← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 61

Sashe 38

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anan suka dan jima dan shima Sir sabir suna tare da Baban Hafsat.

Har abinci suka ci sannan suka taho, ranar shi ya dinga yawo dasu daga can zuwa can.

Har magariba sannan ya kai Zainab gida. Ana sukai sallah magariba sannan Asma'u tai mata bankwana suka taho.

A mota kuwa kowa shiru yayi shi yana tunanin taya zai kara cusa kan sa awajen Asma'u dan ya tabbata Asma'u baza ta ki shi ba sai dan kawai tana son Yaa Aslam ne.

Itama a zuciyar ta rokan Allah take Allah yasa kar yai mata maganar dan bata so.

Can ya dago ya kalle ta ya ce,
"Kin fadawa Maryam bikin ne?"

Kallon sa ta danyi sannan ta kawar da kai ta ce,
"Na fada mata, ta ce, next week ma zata zo."

Kai ya gyada ya ce,
"Oh yanzu dai kun zama friends ko?

Murmushi ta dai yi kawai ba tare da ta bashi amsa ba.

Ya ce,
"Yaushe za muje ki gaida Mamah?"

"Ko yaushe ma!"
Ta bashi amsa.

"Da gaske?"
Ya tambaye ta.

Kai ta gyada. Kallon ta yayi ya ce,
"Ko yanzu ne?"

Kallon jikin ta tayi ta ce,
"A'ah dai."

"Saboda me?"
Ya tambaya.

"Kalli jiki na fa?"
Ta fada tana kallon kan ta.

Murmushi yayi ya ce,
"Me jikin naki yayi?"

"A'ah dai."
Ta fada tana tsare shi da idanun ta.

Da yake shima ita yake kalli take yaji motar na neman kwace masa. Saboda idon ta da suka ruda shi.

Da kyar ya kamo motar ya cigaba da tukin.

Daga haka bai kara cewa komai ba, har suka kara sa gdn.

MS Indabawa
[1/18, 14:30] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
 ASMA'U HUSNAH

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJWO* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

*Gidan Hakuri da juriya tare da kawar da kai, gidan zaman lafiya. Na gaida ku.*

*36-40*

Dedicated to My great *Mamah* Allah ya jikan ki ba dan kin mutu ba.

Allah kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka.

Nagaida ke mahaifiya ta abar alfahari na.

*Manzon Allah (SAW) ya ce,
Idan zaka so mutum kada ka nuna masa tsananin so.
in zaka kisa kada ka nuna masa tsananin ki.

Dukkan su hankalin su ne yayi kan motar, banda *Asma'u* da ta daukar da kan ta, tana wasa da wayar ta.

Khadija ce ta fara magana, ta ce,
"Kai motar nan ta hadu amman."

Amina tace,
"Ai daga duk kan alamu, ma na cikin ta zai fi haka hauduwa."

"Gaskiya kan motar ba karya, ko wane dan gayun ne a ciki."
Hafsat ta fada

"Ni kam ba ruwana da na ciki sai motar da ta burge ni."
Zainab ta fada.

"Kai Allah bani irin motar na."
Hafsat ta fada.

"Hassada kike yi tinda kika ce Allah baki irin ta sai dai kice Allah baki finta."
Amina ta fada.

"Duk karya ne irin haka nan, dan kaga Abu ka roki Allah yabaka irin sa shine haka."
Zainab ta fada tana tabo *Asma'u*

" *Asmy* kalli waccen motar amman tayi kyau wallahi."

Kai ta dago ta kalli motar, ji tayi gaban ta ya fadi.
"Eh tayi kyau."

Ta fada tana mikewa sakamakon kiranta da ake yi.

Can gefe ta koma jikin wata motar, ta dauki wayar.

"Hallo my beauty! (Kyakyawa)"
"Ya Aslam wannan ai tsokana ce."
amsa ta amsa masa da muryar shagwaba.

"Wacce tsokana nayi."
ya tambaya

"Wai beauty!"
ta bashi amsa.

"Oo Ke ba kyakyawar bace."
Ya tambaya.

