← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 61

Sashe 30

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami ce ta dago da kan ta ce,
"Oh Asma'u ke haka zaki ta ciwo da kuka. Wai yaushe zaki daina kuka in baki da lafiya."

Hawaye ta goge tana son kawar da damuwar ta.

Mami ta kalle ta sosai ta ce,
"Bayan zazzabin me yake damun ki. Dan ga damuwa nan fal a fuskar ki. In akan Dady ne, dan Allah ki rage damuwar nan Amsa'u kina masa addu'a kinji."

Kai ta gyada.
"Yauwah koke fa, *Husnahn Dady* "
murmushi tayi.

Mami ta dauki ledar da Buhari ya kawo mata ta bude.
Murmushi tayi ta ce,
"To ai ke sai ya narke"

Ta fada tana zaro mata ice cream din daga leda. Daya ta mika mata ta mika.mata kullin naman da ya siyowa kowa nasa.

A firij ta zuba ragowar ice cream din. Sannan ta ce,
"Ina Buharin?"

"Yanzu zai daw......."
bata karasa fadi ba sai gashi ya shigo da sallama.

"Au ina kaje?"
Mami ta tambaye shi.

Kallon Asma'u yayi ya ce,
"Daki fa naje."

Zama yayi a gefen Asma'u ya ce,
"Sis an sa ranar aure na da Zainab fa dan kiji tare za ayi da naku."

Yana fadar haka taji kirjin ta ya buga. Dan har sai da ta dafe shi.

A zahirin gaskiya taji dadi amman kuma bata san me ya haifar mata da faduwar gaban ba.

Murmushi tayi ta ce,
"Kai Alhamdulilah. Amman kuma shine ba a fada min ba."

"Sorry ai kece naga bakya jin dadi."
"Ni ba wani nan Yaya ka sani fada min zai yi sanadiyar samun sauki na. Zan hadu da Anty Zee din ne."

Murmushi Mami tayi ta ce,
"Kaji har baki ya bude ko?"

Daga haka suka ci gaba da hira sosai suka dauke mata kewar Yaa Aslam.

Dan har sha daya suna tare. Sannan. Buhari ya tafi dakin sa. Mami kuma suka. kwana tare.

Washe gari ta dan ji dama dama amman a zuciyar ta ba sauki sai abinda yyai gaba.

Aslam kuwa sai ya tari Dadyn sa da maganar ko kallo bai ishe shi ba.

Dan haka ya tafi gun Wan Dadyn sa. wan Dady kuma ya shige masa akan maganar auren su da Pretty.

Komai da komai akai aka tsaida nan da sati uku za ai biki.

Lokacin da Dadyn Aslam ya samu labari kasa magana yayi.

Dan baisan me zai cewa, Amina ba shi har ga Allah yafiwa Aslam sha'awar Asma'u.

Ko Momyn Aslam kasa mata maganar yayi shi kadai ya dinga juya abin a ran sa.

Aslam ya kira yai masa gargadi akan ya janye batu auren yarinyar da yake son aura amman sai ga Aslam har da su kuka.

Da Dady yaki sauraron sa mma sai ya zube ya suma a gun.

Da sauri Dady ya fita dashi asibiti hankalin sa a tashe.

*Alhamdulilah*
Anan na kawo karshen littafin. *LABARIN RAYUWAR Asma'u Husnah* *Part 1* Sai ku saurare ni dan jin karashen sa.

Anan ne zamuji Shin Aslam yana auren Pretty ko Asma'un yake aura.
Sannan zamuji Yadda Sabir zai kasance.

Anan nake muku fatan alheri tare da cewa mu hadu a *LABARIN RAYUWAR* *Asma'u Husnah PART 2*

Ina son naga comment sosai tukkinna.

And pls don't forget to vote @MSindabawa

*Nagode masoya na. Allah ya bar kauna*

HHHHH YA KUKA JI. FAN ALLAH KUYU HAKURI AKAN YANAYIN LITTAFIN KOMAI A TSARE YAKE ZAKUJI DADIN SA SOSAI

*Muje zuwa*

YANZU AKA FARA.

