Sashe 25
Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
In ko ba haka ba sai ya ce,
" *Husnah* ko na mutu ina son ki kasance cikin min addu'a sannan ki sawa ya'yan ki sona da min addu'a in Allah yayi ba xan ga lokacin ba. Ki kula da ya'yan ki. Ki basu tarbiyya mai kyau. Allah miki Albarka Allah yasa ki a gidan Aljanna Allah ya miki albarka."
Kullum sai ya nanata mata wanda nan kalaman kullum.
Wani lokacin tare ya shirya musu tafiya suka je dan siyan kayan dakin ta.
In ta nuna abu ya ce, a bata irin sa wanda yafi shi tsada.
Kaya masu tsada da kyau ya siya mata.
Kaya sosai ya lodo aka kawo gida. Daki uku aka dure kayan.
Da Asma'u ta ce,
"Dady kamar an siyo kayan nan da wuri"
Sai ya ce,
" *Husnah* gara na siya tin yanzu ban sani ba ko zan kai lokacin ko bazan kai ba. In na kai Alhamdulilah ga kaya nan sai dai nagan su kamar a sama. in kuwa ban kai ba kinga Mamin ki ta huta sai dai a dauka kawai akai. *Husnah* bana son na mutu da nauyin ku ta wani abu ban muku ba. Na baku ilimi daga arabi har boko to ba abinda zance da Allah sai godiya ko a yau na mutu naci riba dan na ilimantar da ku. Bayan nan na baku tarbiyya wacce kowa yake sha'awar ku ta wannan tarbiyyar taku. To nikan me zance da Allah sai godiya da ya bani ikon daura ku akan dai dai. Gashi duk cikin ku na baku abinda zaku rike kan ku da mahaifiyar ku ko bani da rai. Asibitin can naki ne halak malak dan na rubuta a takardun suma. Kamfani na na sharada kuma na bawa Buhari. Wadan can gidajen na kwandila na barwa Mamin ku. Ina fatan ko bayan raina kar ku shiga cikin kuncin rayuwa. Alhamdulilah da Allah ya nuna min wannan lokacin lokaci daya nake fatan Allah nuna min shine. Allah ya nunan ranar auren ki.
Kasa tayi da kan ta ta amsa da Ameen.Kalaman Dady ba karamin kashe mata jiki suke ba.
A asibiti kuwa Sosai take da kokari dan duk abinda aka daura ta akai tana yin sa bakin kokari. Ga Yaa Aslam dake kara koya mata.
Sir Sabir kuwa yana yawan zuwa ya gaida Mami ya tafi duk da duk zuwan da zai yi baya samun Asma'u a gida.
To shima yanzu ya bar Makaranta ya koma asibiti.
Son Asma'u sai daduwa yake a cikin zuciyar sa. Sako kuwa kullum sai ya tura mata amman sam ko reply.
Hoton ta shi kadai yake kalla yaji dadi a zuciyar sa.
Amman kullun da ita yake tashi da ita kuma yake kwanciyya.
Haka yau kamar kullum bayan ya koma gida yai wanka ya shirya cikin wani tissue yadi fari.
Ba karamin kyau yai masa ba. Fitowa yayi yaiwa Mamah sallama ya fita.
Kai tsaye gidan su Asma'u ya tafi. Bai da buri da ya wuce yaga Asma'u.
Asma'u tana gida yau dan ta yi targade a garin hawa sama yau duk gidan sun san Asma'u taji ciwo.
Tana jikin Mami sai raki take mata.
"Uhm wayoo Mami kafa ta."
Mami kuwa sai lallashin take tana mata sannu. Duk ta rasa inda zata saka 'yar tata.
Dady ya kira shima yana tambayar kafar Asma'u,
Wayar Mami ta bata yai mata sannu sannan ya ce, me take so?
Fada masa tai. Sukai sallama, tana cikin yiwa Mami shagwaba akai yo sallama kan Mami tayi bako.
Izinin shigowa Mami ta bayar. Tana kwance akan kafar Mami tana tsiyayar da hawaye ya shigo.
Da Sallama ya shigo Mami ce ta amsa masa ya shigo ya zauna.
Asma'u dake cinyar Mami tayi juyi ta gyara kwanciyya ta ce,
"Mami kafa ta."
Shigowa yayi. Mami ta ce,
"A'a Sabir ne?"
"Eh wallahi Mami."
Ya zauna suka gaisa, Asma'u ce ta kara juyi ta bude idon ta.
Sabir ta gani da sauri ta mike zaune tana daura kan ta a kafadar Mami.
"Ina yini?"
Ta fada tana kamo hannun Mami.
Amsawa yayi ya ce,
"Yau bakije asibitin ba."
Mami ta kalla. Mami ta ce,
"Wai nan targade tayi shine fa take ta kuka ka ganta nan sai kace ba mace ba."
Baki Asma'u ta turo, Sabir kuwa Murmushi yayi ya ce,
"An duba kafar?"
Kai Asma'u ta daga. Ya ce,
"Zo naga kafar."
Kamar baza taje ba ta mike ta karasa inda yake da kyar take tafiya.
Kafar ya duba ya dan taba ta saki kara tana rike hannun sa.
Lumshe ido yayi jin hannun ta mai laushi da ya ji da ta haifar masa da kasala.
Da kyar ya ce,
"Mami gyaran ne bai ba shiyasa."
Mami ta ce,
"Haba nifa ince tin dazu sai kukan kafar take."
Kafar ya kama ya ce,
"Mami kuna da man zafi."
Eh Mami ta fada ta hau sama, kallon ta Sabir yayi. Kanta a kasa ta kasa dagowa ta kalli fuskar sa.
