← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 61

Sashe 7

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Durkusawa yayi har kasa.
"Mami ina kwana. Da fatan an tashi lafiya?"
"Lafiya lou. Ya ka tashi."

"Lafiya Alhamdulilah! "
"To jeka maza ka kaita makarantar daga nan ka wuce aiki zan aiki driver ya kawo maka abincin ka kaga ta makara."

"To Mami sai na dawo."
"Allah kiyaye hanya Allah muku Albarka."

"Ameen!"
Ya mike ya fice, komowa *Asma'u* tayi ta rumgume Mami ta mata kiss (sumbatar) a kumatu.

Ta sake ta tana.
'Bye bye Mami."

"Bye Ayi karatu sosai banda kula kawayen banza."
"Insha Allahu."

Ta fada tana fita a guje tana mata bye bye da hannu.

Murmushi Mami tayi, dan *Asma'u* akwai ta da hankali ga nutsuwa, bar ta dai da tsokanar yayan ta amman komai nata cikin burgewa take yin sa.

Baka ce *Asma'u* Kamar yadda Dady yake baki, shi kuma Ya Buhari fari ne ya dauko Mami.

Amman komai na fuska da zubin jiki me kyau na Mami ne, dan Mami akwai diri hakan yasa ita ma *Asma'u* tana da diri me kyau.

Kamar yadda shi kuma Ya Buhari ya dauko zubin jikin dadi dan dogune, sannan jikin su a murde yake, suna da dan jiki dai dai gwargwado.

Bakin *Asma'u* bai mata muni ba sai kyau da ya kara mata. Dan Bakin ta me kyau ne, irin chocolate colour haka fatar ta take me kyau da taushi.

Kowa na sha'awar kalar fatar ta.

Kai ta jin jina.
"Allah bada sa'a."
ta fada a fili tana yin dakin Dady.

Tana fita har ya shiga mota. Da gudu ta karasa ta bude gidan gaba ta shige.

Hanya suka dauka. Cikin minti ashirin sun karasa makaranta. Har kofar department ya dire ta sannan ya juya.

Tana karasawa kofar hall din su ta hange, sa a gaban aji.

Sanye yake da ruwan madarar shadda wacce akai masa dinkin riga wacce da kadan ta wuce gwiwa da dogon wando.

An masa aiki a jiki da dark brown (ruwan kasa) zare sai dark brown hula da takalmi dake kafar sa.

Ta jima tana kallon sa, Sai bayani yake zuba musu. Daga bisani ta buya daga gefe dan kar ya ganta.

Tinda ya mata kashe din kar ta matso masa kofar aaji muddin ta makara.

Tana daga taga tana jiyo muryar sa, me sanyi da dadin sauraro. Sai da taga ya kusan fitowa sannan tabar kofar hall din.

Ya fito ya tsaya a kofar ajin yana kallon ta, duk da ta bashi baya amman ya tabbata ita ce.

Ya jima yana kallon ta ko zata juyo amman ina ko juyowa batai ba kamar tasan yana wajen.

Wajen ya bari ya nufi Office din sa. Yana bawa wajen baya tana juyowa bayan sa ta tsaya kallo.

Kai ta girgiza ta juyar da kanta. Zainab ce ta karaso wajen.
"Sannun ki, kin kyauta."

"Wallahi bansan lokaci ya tafi haka ba."
"Haka dai kullum bayan kin gama tsokanar ki ko."

"Ni yau ban tsokane sa ba."
"Ke din kuwa."

"Eh!"
Dariya zainab tayi,

"tashi ki rakani na siyo lemo dan Allah."
Mikewa tayi suka nufi cafeteria. Sai da suka siyo lemo sannan suka dawo.

Wajen da suka saba zama nan suka zauna gefen hall (dakinn daukar darasi) din su karkashi wata bishiya.

Suna zama, sai ga kiran Ya Aslam nan.
"Assalamu Alaikum!"
"Wa'alaikum salam!"

"Love!"
"Na'am Yayana ya hanya?"

"Hanya lafiya gashi har nagama komai yanzu sai gida, shine nace bari na karaso naga Queen of my heart."

