← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 61

Sashe 58

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa yayi da sauri ya nufi kitchen ya dauko ya koma.
Sosai taci wainar dan sauran ma a firij ta saka.

Tun daga lokacin lafiya ta yiwa Asma'u wuya ga uban amai da takeyi komai taci sai ta amayar.

Lemo Kadai take iya sha shima a rana guda daya take yini tana sha.
Momy kam ba karamin tausayawa Asma'u take ba dan ta rame.

Da ta ce Asma'u ta koma gidan ta har kuka Aslam yai mata dole ta barta.

Amman kullum tana hanya zuwa duba ta.
Da Aslam yai wa Momy korafi akan aman da take yi.

Momy cewa, tayi,
"Ai wannan Aman na lokaci ne, lokaci daya zata daina sai a hankali."

Mami ma da taji Asma'u na da ciki tayi murna.
Haka Zainab da takanas tazo duba ta, tana ganin Dadyn ta ta farai masa wasa.

Sosai tai murna da zuwan Zainab komai ta dauko Zainab da Dadyn ta, ganin su ma sai yasa ta warke.

Dadyn ta kuwa kullim yana gun ta yaro ya dada wayo dan har an yaye shi ma.

Kwana biyu sukai ta koma. Asma'u na cewa ta bar mata Dady.
Zainab ta ce,
"Kiji da na cikin ki ma."

A lokacin ita kuma Nusaiba ta haifi dan ta Namiji aka saka masa sunan Dadyn Sabir Marzuk suke kuran sa da Fauwaz.

Itama Zainab tana da yaron ciki a lokacin.
Maimuna ma ta haifi yar ta mace aka saka mata ssuna Asma'u. Suke kiran ta little Husnah.

Asma'u ce kwance acikin kujera a falo shi kuma Aslam yana kitchen yana soya mata wainar fulawa, falon ya kawo mata ta tashi tafara ci sai data cinye tafara sheka amai shi kanshi Aslam sai data wankeshi da amai, rigar jikinta ya cire mata yafara gogge mata jikinta.

Ido ya zuba mata, kirjin ta ya kara cika, haka nan hip din ta sun bude. daukarta yayi yakaita toilet yayi mata wanka shima yayi yadaukota yakawota daki.

Magani ya bata ta sha sai bacci. Yana tausayawa Asma'u dan tana sha wahala sosai.

Ido ya zuba mata, ya ga ta rame sosai. A ransa ya ce,
"Wannan Babyn yana wahalar min da Honey bae ta."

Jikin ta ya shiga ya kwanta. Baccin ne shima ya dauke shi.

Sai da cikin Asma'u ya girma sannan ta samu sauki.

Tin daga lokacin kuma sai kwadayi ya bude.

Komai tasa a kawo mata. Momy kuwa yau ita ce kai mata kaza gobe kaza duk abinda tasan zata ji dadin sa.

********
Cikin Husnah ya girma haihuwa ko yau ko gobe.

Komai Aslam ne,  ke yimata hatta wanka da wanki shine yake yi mata.

Yau tin rana take jin ciwon ciki amman bata fadawa Aslam ba.

Har dare suka kwanta.  cikin dare ta tashi da ciwo.  Nan Aslam ya tashi ya duba yaga haihuwa ce.

Kasacewa tin da cikin ta ya shiga wata tara ya debo kayan da zasu bukata ko da irin haka ta faru haihuwar dare kenan.

cikin kankanin lokaci ta haifi jariranta tagwaye guda biyu duk maza nanfa Aslam yafara murna.

Shi ya gyara ta, yai mata wanka ya shirya yaran sa.
Gari yana wayewa ya fara shelar fadin haihuwar Asma'u

Ai kuwa yan uwa da abokan arziki suka yita xuwa ganin jariran.

