."
"Ameen muje nai mata sallama ko?"
Suka fita tare Asma'u rike da ledar kayan kwalliya a hannun ta.
Sai da Mami tai mata sallama tare da godiya, sannan suka fita tare da Asma'u.
Suna fita suka tadda Yaa Buhari ya dawo. Asma'u ta ce,
"Yauwah kinga Yaya ya kaiki ma ko?"
Banza Zainab tai mata har suka karasa gefen sa.
Murmushi yake sakarwa Zainab dan shi bai ma kula da wata Asma'u ba.
Asma'u dake gefe ta ce,
"Ah lallai soyayya!"
Duka ya kai mata. Tai sauri kaucewa. Tana dariya.