Shi kuwa kallon ta yake kamar ya samu TV sai da yaga kamar zata dago sannan ya dauke kan sa.
Mami ce ta sauko rike da man zafi a hannu ta mika mata.
Amsa yayi yai tofi ya daura hannun sa a kan kafar ya danna ya ja.
Ihu ta saki tana kiran Mami. Kara tayi tai saurin rike hannu.
Hannun sa ya zare daga nata, ya karayin tofin yana jan kafar.
Kuka sosai Asma'u take, Sai da ya tabbatar da kafar ta gyaru sannan ya bar ta.
Akan kafet din falon ta kwanta tana kuka, hannun ta rike da kanta.
Mami ce ta mike ta kawo Sabir lemo da ruwa, sannan ta tahowa da Asma'u ruwa.
Kama Asma'u tayi ta kai ta kan kujera, ruwan ta sha, sannan ta langwabe a jikin Mami sai bacci.
Sai magariba sannan Sabir ya tafi.
*INDABAWA*
[1/18, 14:21] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*
Dedicated to *My Lovelly Momy*
*131-135*
Asma'u kuwa sai Magariba ta tashi. Tana tashi taji kafar ta saki.
Mikewa tayi ta haye sama tai alwala tai sallah. Tana idarwa Yaa Aslam ya kira ta.
Kafar ya tambaye ta ta ce,
"Ai Yaa Aslam sai da aka kara gyara min ashe bai gyaru ba."
"Ayyah sorry my dear da zafi ko. Sorry."
"Yaa Aslam ai zafi har ba'a magana."
"Sannu toh!"
Daga haka suka cigaba da hirar su.
Yau takanas Maimuna ta wanko.kafa tazo gun Asma'u.
Dawowar Asma'u kenan daga Asibiti aka zo akace ta yi bakuwa.
Sakowa tayi. Wa zata gani in ba Maimuna ba. Cikin shigar ta, ta riga da zani sai hijab din ta iya gwiwa.
Asma'u da murna ta karasa wajen ta ce,
"Lallai yau Maimuna ce a gidan namu."
Maimuna tai murmushi ta ce,
"To ina kewar ki ba dole na zo mu gaisa ba."
Gaisawa sukai sannan Asma'u ta kawo musu abinci suka ci suka koshi.
Wajen Mami ta kai ta suka gaisa sannan tace tafiya zatayi.
Dubu biyar Mami ta bata tana mata godiyar ziyar da ta kawo musu.
Har waje ta rakata dan sai da ta hau Napep sannan sukai sallama ta juya gida.
Wata mota ta gani wacce kwanan nan kusan kullum sai ta ganta a layin ta rasa motar wace, ga bakin glass da take dashi.
Motar ta kuma kalla ta shige gida abinta. Sabir dake cikin motar ya yi murmushi ganin ta kallon da ta tsaya yiwa motar.
Ya tabbata ta fara gane da zaman motar a wajen.
Motar ya tayar ya bar unguwar ransa fari tas yaga abinda yake son gani.
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah. Yau gashi sauran wata uku su Asma'u su kammala karatun su.
Yau ma kamar ko da yaushe da yake asabar ce suna zaune, a falo ita da Dady
Dady ne ya kalle ta ya ce,
" *Husnah* ba abinda kike bukata a kara siya miki."
Kallon Dady tayi ta ce,
"Dady da sauran lokaci fa."
"Haka ne, amman na fison komai na gama shi da wuri dan bamu san me lokaci zai bayar ba "
"Haka ne Dady. Amman ni bana bukatar komai."
"Kin tabbata?"
"Eh Dady."
"Shikenan na miki transfer din kudi ta account din ki kingan su."
Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah!"
"Ki duba wayar ki, zaki gani. Dan haka ki ajiye in lokacin bikin yazo in kina bukatar kudi ki huta ba sai kin hau tambayar Mami ko Yayun naki ba."
Murmushi tayi ta ce,
"In ban tambaye su ba ai ina da Dady ko?"
"haka ne! Kina da Ni amman in ina nan ba."
Murmushi tayi ta ce,
"Dady tafiya zaka yi ne?"
Kai ya girgiza ya ce,
"Ko daya in na mutu nake nufi."
Damuwa ce ta sauka akan fuskar Asma'u sosai har ta kasa furta komai.
Dady ya ce,
"Haba *Husnahn Dady* mene na bata rai dan na fadi abunda dole ne ya faru. Ki daina sa damuwa aranki nasan ko na mutu kina da masu rike ki amana. Amman mutuwa tana kan kowa. Kowa lokaci yake jira da tazo kuma bata jira dauka kawai take. Gara duk abinda zamu nayi muna tunawa da ita. Kuma muna sawa a ran mu a ko da yaushe zaata iya zuwa ta dauke mu. Ki daina damuwa. Allah shi ya tsara mana rayuwar mu kuma in yai niyar mutun ya rayu sai kiga ya shekara nawa ma bai mutu ba. Ina iyayen mu duk sun mutu to muma haka wata rana zamu tafi. Fatan mu da addu'ar mu Allah yasa mu cika da imani kuma Allah yasa can ta fi nan."
"Ameen!"
Mami ta fada dan duk tana jin abinda suke fadi.
Murmushi Asma'u tayi ta ce,
"Mami kinga Dady yai ta kawo maganar mutuwa. Mami nifa bana son maganar mutuwan nan."
Dariya Mami tayi ta ce,
"Oh su Asma'u har yau ba a girma ba. To ya zamu Allah ya bamu gadon ta kowa sai ya mutu kuma tunawa da mutuwa yana daura mu akan hanyar Allah yadda zamu gyara kura kuren mu. Ki daina damuwa dan Dady ya kawo magane mutuwa. Yana da kyau ana tinawa da ita."