← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 61

Sashe 34

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tin da Dady ya bayyana, min son ka akan kai ne, mijina baka ji yadda naji ba. Saboda Allah yasa ga wanda nake so aka hada kaga yafi dadi ko."

"Shiyasa nacewa Dady kar a fada miki sai na kama bakin zaren!"
"Wane zaren kuma"

Ido ya kashe mata.
"Zuciyar ki man. Hmmm *Husnah* baki san yadda na riki soyayyar ki a raina ba. Ta zama abin yi dare da rana. Soyayyar daraja ne da ita. Samun irin taki shine burin ko wane me hankali. Bana son na taba yin nesa dake. Kin shiga zuciya kinyo kafuwa. Ni dake babu rabuwa koman dadewa."

Kallon sa ta tsaya yi.
"Kai ma kasan kaine zabin rai na. Zuciya ta, ta adana soyayyar ka ba wanda ze maye gurbin ta. Sa'a ni na sama tinda na samu gwarzon masoyi kamar ka. Kai ka ke sani addu'ar neman miji na gari, kuma nasan Allah ya amsa min da ya aikon da kai a matsayin masoyi wanda nake fatan shine miji na."

"Gaskiya ne. Dace da masoyi shine ribar soyayya. Nasan sabon da mukayi ni dake sai dai a kira mu tagwaye, ko yaushe in na tina ki nakanyi murmushi da jin frin ciki a cikin zuciya ta."

Murmushi tayi, ta sauke ajiyar zuciya me karfin
"Lafiya?"

Ya tambaye ta.
"Ya Aslam in na tuna da rabuwa ne sai naji zuciya ta tayi min rauni"

"Haba *Husnah ba mun kashe wannan maganar ba ne."
"Eh!"

"To Bazamu rabu ba sai dai mutuwa itama insha Allahu tare zata dauke mu."

"Allah yasa!"
"Ameen."

"Yauwah kinga tin yanzu sai mu fara tsara yadda bikin mu zai kasance ko?"

****---****
Kuka ta fashe da shi tina wannan hirar tasu.

Ta ce,
"Ni na gama amince maka Yaa Aslam amman me nai maka kake min irin wannan horan. Wallahi nasan in har nan da wani lokaci Yaa Aslam bai dawo gare ni ba komai zai iya faruwa da zuciya ta."
Ta fada tana kara fashewa sa kuka.

Dan a yadda take jin zuciyar ta ji take kamar zata fashe.

*INDABAWA*
[1/18, 14:28] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
     *Asma'u Husnah*

*part 2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*

Dedicated to *My Lovelly Momy*

*Last page nayi mistaking wajen page number zan sa 6-10 na saka 11-15 ayi hakuri wannan shine 11-15 wancan 6-10 ne nagode*

MASOYA MASU BIBIYAR WANNANN LABARIN NAGODE KWARAI DA GASKE. ALLAH BAR ZUMUNCI. COMMENT DIN KU NA DADA MIN KWARIN GWIWA NAGODE.

*11-15*

Kuka ta kuma fashewa da shi ta ce,
"Meyasa? meyasa? Meyasa yaa Aslam? Me nayi maka da na cancanci haka."

Ta kuma fashe wa da kuka dan har numfashi ta na sarkewa.

Mami ce ta fito ta tadda ta a hankalin da take ciki.

Da sauri ta karassa gun ta. Ina har numfashin ta ya dauke

Da sauri Mami ta kira suka tafi da Asma'u asibiti.

Aslam kuwa ana can yau daurin aure. Duk da yau take ranar farin ciki a gunsa amman sai akasin haka.

Dan damuwa sosai ya shiga na tinawa da tini da Asma'u ake daura auren nasu.

Duk yadda yaso yai farin ciki ya kasa. Abokan sa kuwa dayawa duk basu je daurin auren ba dan ya riga ya koya musu son Amsa'u.

Dukkan su mamaki suke sosai. Wasu kuma haushin Pretty suke ji.

Wasu daga cikin abokan sa su suka hallaci daurin auren.

Bayan an gama reception ya koma gida ne ya kwanta a daki.

Ba abinda yake gani sai Asma'u da ke masa murmushi.

Ido ya lumshe, ya rasa me yake damun sa.

Gani yake kamar a mafarki wai ya auri Pretty. Mamaki yake sosai amman kuma sai wani abu ya dauke hankalin sa daga wannan.

Haka da dare aka kai amarya gidan ta. Dan Mami ta ce bazai saka kowa a gidan da ya gina dan Asma'u ba.

Wani daga cikin gidan shi yasa aka gyara akai wa Pretty kafin kayan ta.

Amarya kamar ba amarya ba dan mayafi ma a kafada ta yafa aka raka ta gidan ta.

Aslam kuwa lokacin yana gida a kwance ya rasa me zai yi.

Mami da kanta taje ta same shi a daki.

Duk da ganin yanayin da yake ya bata tausayi amman hakan bai sa ta ce,
"Ka tashi ka tafi gidan ka. Ga amaryar ka can an kai maka ita."

Shiru yayi kamar bazai yi magana ba. Sai kuma ya sauko daga kan gadon ya durkusa a gaban ta ya ce,
"Momy dan Allah ki yafe min. Momy wallahi ban san abinda yake damu na ba."

Kai Momy ta dauke, Kuka ya saka yana nema yafiyar Momy.