Da Momy ta zo, take cewa Asma'u gida zata tafi ayau sai tayi 40 zata dawo, nan kuma Aslam  yace bai san zancen ba babu inda Asma'u zataje

Fada Momy ta rufe shi dashi ta shiga hadawa Asma'u kayanta.

Tana mitar yarinya aure shekara daya da wata hudu bata je gida ba sannan ta haihu ma baza ka bar ta taje ta huta ba.

Asma'u kanta bata son tafiya tabarshi amma, tana son taje gida a kula da ita.

Duk da tasan shima zai kula da ita amman kuma zata kara hutu bare ma yara biyu ai sai da taimako.

Momy da kanta ta kai Asma'u har Kano nan Mami ta  shiga murnar ganinta.

Aslam kuwa tunda ta tafi bai kirata ba dan fushi yake wai meyasa zata tafi bada izininsa ba, ko kanon ma yaki zuwa.

Sai dai duk abinda ake bukata ya turawa Momy shi dan Momy ta ce, sai anyi suna zata koma.

Ana gobe suna sai ga Aslam, da kaya niki niki. Dan set din alkwati ya ciko musu kowa da kayan sa.

tinda yaje ya dauki yaran ya kasa ajiye su.

Sosai yake jin kaunar yaran a cikin ransa yana mai godewa Allah da ya azurta shi da yara har biyu duk maza. Anan yai musu huduba da Suleiman, Sunan Dadyn Asma'u sai Muhammad sunan Dadyn sa.

Ranar suna anyi shagali sosai inda yara suka ci suna Suleiman da Muhammad.

Anyi shagali dan duk kawayen su Asma'u sun zo na makaranta.

Maryam ma taje a lokacin tana da yaron ciki. Anyi bikin ta da Naufal lokacin Asma'u ba lafiya wannan ya hana Asma'u zuwa sai sako da ta aika mata.

Sosai Asma'u tai murna da zuwan ta. Haka Nusaiba ta zo ita ma da kayan barka da Danta Fauwaz ya girma dan watan sa hudu.
Ana gama shagalin suna Aslam da Momy suka fara shirin tafiya.

Aslam kuwa ya san. Zai yi missing din Asma'u ace sai tayi arba'in.
Tana daki a kwance taci ado sai fitar da kamshin take, su yan biyu suna wajen Momy.

Dakin taji an turo, daga kai tayi ta kalle shi. Murmushi ta aika masa ya karaso cikin dakin.

kusa da ita ya zauna ya tsura mata ido tana sanye da jar atamfa mai ratsin baki ajiki tayi dan kwaliyya jikin ta ya murje, kirjinta ya cika sosai.

Janyo ta yayi jikin sa, can kuma ya daga ta, ahankali yadaga rigarta ya kwantar da kansa acikinta,

Wasa ta fara da gashin kansa. Ya ce,
"Husnah kice zaki bini dan Allah."

Murmushi tayi a ranta ta ce,
"Da yake gani uwar marasa kunya ba."

Mikewa yayi ya ce,
"Baki ce komai ba."

Ta ce,
"To me zance? In nace zan bika ai nayi rashin kubya ko?"

Kai ya girgiza ya ce,
"ba wani rashin kunya."

"Hmm!"
ta fada tana wasa da yatsun hannun sa.

"Wallahi zan shiga wani hali in bakya tare da ni. Ki taimaka kizo mu tafi kinji love."

Dariya ta dan yi ganin da gaske dai Yaa Aslam yake.
"Au dariya kike?"
baki ta danne da hannu ta girgiza kai.

"Shikenan Allah aure zan kara."
nan take taji gaban ta ya fadi.

Dagowa tayi ta kalle shi sai kuma ta dauke idon ta.
Mikewa yayi ya fice ya barta cikin fargaba da tsoro.

Washe gari da safe sai a falo ma tajiyo shi, mutumin da adakin ta suke karyawa.

Yana zaune yaran sa akan cinyar sa yana ta daukar su hoto.

Zama tayi a gefen sa ta dan rage murya ta ce,
"Ina kwana?"

