← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 61

Sashe 42

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama murmushin tayi. Ya zauna a kujerar dake fuskantar ta.

Ido ya zuba mata, kasa tayi da kai, murmushi yayi ya ce,
"Baby nah!"

Shiru tayi, ya ce,
"Me yasa kike boyar min ne, bayan kinsan ganin ki shi zai samin sassauci a zuciya ta."

Dagowa tayi idon ta jajir ta ce,
"Dan Allah Sir ka kyale ni kaima kaje wajen mai son ka."

Kallon mamaki yake mata ya ce,
'Me sona kuma? Wace mai so na?"

Mikewa tayi ta ce,
"Kai ma kasani ai, dan Allah Sir ka so Nusaiba!"

Ta fada tana tafiya. Mikewa Yayi yabi bayan ta.

Kafin ya karasa ta shiga mota ta tayar harta danna horn mai gadi ya bude mata gate.

Mota shima ya shiga yabi bayan ta. Gidan Zainab ta tafi. Sabir kuwa yana biye da ita a baya.

Tana shiga shima ya shiga. Da sauri ta fita a mota tayi cikin gidan.

Tana shiga taci karo da Zainab, kallon ta Zainab tayi ta ce,
"Lafiya?"

Ganin ta da tayi ta shigo a firgice, bata rufe baki ba Sabir ya shigo.

Murmushi tayi ta ce,
"Au ashe tare kuke?"

Ciki Asma'u tayi ta barsu a nan falo. Zama yayi yana kallon hanyar da Asma'u tayi.

Murmushi Zainab tayi duk da yanayin Asma'u ya bata tsoro.

Lemo da ruwa ta dauki masa. Bai sha ba sai magana da ya farai mata.

"Zainab ke kadai kika fi kusanci da Asma'u a kawayen ta dan Allah ki taimaka ki shawon kanta. Wallahi ina son Asma'u amman ita taki ta gane"

Murmushi jin Dadi zainab tayi ta ce,
"Kar ka damu zan sanar da ita."

Kai ya girgiza ya ce,
"Na fada mata, amman taki ta fahimci irin son da nake mata ne"

"Ka barni da ita. Ina zuwa."
Ta mike tayi

Tana daya daga cikin dakin da ta ce na ta ne.

Saboda shi karami ne kuma komai na ciki kalar ta ne.

Tana kwance akan kujera idon ta lumshe hawaye na zubo mata.

A ranta take cewa
'Duk Yaa Aslam ne ya jawo mata. Yanzu ita bata da wani kwanciyar hankali. Daga wancan sai wancan. To wai ita tayaya zata auri Sir Sabir bayan tasan irin son da Nusaiba ke masa. Ai kamar ta zama azaluma ne "

Wata zuciyar ta ce,
'To ai shi baya son ta. In kinso shi ba wani abu bane."

Juyi tayi ta bude ido ta. Zainab ta gani tsaye akan ta.

Zaune ta mike ta ce,
"Ya dai?"

Kai ta girgiza ta zauna agefen ta. Ta ce,
"Lafiya naganki haka?"

"Uhnm Nida Sir Sabir ne!"
Ta fada mata duk abinda ke faruwa.

Zainab ma tana son Asma'u da Yaa Aslam to amman ba yadda zasu yi tinda shine ya nuna baya son ta.

Tinda haka ne gwara ta amshi Sabir din tinda shi yana son ta.

"Asma'u nima a gaskiya ina son ki da Yaa Aslam, but amman tinda haka ta faru ki yi hakuri ki rumgumi wanda yake son ki. Bance ki Yaa Aslam baya sonki ba, amman ki karbi Sir Sabir kuma ki yi istihara Allah zaba mafi alheri. Kiyi hakuri."
Zainab ta dafa kafadar ta.