Godiya ga masoya masu bibiyar littafi na. Bazan manta dake ba *Ummu Ayda, fadeelat, bela'u, sis Kibdiyya, Fatitih, namesake, Asmy, Husnah, and also u Mahee Abdullahi kai kuna da yawa da yawa nagode nagode da bibiyar littaffin man da kuke. Allah ya bar kauna nagode*

Muje zuwa

*INDABAWA*

[1/18, 14:26] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
  *Asma'u Husnah*

*part 2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*

Dedicated to *My Lovelly Momy*

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

*Alhamdulilah.*
Allah nagode maka da ka bani ikon fara cigaba da karashen littafin *Asma'u Husnah* Allah ina rokan ka da ka bani ikon kammala shi lafiya kamar yadda na fara lafiya.

Masu korafi akan littafin kucigaba da bibiyar sa zakuyi komai.

*Mahaifiya ta farin cikin rayuwa ta. Mahaifiya ta hasken idaniya ta. Allah dada lafiya da nisan kwanan Momy Ameen*

Allah ka jikan *Mahaifina, da dukkan musulmai baki daya.

*Kannena farin ciki na. Allah bar min ku. *Nusaiba and Hauwa'u (Yasmeen)*
One love.

Ina mika gaisuwa ta ban girma gare ki yar uwa Anty nah. *Rashida Abdullahi Kardam* Allah ya dafa Allah ya karawa Mama lafiya. Allah baki miji nagari da zuri'a daiyaba. Ameen.

Sai sakon gaisuwa ta ga *Hajiya Nafisa* Momyn mu. Allah ya kara girma ya kara lafiya da arzuki ya Allah ya raya zuri'a. Ameen.

Sai gaisuwa ga Dukkan nin yan uwa marubuta musam yan kkungiyar HAJOW tare da yan uwan abokan azurki masoya. Allah ya kare mana ku Ameen.

Masoya nagode da kaunar ku a gareni nima ina kaunar ku.

Allah marasa lafiya na gida dana asibiti Allah ya basu lafiya. Allah ka daukaka musulunci da musulumai. Allah ka karya kafirci da kafirce.
*Ameen*

Bari mu shiga cikin karashen littafin dan muji abinda zai faru.

*1-5*

Ganin halin da Aslam. ya shiga ba karamin dagawa Dady hankali yai ba.

Amman duk da haka ya ce bai yadda Aslam ya auri Pretty ba.

Aslam kuwa ba karamin tashin hankali ya shiga ba. dan jinin sa ba karamin hawa yayi ba.

Momy da batasan me yake faruwa ba yasa ta shiga tashin hankali na rashin ganin Aslam ba.

Dady ta tara dan ganin bata ga Aslam ba har dare.

Dady ne ya fada mata duk abinda ya faru.

Momy mamaki ta tsaya yi yanzu abinda Aslam ya zaba kenan.

Zama Momy tayi ta dafe kan ta. Dady ne ya zauna kusa da ita ya kamo hannun ta.

Kallon sa tayi idon ta jajir ta ce,
"Dadyn Aslam ya zan yi da Asma'u. Kai kan ka shaidane akan soyayyar dake tsakanin su. Ban san me ya samu Aslam ba har haka ta faru. Amman ka min izini gobe na tafi kano naji me yake faruwa."

"Ba komai. Ki kwantar da hanaklin ki. Na amince kije Allah ya kyauta."
"Ameen!"

Kwana Aslam yai a asibiti dan Dady ko wajen sa bai koma ba.

Sai Pretty ya kira ya ita ta kwana a wajen sa.

Washe gari Momy ta daga zuwa Kano.

Asma'u ce kwance zazzabi ya rufe ta dan jikin ta kamar wuta.

Sai rawar sanyi take, idanun ta sunyi jajir dashi.

Mami ce ta shigo dakin rike da wani dan bowl da karamin towel a hannun ta.

Zama tayi a gefen Asma'u ta yaye bargon da ta rufa dashi.

Hijab din jikin ta ta cire mata ta matsa kusa da shi ta na tsoma towel din a cikin ruwan ta dauko ta matse sannan ta saka mata ajiki.