Ta ce,
"Gaskiya ni ba kyakyawa bace. Wannan ai sai kasa ayi min dariya."

"Ba wanda zai miki dariya kinji, saboda kyan ki ba kowa ke da irin shi ba. Kina da wani kyau wanda kafin a samu mutum me irin sa ake dade wa. Ur skin is fresh with a beauty colour. (Fatar ki a murje, me kala me kyau)."

Ta ce,
"Uhmm please stop dis joking I beg you. (Dan Allah daina wannan tsokanar na roke ka."

Murmushi yayi ya ce,
"Wallahi I am not joking, I am telling the true. (Ba tsokanar ki nake ba ina fadan gaskiya ta ne.)"

Baki ta turo ta ce,
"Naji ya isa, ka karaso ne,"
"Eh! Gani kina ina ne."

Ta ce,
"Ina kofar department din mu,"
"Nima ina wajen."

"Kai ya Aslam!"
ta fada.

"Da gaske ina wajen."

"Ta ina."
"Ina cikin wata Ash marsandi."

"Oh na ganka. Ina ta bayan ka."
"To kizo man."

"A'ah Yaya please kai ka fito."
"To gani nan."

Baya ta juya masa.

Kofar motar ya bude, wani sanyi da kamshi me dadi ne ya fito.

Kafar sa ya ziro kasa. Safa ce da takalmi sau ciki bakake a kafar sa.

Daya ya diro sannan ya fito gaba dayan sa. Suit ce a jikin sa, ruwan kumkumadi.

Ya cire ta saman sai yar ciki da ya rage. Tin daga kafar sa na fara kallon sa inayin sama. har na karasa kirjin sa wanda yake a bude dashi na kirar cikaken namiji me jini a jiki wanda ya cika namiji.

Kan fuskar sa na gangara. Fuskar sa me kyau ce doguwa fari ne tas dashi, sai manyan idanu wadan da suke a lumshe, wanda ake ce musu (sexy eye)

Bakin shi dan karami ne, wanda yake da lebe me taushi gasu pink sai kwalli suke. Kansa cike yake da suma, kamar ta indiyawa.

Sai saje dake gefen fuskar sa, wanda ya kara fito masa da kyaun fuskar sa. Idon sa sanye da farin gilashi.

Masha Allah wannan gayen duk inda ake neman cikaken namiji me kyau da kwarjini ya kai ya ma wuce nan.

Yan mata da yawa kallon sa suka tsaya yi sai gulmar sa akeyi. Dan ya gama haduwa ba karya.

Waige waige ya farayi dan neman inda take, duk da ta juyar da kanta sai da ya gene ita ce. Dan duk jikin sa ya gama shaida masa, *Husnah* sa ce.

Cikin tafiyar kasaita da nuna kalama tare da nutsuwa yake tafiya.

Sannu a hankali har ya karasa gefen ta. Ta bayan ta ya zaro hannayen sa dake cikin alhiju ya rufe mata idanu.

Jin an rufe mata ido da hannu me laushi, ga kamshin turare dake tashi, tasan Ya Aslam ne.

Murmushi ta saki me sauti.
"Haba My Hero, ai nasan kai ne."

Hannun sa ya janye ya maidasu kan kafadun ta ya juyo da ita.

Kasa magana yayi ya kure ta da idanu.

Ido ta kashe masa guda daya.
"Yah dai."

Yawu ya hadiye tare da sauke ajiyar zuciya yana me sakin wani murmushi dake karawa fuskar sa kyau.

Wani kallon soyayya yake aika mata dashi.

Ba karamin kyau sukayi ba.
"Baby nah kinyi kyau fa."
ya fada yana kara kallon ta.

"Zaka fara ko?"
Ta fada tana nuna masa wasu kujeru da aka gina su.
Zama yayi ita ma ta zauna.

"Sannu Yaya nah Ya hanya?"
ta tambaya cikin kulawa.

Ya ce,
"Hanya Alhamdulilah."

"Sannu toh!"
"Yauwah! Naji dadin zuwa na dana ganki Sweetheart, kin kara kyau, ashe duk hoton da nake gani rage min kyaun ki yake yi."