"Wow! Amman kuwa da ka kyauta."
"Gani nan shigowa ckul din."

"Sai ka karaso."
"Aha."

Ta kashe tana murmushi.
"Waye zezo?"

Zainab ta tambaye ya.
"Ya Aslam ne."

"Oh Allah kawo shi lafiya."
"Ameen!"

Yan department din sune suka karaso wajen su uku. Hafsat, Amina da Khadija.

Bayan sun gaisa suka zauna. Hafsat sai hade fuska take Suna dan taba hira. Amman ita ta hade rai

Zainab ce ta ce,
" *Asma'u* wannan week end din zamu zo gidan ku, zamu kawo miki IV Fadila."

"Eh daman ai ke bakya zuwa gidan mu sai da dalili wai ke kunya."

Khadija ce, ta sa baki.
"Ke zuwa kike."

Murmushi Zainab tayi.
"Yauwah tambayar min ita dai."

Amina ce tace,
"Yo ke ina ruwan ki. Sun fi kusa kuma kowa yasan zee bata son zumunci."

Dariya Zainab tayi,
"Ai ita tasan ina da zumunci tasan kuma me yasa yanzu na daina zuwa gidan su."

Tsaki *Asma'u* tayi,
"Wai fa dan Yaya Buhari saurayin tane shine fa."

Khadija tace
"To kunji dalilin ta ko."

"Wannan ba dalili bane,"
Cewar Amina.

"Yauwah yar uwa."
*Asma'u* ta fada tana wa Zee gwalo.

Zuwan wata katuwar mota shi yaja hankalin su banda *Asma'u* da tayi kasa da kai tana wasa da wayar ta.

*Morning yan uwa ya kk ya gd da iyalai.*

Pls don't forget to vote @Msindawa

*MUJE ZUWA*

*INDABAWA*
[1/18, 14:09] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
 ASMA'U HUSNAH

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJWO* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

*Gidan Hakuri da juriya tare da kawar da kai, gidan zaman lafiya. Na gaida ku.*

*36-40*

Dedicated to My great *Mamah* Allah ya jikan ki ba dan kin mutu ba.

Allah kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka.

Nagaida ke mahaifiya ta abar alfahari na.

*Manzon Allah (SAW) ya ce,
Idan zaka so mutum kada ka nuna masa tsananin so.
in zaka kisa kada ka nuna masa tsananin ki.

Dukkan su hankalin su ne yayi kan motar, banda *Asma'u* da ta daukar da kan ta, tana wasa da wayar ta.

Khadija ce ta fara magana, ta ce,
"Kai motar nan ta hadu amman."

Amina tace,
"Ai daga duk kan alamu, ma na cikin ta zai fi haka hauduwa."

"Gaskiya kan motar ba karya, ko wane dan gayun ne a ciki."
Hafsat ta fada

"Ni kam ba ruwana da na ciki sai motar da ta burge ni."
Zainab ta fada.

"Kai Allah bani irin motar na."
Hafsat ta fada.

"Hassada kike yi tinda kika ce Allah baki irin ta sai dai kice Allah baki finta."
Amina ta fada.

"Duk karya ne irin haka nan, dan kaga Abu ka roki Allah yabaka irin sa shine haka."
Zainab ta fada tana tabo *Asma'u*

" *Asmy* kalli waccen motar amman tayi kyau wallahi."

Kai ta dago ta kalli motar, ji tayi gaban ta ya fadi.
"Eh tayi kyau."

Ta fada tana mikewa sakamakon kiranta da ake yi.

Can gefe ta koma jikin wata motar, ta dauki wayar.

"Hallo my beauty! (Kyakyawa)"
"Ya Aslam wannan ai tsokana ce."
amsa ta amsa masa da muryar shagwaba.

"Wacce tsokana nayi."
ya tambaya

"Wai beauty!"
ta bashi amsa.

"Oo Ke ba kyakyawar bace."
Ya tambaya.

Ta ce,
"Gaskiya ni ba kyakyawa bace. Wannan ai sai kasa ayi min dariya."