Wata ajiyar zuciya ta sauke, tana mme bude idon ta da sauri.

"Sannu!"
Mami ta fada tana cigaba da Shafa mata ruwa a jikin ta.

Sallamar Momy, Mami ta jiyo daga sama. Ajiye ruwan hannun ta Mami tayi ta mike ta fita.

Ganin Momy yasa ta saki fara'a ta ce,
"Anty nah Oyoyo."

Ta rumgume Antyn tata.
"Mu shiga dana ciki."

Suka shiga dakin Mami inda Asma'u ke kwance.

Momy na shiga taci karo da Asma'u kwance da sauri ta karasa wajen ta ta ce,
"Asmy na lafiya?"

Ido Asma'u ta bude jin muryar Momy. Da sauri ta mike tana sakin murmushi. Idon ta kamar zafin wuta saboda haka kanta yake sara mata dan har harbawa yake.

Zama Momy tayi agefen ta tana kamo hannun ta. Ta ce,
"Asmy bah lafiya ne?"

Murmushi Asma'u tayi ta ce,
"Dan zazzabi nake."

Momy ta kalli Mami ta ce,
"Tin yyaushe kuma amman baki fada min ba."

"Yi hakuri Anty, Wallahi kwana ta uku ke nan."

Kallon ta, ta maida kan Asma'u ta ce,
"Sannu Baby nah. Kunje asibiti."

Mami ce ta ce,
"Kinsan Amsa'u ai, tana likita amman bata son shan magani."

"A'ah haka bazatai yiyu ba. Tashi muje."
Ta mike tana daga Asma'u

Mikewa Mami tayi tabi bayan su. Asibitin Malam Aminu Kano suka tafi. Suna zuwa suka wuce Emergency.

Suna zuwa suka shiga ganin likita da yake suna da hanya.

BP ta ya auna, sannan ya dauki jinin ta, ya auna.

Gado ya basu ya ce, sai ana mata karin ruwa.

Buhari suka kira suka fada masa suna asibiti.

Sosai Doctor yayi musu fadan akan me jinin Asma'u da ya ga ya hau.

Mami ta rasa me yayi sanadin haka ita gani take kawai damuwar rashin Dadyn ta ce.

Momy ce ta hau tunanin ko dai sun ssamu matsala da Aslam ne shiyasa hakan ta faru.

Nan da nan sai ga Buhari yazo. Lokacin Asma'u na bacci.

Zama sukai ranar a asibiti suka yini sai gab da magariba aka ssallame su suka tafi gida.

Suna shiga gida Mami ta shiga kitchen. Asma'u kuma Momy ta hada mata ruwan wanka ta shiga tayi.

Tana fitowa ta saka kayan baccin ta sannan ta tada sallah.

Momy ma sallah tayi sannan ta zauna tana kallon duk wani mmotsin Asma'u.

Tin aa hanya take fama da kiran wayar Aslam bai dauka ba.

Yanzu ma kiran nasa ta karayi. Ganin bai dauka ba ta fara zargin ko lafiya.

Wata ta ce, lafiya kalaou da ba lafiya zai kira ya fada mata.

Wata zuciiyar kuma ta ce ko wayar sa aaka dauke. Nan ma ta ce da zai sanar da ita.

"To ko nai masa wani abun ne?"
Ta tambayi kanta. Kai ta girgiza ta ce
"In haka ne da zai sanar dani."

Shiru tayi tana son ta gane me yake faruwa amman ta kasa.

Har akai isha'i tana zaune a inda take mikewa tayi tai sallah.

Sai da ta idar tai addu'a sannan ta kalli Momy da ta idar da sallah itama.

Ta ce,
"Momy ya Aslam kuwa lafiya ina neman wayar sa bana samu."

Kallon ta Momy ta yi ta ce
"Tin yaushe kuma?"

"Yau wajen kwana biyar fa rabon da muyi waya. Bayan Yaa Aslam kullum sai munyi waya dashi."

Kallon ta Momy tayi ta tausaya mata ta ce,
"Kuma ba abinda yya hada ku."

Kai ta girgiza ta ce,
"Lafiya muka rabu da shi."
Chapter 30 · 0% Book details