Dagowa tayi da idanun ta dake zubar da hawaye ta ce,
"Zainab kinsan so amman baki san zafin sa ba. Nusaiba na kaunar Sir tin tana yarinya take son sa. Tayaya xan raba wannan soyayyar da take masa. Ki tayani wannan abin ina son Sir ya fara son Nusaiba ni na hakura dashi. Ina tausayawa Sir saboda yana sona ni bana son sa, kuma ni ba kinsa nake ba, kawai dai Yaa Aslam nake so. Gwara ya auri wacce yake so zai fi jin dadin yasan yai aure da ya aure ni ni kuma zuciya ta na wani wajen ki duba magana ta Zainab nasan ke zaki fahimce ni."

Ta fashe da kuka, jikin ta Xainab ta jata tana lallashin. Sai da tayi shiru sannan Ta ce,
"Zan sanar da shi amman ki daina kukan nan."

Kai ta gyada. Mikewa Zainab tayi ta fita. Ta sanar dashi indai yana son Asma'u to sai dai ya hada da Nusaiba. Sosai hankalin sa ya tashi. Lallabashi tayi kan yaje yai tunani sannan ya tafi gida.

Wajen Asma'u Zainab ta koma. Kallon ta tayi ta ce,
"Sis nai miki shishigi fa"

Kallon ta Asma'u tayi ta ce,
"Name fa?"

"Nace indai yana son ya aure ki sai dai ya hada ke da Nusaiba."

Shiru Asma'u tayi. Zainab ta ce,
"Kiyi hakuri in bakiji dadi ba."

"Ba haka bane. Amman ba komai."
"Yauwah dan Allah sis kina rage damuwa akan Yaa Aslam. Kina addu'a Allah ya yaye miki son sa."

Dagowa Asma'u tayi ta kalle ta ta ce,
"Wallahi kullum sai nayi wannan addu'ar amman kamar bana yi son Yaa Aslam kara shiga ta yake. Kwanaa biyun nan ji nake kamar nai hauka dan son ganin sa da nake. Na rasa ya zanyi da son sa. Ina son Yaa Aslam kuma yana daga cikin wadan da ya koya min son sa haka."

Ta fada hawaye na saukowa daga idon ta.

"To ya isa. Allah yasa haka shine mafi alheri"
Asma'u ta ce,
"Ameen!"

"Ina Mami?"
Zainab ta tambaya

"Uhmm Mami ta fita nima bata san nazo ba."

Asma'u ta ce,
"Me kika dafa ne?"

"Taso muje ki gani."
Ta mike ta kama hannun ta.

Dining sukayi suka zauna ta fara cin abinci.

Ranar har dare suna tare da yake Yaa Buhari bai dawo da wuri ba basu san har dare yayi ba.

Sai karfe goma sannan ya shigo, da ta ce, zata tafi kuma ya ce,
"Ba inda zata tinda Mami tasan tana gidan ta kwana kawai."

Haka dole ta kwana agidan. Washe gari tare da Zainab sukai komai tai wanka ta shirya ta ce zata tafi.

Hanata tafiya yayi a lokacin ya ce, Ta bari sa tafi tare gaba dayan dan zainab ma zataje gaishe da Mami.

Haka ta zauna har karfe biyu sannan suka tafi gaba dayan su.

A gida suka yini sai dare suka koma gida.

Mami kuwa sai jan Zainab take ajiki bama da taga tana jin kunyar ta.

Ita ta fiso ta zama free da ita kamar yadda Asma'u take mata.

Tin daga lokacin ya zama na yar boye ke tsakanin Sir Sabir da Asma'u.

A office ta maida kanta busy yadda ko ya ganta ba damar magana saboda yadda take tare da patient din ta.

Haka a gida da ta shigo taga motar sa take komawa, in kuwa har ta shigo da sun gaisa take guduwa sama.

In waya ya kira ma baya samu dan yanzu sai tai kwana nawa ma wayar ta a kashe.

Sosai ya damu, dan yana son Asma'u yana kuma jin tausayin ta.

