← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 61

Sashe 48

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yadda tayi baki, ta rame, ga yaro ko a ina ta samo shi.

Bacci sosai tayi dan har akai magariba tana bacci.

Sai da Dady ya dawo suka shiiga da Mommah ce ta same ta tana zaune, tana bawa danta nono.

Tana ganin Dadyn ta ta mike. Dady ne ya karasa ya amshi yaron hannun ta.

Magana yai mata amman da ta bude baki zata bashi amsa dai ta kasa magana.

Har kuka tayi dan jin ta kasa magana. Dady na ganin haka ya samo malami yai masa bayani.

Addu'a aka kara mikewa da ita da rokan Allah.

Cikin hukuncin Allah sai ga Preety na magana.

Anan ne take fadawa Dady duk abinda tayi da raba Aslam da Asma'u da bin malaman da take.

Har da auren da sukai da boka wannan yaro kuma dan ta ne da boka,

Bata taba zaton zata kubce daga wajen boka ba.

Sai rana daya ta ganta ta samu hanya har ta fito.

Bara tayi sannan ta samu na mota. Da kyar wata motar koso tumakai ta dauko ta.

Acikin wajen da tunakrn suke ta zauna duk da wajen kashi da fitsarin su ne.

Da haka suka karaso har kano aka sauke ta.

Da kyar ta samu ta karaso Abuja. Take fada musu a kafa ta karaso gida.

Jikin ta kuwa yayi wani iri kamar konuwa ga kaikayi.

Asibiti Dady ya fara kkai ta amman ina abin ba na wasa bane.

Da aka basu wasu gwaje gwaje aka gano tana dauke da cutar kanjamau.

Dady sosai ya razana. Preety kuwa kuka ta dinga yi tana dana sanin abinda ya faru.

Haka suka koma gida bayan an basu ranar da zasu na zuwa ganin likita da amsar magani.

Sosai Pretty ta razana da rayuwar duniyar nan, Ganin yadda take da amman yanzu ji yadda ta koma.

Ji dan da take riki dan shege, kuma ma na boka wai.

Haka nan ita ce ke dauke da kanjamau, yanzu wa zai aure ta.

Lallai *Duniya abar tsoro*

*MS Indabawa*
[1/18, 14:37] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

?? *HAJOW* ??
*Hakuri da juriya Online writer's*

Dedicated to *My lovelly Mum*

*86-90*

Yau ta kama kamu Asma'u ansha lalle da gyaran kai.

Duk da a kwance take sosai dan yanzu haka ma wani irin ciwon kai da zazzabi ke damun ta.

Tana kwance Zainab ta shigo da mai kwalliya ta ce,
"Asma'u tashi mai kwalliyar tazo."

Da kyar ta iya mikewa idon ta jajir ta shiga bayi. Kasa sakawa jikin ta ruwa tayi sboda sanyin da take ji.

Fitowa tayi ta saka kayan da zata amfani dasu. zama tayi aka farai mata kwalliya.

Yar kadan akai mata amman ba karamin kyau tayi ba.

Ana cikin mata dauri Nusaiba ta kira ta. Dagawa tayi murya a sanyaye ta ce,
"Amarya"

Dariya Nusaiba tayi ta ce,
"Amare dai. Ya kunyi kamun ne, nifa har na gama shiri fita kawai zanyi. Yanzu Uncle Sabir ya kira ni wai ya muka tsara dinner nace ai ni ke na barwa komai."

"Uhmm kema dai. Ni ba wata dinner da zan yi. Yazo nan kawai."

Nusaiba tace,
"Ke kin isa ma. Kinji ana jira na bari naje mayi waya anjima."

Ta katse wayar. Kallo ta bi wayar da shi ta ce,
"Oh wai wannan ce kishiya ta. Ita sai murnar bikin take yi."

Maryam ce ta kira ta. Ta ce,
"Anty kiyi hakuri sai gobe zan taho yau zan tsaya wajen kamun Nusaiba. Jibi wai za ai dinner."

Asma'u tace,
"Nifa ba wata dinner da zanyi."

Shiru Maryam tayi a ranta tana tunani ko Asma'u bata son a hada musu dinner su biyu ne.

Sallama sukai tayi wajen Momyn ta tana fada mata gwara kowa yayi event din sa kar a wani hada.

Haka kuwa akai dan Mamahn Sabir ma haka tace kowa yai nasa.

A wajen Kamu kuwa Asma'u sai rawar sanyi take ga ciwon kai.

Anyi hotuna da kawayen su da yan uwan Dady da Mami.

Inda kafin a tashi jikin Asma'u yayi zafi kamar wuta.

Nan da nan Momy tasa aka maida ita gida. Ciwo sosai ta kwanta.

Washe gari akai Monday's even Amman Asma'u da kyar ta iya zuwa.

Asabar dinner amma ranar a kwance sosai Asma'u take dan har asibiti aka tafi da ita.

Riketa sukai suka bata gado ana mata karin ruwa. Dinner dai da ba ayi ba kenan.

Rannar lahadi da safe aka daura auren Asma'u duk da tana asibiti lokaci nayi taji wata faduwar gaba.

Kuka ta sawa Momy dake wajen ta.

Momy sai lallashi take yi. Ba wanda yazo asibiti a ranar sai Zainab.

Shima abinci ta kawo fuskar ta dauke da fara'a sai tsokanar Asma'u take wai ta kwanatr da hankalin ta ta samu abinda take so ta mike.

Kiran da Mami ke mata yasa ta mike ta tafi ba tare da ta cigaba da tsokanar Asma'u ba.

Asma'u kam zuciyar ta ta gama karaya ta rasa Yaa Aslam kenan.

Da dare aka sallamo su gida suka nufa dan gidan ma har ya rage jama'a.