Bai kalle ta ba duk da kamshin da take yana fizgar sa, amman ya maze ya cigaba da abinda yake.

Ayman ta dauka, wato usaini mai sunan Dadyn Aslam.

Sannan ta dauki, Aayan mai suna Dadyn ta.

Tana amsar su ya mike yayi dakin sa.
Shayar dasu tayi sannan ta mike ta shiga dakin Mami.

Suna zaune Mami da Momy. Sai da ta gaisar da su sannan ta mika musu Baby.

Momy ce ta mike ta ce,
"Bari na kira Aslam yazo mu tafi."

Ta fice can sai gasu sun shigo, Aslam ya canja shiga zuwa wata Ash kalar shadda.

Yayi kyau, kamar ka dauke shi. Sai tashin kamshi yake.

Akwatin ya dauka ya sauka sannan ya dawo Mami ce ta mike tabi bayan sa.

Momy ta kalli Asma'u ta ce,
"Asma'u zamu tafi munyi magana da Mamin ki mun yanke zaki wata uku saboda yaran su kara kwari kin haihuwar fari ce kina bukatar kulawa. Naso ki zauna a guna amman naga tinda kikai aure baki zo kinga Mamin ki ba. Amman wata haihuwar ni zan kula dake. Da kai na zan zo na dauke ki in lokacin yayi. Duk abinda kike bukata kina sanar dani "

Ta karasa maganar tana shafa kanta. Tace,
"Ki zauna mun tafi Allah kara lafiya."

Momy ta fita. Asma'u kuwa hawaye taji yana zubo mata Ta ce,
"shikenan sai yai auren da yace zai yi."

Mikewa tayi takarasa window tana kallon su, suna shiga mota.

Aranta tace,
"Lallai Yaa Aslam ko ya min sallama."

Waya ta dauka ta tura masa da text din Allah ya kaisu lafiya.

Ta koma ta kwanta akan gadon Mamin ta.

*BANYI ALKAWARIN ZAKU SAMU UPDATE NAN KUSA BA AMMAN YADDA NAJI JIKI NA ZAN KOKARTA DAN IN GAMA NIMA NA HUTU.*

NAGODE DA KULAWAR KU

*MS Indabawa*
[1/18, 14:44] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐

Dedicated to *My lovelly Mum*

*131-135*

Alhamdulilah jiki Alhamdulilah wallahi sai godiyar ubangiji. Nagode da addu'ar ku fans musammam yan group din Zama na Amana 2 da khaleesar haidar. Nagode Allah ya bar zumumci Ameen

 Wannan shafin nakune na duk mai suma Hauwa'u, Jidda, Yasmeen kuyi yadda kuke so dashi duk dan sbd da jin dadin Autar mu
Hauwa yasmeen

Tin daga ranar Aslam bai kara kiran ta ba dan yai fushi sosai duk da yana son yaji ta sai dauriya da yake sai dai ko ya bugi cikin Momy ko in suna waya yana musu labe.

Sosai Asma'u ta damu, amman kuma tana cikin jin dadi da kula da hutu.

Mami bata barin ta da kadaicin da zata zzauna tinani.
Ba abinda take a gida daga wanka sai bacci. Ko yaran sai zasu sha mama ake kawo mata su.

Gyara kuwa da wanka sosai Mami ke mata dan jkin ta har ya saba gashi Mami ta ce wata ukun nan sai an mata wanka dan haihuwar fari ce kuma ya'ya biyu dole a gyara ta in ba haka ba faba zata ji jiki.

Sai anan ta gane manufar da akace sun ka je gida. Dan ta godewa Momy da tace lallai lallai sai ta zo kano,
Tana shan gyara banda cima da Mami ta canja mata.

Sosai ake kula da ita. Kuma akai akai Zainab da Nusaiba da Maimuna suna zuwa duba ta.
Chapter 58 · 0% Book details