A haka sai da suka debe wajen wata uku suna yar buyar nan.

Kuma baya taba samun damar da zai ganta.

Sunyi bikin Maimuna inda aka kai ta gidan mijin ta dake sabuwar gandu.

Gida ne mai kyau kuma komai ya mata. Sosai Asma'u ta bata gudumawa mai yawa banda wasu abun da ta dauke mata.

Asma'u da Zainab ne dai sukai mata Babbar kawa.

Wanna karan ma sai da Maryam tazo, Nusaiba dai bata zo ba dan a lokacin basa kasar.

Anyi biki lafiya an kai amarya gidan ta.

Sosai Nazir ya amshi kaddarar Maimuna tinda daman yasan ba budurwa bace.

To shi ita yake so, dan haka ya daura aniyar zama da ita da dadi ba dadi.

Duk da Maimuna ba ruwan ta yanzu abinda ya ce, shi take yi.
Zaman lafiya suke sosai yake faranta mata shima take faranta masa.

*MS Indabawa*
[1/18, 14:34] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer's*

Dedicated to *My lovelly Mum*

Pagr *61-65*

Bangaren Sabir kuwa da abin ya ishe shi sai ya samu Yaa Buhari da batun yana son Asma'u.

Duk da Yaa Buhari yafi son Asma'u su daidai ta da Aslam amman bai sa shi rashin jin dadi ba.

Sosai yaji dadi dan shi yasan waye Sabir, Dan in Asma'u bata auri Yaa Aslam ba ta auri Sir Sabir ba komai.

Dan ya tabbata Sir Sabir ma zai kula masa da kanwar sa.

Daga nan kuwa Yaa Buhari ya tafi gida ya fadawa Mami.
Mami cewa tayi, a tambayi Asma'u aji daga bakin ta.

Yaa Buhari ya ce,
"Aah Mami in har aka ce sai anji daga bakin Asma'u to tabbas baza ta amince ba. Kinsan irin son da takewa Yaa Aslam."

Shiru Mami tayi ta ce, zata tambayi Momy taji.
Momy ma sosai taji dadi dan daman ta yaba da hankalin Sabir sosai.

Itama cewa tayi a bari sai abin ya matso a fada mata sanin halin Asma'u zata ce A'ah

A bangaren Sabir kuwa yadda yayi zai hada Nusaiba da Asma'u dan yasan in ba haka ba Asma'u baza ta taba yadda ba.

Yasan ko ba komai Nusaiba mai son sa ce dan haka zai samu duk abinda yake nema a gun ta.

Amman yayi wa kansa alkawarin sai ya yayewa Asma'u halin kuncin da take ciki na rashin Yaa Aslam.

Ko bata son sa shi zai zame mata farin ciki. Farin cikin da zata manta da Aslam.

Nusaiba kuma ta fawalawa Allah komai. Addu'a da istihara take amman kullum son Sabir kara shigar ta yake.
Duk da haka suna waya da Asma'u dan sun zama kawaye.

A bangaren Zainab yanzu auren su wata bakwai yanzu tana da ciki wata hudu.

Bakuga yadda Asma'u ke ji da cikin nan ba.
Dan gidan ta koma da zama ma saboda taya ta aiki.

Komai yi mata take. In Asma'u ta zauna hira da cikin kuwa kwa rantse da mutum take hira.

Sosai Zainab ke kara lalashin ta akan zancen Sabir.
Duk da yanzu ya daina mata maganar amman tana lura ba wai hakura yayi da ita ba.

Yau tana gidan Yaa Buhari ake sa ranar bikin ta da Sabir, an sanya rana shekara daya, saboda so ake a hada bikin da na Nusaiba akai masa mata biyu a rana daya.

Ya sanar da su manufar sa tayin hakan kuma sun yadda dan sun san kafiyar Asma'u.

In ta ce,
"Eh!"

Ba wanda zai sa ta ce,
"A'ah!"
Chapter 42 · 0% Book details