Kallon sa tayi ta tausaya masa ta ce,
"Ba komai kaje Allah bada zaman lafiya. Amman har ga Allah bana son auren nan naka."

Kin sakin ta tayi sai da Momy ta daga sa tace,
"Kaje ka shirya dare nayi."

Mikewa yayi ya shiga bandaki. Ya fito ya shirya cikin sky blue din shadda. Yayi masifar kyau.

Wanka da turare yayi sannan ya fita falo.

Momy bata nan dan haka yayi bangaren ta. Ko da ya taba kofar a rufe take.

Dan haka ya juya ya fice, motar sa ya dauka ya fice daga gidan.

Gidan shi ya wuce kai tsaya. Gidan ne babba wanda yake dauke da babban falo sai kofa da take kallon gabas ita ce in an bude za a shiga bangaren Pretty, Da katon falo sai bed room guda biyu da kitchen da bandaki.

Gidan yayi kyau sosai. Sai dayar kofar dake kallon ta Pretty shine bangaren Aslam benene.

Shima katon falo ne sai Bed room guda biyu kamar yadda bangaren Pretty yake.

Sai wajen gidan kato ne, dan bayan gidan da an shakatawa ba kamar dayan gidan da yake da komai dan har garden da swimming pool ne a shi.

Zama yayi dadi tsakanin ango da amarya sai dai sabin halaye. Da yadda ya same ta.

Ta maida Aslam kamar bawan ta dan sai abinda ttace shi yake mata.

In ta ce, kaza dole yayi shi. haka in ta aiki shi da gudun sa yake zuwa.

Duk da wani lokacin yana mamakin sa in ya kudurce a ransa bazai ba sai ya kasa.

Kamar ko da yaushe yau ma gefen karfe biyun dare ya zame jikin sa daga na Pretty.

Bandaki ya shiga yai wanka ya dauro alwala.

Sallah yazo ya dinga yi dan sai gab da asuba ya zauna yana karanta alkur'ani.

Ana kiran asuba kuma ya mike ya tafi massalaci.

Bai dawo ba sai karfe bakwai. Amman har lokacin Pretty ko mikewa batayi ba bare ta yi sallah.

Gidan dai yan aiki suna ta gyara shi. dan yan aikin da tazo dasu sunfi hudu kowa da aikin sa.

Daga mai gyara mata turaka sai mai gyara mata kitchen da girki.

Sai mai mata gyaran jiki da mai mata wanki under wears din ta.

Sai wani yaro dake mata sharar harabar gidan.

Ita ba abinda take sai dai a kawo mata taci ta koshi ta kwanta.

Dan ba abinda ttake yi. Daga zama sai kallo sai kuwa fita yawo.

Dan wani lokacin ta fice tin safe sai dare take dawowa.

Aslam kuwa da yake ba gwanin cin abincin masu aiki ba sai dai yaje gida ya ci.

Haka yake rana da dare. Duk ya rame ya zama wani iri da shi.

Ita Momy ma tausayi yake bata. Haka shi da baya son hayaniya dan gayu ya tsara yadda zai na jin dadi da matar sa.

Sai dai ya dawo ya tadda uwar lalaci a kwance yan aiki suna mata tausa.

Ko wani lokacin ya dawo ya tadda bata nan.

Bangaren Asma'u kuwa sai da tayi jinya sosai a makkah dan sai da Buhari da sir sabir suka je duba ta.

Sai da tayi sati biyu a asibiti sannan aka sallamo ta.

Ranan tana daki a kwance. Mami da Sir Sabir da Yaa Buhari suna falo suna hira.

Sir Sabir ne ya tambayi mene ya jawo wa Asma'u hawan jini haka.

Shiru Mami tayi kafin ta bashi labarin komai.

Sir Sabir sosai ya tausayawa Asma'u duk da yana mai godiya da Allah wata kila rabon sa ce shiyasa Allah yayi ba ai auren ta ba.

Daman ance, *Matar mutum kabarin sa* in Allah yayi rabon sa ce shikenan.

Sir sabir ya ce,
"Mami yanzu kina nufin Aslam yai aure?"

A kunne Asma'u kenan lokacin da ta fito daga daki.

Faduwar ta kawai suka ji. Da gudu sukayi wajen ta.

Nan da nan suka kara daukar ta sai asibiti.

Da kyar suka samo numfashin ta ya dawo dai dai.

Dr sai fada suke dan zuciyar ta da kamo da ciwo. Banda jinin ta da ya hau. Ya ce,
"Allah yasa ta tashi lafita dan ba karamin hawa jinin ta yayi ba."

Kuka Mami ta dinga Sir Sabir ne mai lallashin ta dan Yaa Buhari ma ya rasa me yake masa dadi.

Abinda baya so Asma'u taji kenan ya baro ta daga kano amman dai da taji.

Wata zuciyar kuma ta ce,
"Shikenan yanzu ai komai jjuj zo da sauko tinda ta san komai."

Sai da tai kwana uku a kwance kamar gawa. 
Dan likita yai mata allurar da zata sa ta sami hutu ko nutsuwar ta zata dawo.

Kwanata hudu sannan ta farfado shima da kuka.

Dan sai a lokacin ta samu damar kuka. Ba karamin tashi hankalin ta yayi ba.

Asma'u kuka take kamar ranta zai fita. Mami ce ke lallashin ta.
Chapter 34 · 0% Book details