"Yayana kenan yasu Momy."
ta fada tana wasa da yatsun hannun ta.

"Suna lafiya."
Ya fada yaba dago face din ta.

"Bari na karbo maka lemo."
Ta mike.

Kamo hannun ta yayi ya ce,
"A'ah yanzu na gama cin abinci ga naku can ma a mota."

Murmushi tayi,
"Kai Yayah."
"Eh!"

"Zakaje gida ne."
"A'ah! Daga nan zanyi gida."

"Ok."
"Ina sonki Baby nah."

Murmushi tayi ta dukar da kanta.
"Baby kunyar nan taki tana dada miki kyau."

Kai ta kuma dukar wa.
"Bari na wuce kar nayi dare. Tinda naga Baby nah ai nagodewa Allah."

Murmushi tayi.
"To nagode."
"Nike da godiya Baby nah "

Suka mike suka nufi motar. Dai dai karasowar Sir Sabir zai dauki motar sa.

Kallon juna suka yi, ya shige motar sa.
"Waye wancan."

Juyawa tayi,
"Sir Sabir wani lecturern mune."

"Kuna magana ne?"
Ya tambaya fuska a dan hade

Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah!"

"Ina zee kuwa?"
Ya tambaya.

Kallon gun da suke tayi ta ce,
"Gata can bari na kira ta."

Ta tafi wajen su Zee,
"Zee kizo inji Ya Aslam!"

Ta fada tana kamo hannun ta.

Wajen su suka karasa.
"A bamu waje ko?"

Ya fada yana kallon *Asma'u* baki ta tabe ta bar wajen. Dariya yayi, yace,
" *Husnah* rigima."

Sannan ya dawo da hankalin sa kan Zee.
Bayan sun gaisa yake bata amanar *Asma'u* sannan sukayi sallama.

Wajen *Asma'u* yayi,
"Haba Baby na yanzu da Yayan naki kike fushi. Kiyi hakuri kinji."

Shiru tayi masa. Murmushi yayi, ya koma gaban ta,
"Ko so kike na rumgume ki na rarashe ki."

Ido ta zaro, tana girgiza kai. Ya jawo ta. Saurin janye hannu ta tayi. Tayi wajen motar sa.

Bayan ta ya bi, yana Murmushi ya shiga motar. Leda ya miko mata.

"Gashi ni zan tafi."
Amsa tayi ta ce,
"To Allah kiyaye hanya."

"Ameen nagode!"
Ta rufe masa kofar tana daga masa hannu. Tare da murmushi akan fuskar ta.

Sai da taga bata hango shi sannan ta koma wajen kawayen ta.

Ido suka bita dashi,
" *Asma'u* waye wancan."

Hafsat ta tambaya fuskar ta a hade. Kallon ta *Asma'u* tayi sannan ta dauke kai.

Zainab ce, tace,
"Yayan ta ne."

Khadija tace,
"Amman fa ya hadu. Wai meyasa ke kike baka ne."

Amina ce, tace,
"To ko zaki canja mata halitar ta ne,"

Harara ta Khadija tayi,
"Ni na tambaye ta, ta wani haden rai da dauke kai."

Hafsat ta fada, Mikewa *Asma'u* tayi ta kalle ta.
"kin tambayen an amsa miki ba shikenan ba. ko kin manta wa kike tambaya ne. *Asma'u* da batai miki komai bace kika dau gabar duniya kika daura mata, kin manta in nayi miki magana ko kallo na bakya yi shine kuma yanzu zaki zo kina tambaya ta. Kuma cikin isa sai kace ni yar kice. Ke bama zan fada ba. Kiyi abinda xakiyi."

Ta fada tana kama hannu Zainab suka shige hall.
"Haba *Asma'u* me kenan kika yi ke da bakya fada."

Kuka *Asma'u* ta fashe dashi,
"Ya zanyi kema kinsan dai Hafsat ta kaini bango ne. Duk makarantan nan ba wacce ta tsana kamar ni tin ina dauke kai sannan yanzu tazo tana min gadara. Akan abinda be kai ya kawo ba."
Chapter 38 · 0% Book details