Dakin ta aka kai ta. tana kwance akan gado duk ranta a bace.

Zainab ce ta shigo ta ajiye roba sai karamin towel a gefe. Saboda jikin ta yai zafi za a fan sa mata ruwa.

Kai ta dauke ta lumshe idon ta. can taji an bude dakin. A hanakli taji ana taciya har aka karaso bakkin gado.

Bata san waye ba dan haka ta kara gyara kwanciyya. Roba taji an dauka an tsoma towel a ciki.
Ji tayi an tada ta zaune, ana cire mata kayan dake jikin ta.

Karamin wandon dake jikin ta kawai aka bari. Ido ta kara lumshewa. Saboda bata son bude su fan yadda suke mata zafi.

Jin an soma goga mata towel ta ajiye wata uwar ajiyar zuciya.
Ji tayi ana ta goga mata ruwa a jikin.

Shiru tayi abu daya taji shine, an fi goga mata a kirjin ta. Duk da haka batai gigin bude ido ba.

Can kuma sai taji kamar kamshin Yaa Aslam amman kuma sai ta tuna baya garin ma.

jini shirun yai yawa yasa ta a bude idon ta a hankali. Waza ta gani?
Yaa Aslam ta gani durkushe a gaban ta.
Ido ta zaro ta mike da sauri. Murmushi ya saki.

Bandaki ta shiga da gudu tana dafe da kirjin ta.
Ta jima a bandakin tana kukan da ta rasa dalilin name ne.

Sannan kuma tana mamakin taya Yaa Aslam ya shigo har ya ke shafa mata ruwa.

Ta jima a bandakin tana kuka ita kadai  dan har sai da taji Zainab ta shigo tana kiranta.

Fitowa tayi daure da towel tana rawar sanyi. Dan wani zazzabi ne ya kara ta yar mata.

Kayan bacci ta fito ta saka. Har ta kwanta Zainab ta ce, taje falo ana neman ta.

Hijab ta dauka ta saka ta mike ta fita a hankali kirjin tane bugawa.

Falo ta fito jiki a sanyaye dan wani zazzabi take kara ji. Kan ta kuwa kamar zai rabe gida biyu.

Ta shiga falo taga Mami da Momy sai Uncle Habu (kanin Dady) sai Yaa Buhari da Sir Sabir. Taji dadi da bata Aslam a dakin ba.

Dukkan su murmushi ne akan fuskar su sai hira suke.

Kirjin ta ne ya buga ta ce,
"Allah yasa ba cewa za'ai na fito mu tafi ba."

Karasa wa falon tayi ta zauna a gefen Uncle Habu.

Mutanen dakin ta gaisar daya bayan daya sukai mata sannu.

Kasa tayi dakai. Uncle Habu ne yai gyaran murya ya ce,
"Alhamdulilah Asma'u yau Allah ya nuna mana ranar Auren ki. Muna fatan zaki zama mace ta gari a wajen mijin ta. Kafin nan Asma'u. Asma'u duk abinda ya faru gareki ki dauka taki kalar Kaddara ce."

Yai shiru, sannan ya ce,
" Auren ki dai bai dauru da Sabir ba."

Dagowa tai da sauri ta kalli Uncle Habu sannan ta kalli Sir Sabir.
Murmushi ya sakar mata. Uncle Habu yacigaba da magana,
"Yau a wajen daurin aure anzo daura auren ku Sabir ya dakatar ya ce, a daura auren ki da yayan ki Aslam."

Nan ma da sauri Asma'u ta dago tana kallon Sabir tana girgiza kai.
Murmushi ya sakar mata, yana mai girgiza mata kai ganin hawaye na shirin fitowa daga idon ta.

Uncle ne ya cigaba da magana ya ce,
"Ko da na tambaya akan me za'a fasa da shi sai ya kawon dalilan sa kamar haka:- Sabir ya ce, Uncle ina son Asma'u amman nafi son samuwar farin cikin ta. dole na hakura da ita tunda suna son juna su ita da Yaa Aslam. Dan ciwon da Aslam ya kwanta ma akan tane, haka ma kema kina son sa."

Kai Asma'u ta fara girgizawa, Uncle yace, haka
"Haka sabir yacigaba da bani dal'lan sa. Ya ce, Na yadda Yaa Aslam na son ta kuma in na aure ta mutum biyu zasu rasa farin cikin su. In ni na hakura ni kadai ne zan ji ba dadi kuma nima na lokaci ne tinda na samu wacce ke sona tsakani da Allah. Nagodewa Asma'u dan ita tai min wannan gatan bazan taba mantawa da ita ba. Ina son Asma'u amman na hakura da ita Allah bata zaman lafiya da mijin ta."

Kukan da Asma'u take boyewa shine ya fito fili ta fashe da kuka.
Zainab da shigowar ta kenan ta karaso tana lallashin ta.

Uncle ya ce,
"Ki daina kuka ki godewa Allah. Ina miki fatan Alheri Allah ya baki zaman lafiya. Ina farin ciki yau burin Yaya Suleiman ya cika. To Allah ya tabbatar da alheri. Ki kula da mijin ki. Allah miki Albarka."

Ya mike ya fita. Mikewa Momy da Mami sukai suka fita.
Haka ma Yaa Buhari ya mike ya fita, bin bayan sa Zainab tayi ya rage daga Asma'u sai Sabir.

Mikewa yayi ya karaso gefen ta. Ya ce,
"Haba Husunah mene na kuka. Ki godewa Allah da ya sa na gane irin son da Aslam yake miki na tabbata Aslam na kaunar ki fiye da yadda nake kaunar ki, akwai dalili mai karfi da ya hana shi auren ki a baya zai iya zama ko bayin kan sa bane."
Chapter 48 · 0% Book details