"Ba wanda zai miki dariya kinji, saboda kyan ki ba kowa ke da irin shi ba. Kina da wani kyau wanda kafin a samu mutum me irin sa ake dade wa. Ur skin is fresh with a beauty colour. (Fatar ki a murje, me kala me kyau)."

Ta ce,
"Uhmm please stop dis joking I beg you. (Dan Allah daina wannan tsokanar na roke ka."

Murmushi yayi ya ce,
"Wallahi I am not joking, I am telling the true. (Ba tsokanar ki nake ba ina fadan gaskiya ta ne.)"

Baki ta turo ta ce,
"Naji ya isa, ka karaso ne,"
"Eh! Gani kina ina ne."

Ta ce,
"Ina kofar department din mu,"
"Nima ina wajen."

"Kai ya Aslam!"
ta fada.

"Da gaske ina wajen."

"Ta ina."
"Ina cikin wata Ash marsandi."

"Oh na ganka. Ina ta bayan ka."
"To kizo man."

"A'ah Yaya please kai ka fito."
"To gani nan."

Baya ta juya masa.

Kofar motar ya bude, wani sanyi da kamshi me dadi ne ya fito.

Kafar sa ya ziro kasa. Safa ce da takalmi sau ciki bakake a kafar sa.

Daya ya diro sannan ya fito gaba dayan sa. Suit ce a jikin sa, ruwan kumkumadi.

Ya cire ta saman sai yar ciki da ya rage. Tin daga kafar sa na fara kallon sa inayin sama. har na karasa kirjin sa wanda yake a bude dashi na kirar cikaken namiji me jini a jiki wanda ya cika namiji.

Kan fuskar sa na gangara. Fuskar sa me kyau ce doguwa fari ne tas dashi, sai manyan idanu wadan da suke a lumshe, wanda ake ce musu (sexy eye)

Bakin shi dan karami ne, wanda yake da lebe me taushi gasu pink sai kwalli suke. Kansa cike yake da suma, kamar ta indiyawa.

Sai saje dake gefen fuskar sa, wanda ya kara fito masa da kyaun fuskar sa. Idon sa sanye da farin gilashi.

Masha Allah wannan gayen duk inda ake neman cikaken namiji me kyau da kwarjini ya kai ya ma wuce nan.

Yan mata da yawa kallon sa suka tsaya yi sai gulmar sa akeyi. Dan ya gama haduwa ba karya.

Waige waige ya farayi dan neman inda take, duk da ta juyar da kanta sai da ya gene ita ce. Dan duk jikin sa ya gama shaida masa, *Husnah* sa ce.

Cikin tafiyar kasaita da nuna kalama tare da nutsuwa yake tafiya.

Sannu a hankali har ya karasa gefen ta. Ta bayan ta ya zaro hannayen sa dake cikin alhiju ya rufe mata idanu.

Jin an rufe mata ido da hannu me laushi, ga kamshin turare dake tashi, tasan Ya Aslam ne.

Murmushi ta saki me sauti.
"Haba My Hero, ai nasan kai ne."

Hannun sa ya janye ya maidasu kan kafadun ta ya juyo da ita.

Kasa magana yayi ya kure ta da idanu.

Ido ta kashe masa guda daya.
"Yah dai."

Yawu ya hadiye tare da sauke ajiyar zuciya yana me sakin wani murmushi dake karawa fuskar sa kyau.

Wani kallon soyayya yake aika mata dashi.

Ba karamin kyau sukayi ba.
"Baby nah kinyi kyau fa."
ya fada yana kara kallon ta.

"Zaka fara ko?"
Ta fada tana nuna masa wasu kujeru da aka gina su.
Zama yayi ita ma ta zauna.

"Sannu Yaya nah Ya hanya?"
ta tambaya cikin kulawa.

Ya ce,
"Hanya Alhamdulilah."

"Sannu toh!"
"Yauwah! Naji dadin zuwa na dana ganki Sweetheart, kin kara kyau, ashe duk hoton da nake gani rage min kyaun ki yake yi."

"Yayana kenan yasu Momy."
ta fada tana wasa da yatsun hannun ta.

"Suna lafiya."
Ya fada yaba dago face din ta.
Chapter 7 · 0% Book details