← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 61

Sashe 3

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna shiga mota, Aka kira ta. Dagawa tayi, da fara'a akan fuskar ta.

"Assalamu Alaikum!"
Ta fada dauke da murmushi.

"Wa'alaikum salam!"
Aka amsa mata daga can bangaren

"Ina kwana Yaya nah!"

"Lafiya lou. Kin fita dai ko."
"Gani a hanya."
ta amsa masa"Ina hoto nah?"
y

a tambaya.

"Bari na turo maka. Ina nawa?"
Ta fada tana lumshe ido.

"Naki yana can yana jiran ki."
ya bata amsa.

"Masha Allah ganawa nan zuwa."
Ta kashe wayar. whatsapp ta hau tayi masa sending pics din da ta dauka.

Nasa ta fara budewa, kallon wayar ta zubawa idanu.

Wani hoto ne ya bayyana, akan wayar ta.

Wani hadaden Balarabe ya bayyana, yana sanye cikin bakar suit, idon sa sanye da farin gilashi.

"Masha Allah! Yayanah kayi kyau."
Ta tura masa.

Amsa ya turo mata.
"Tabarakallah! Allah nagode maka da ka bani wannan kyakyawar yarinyar Allah ka mallaka min ita."

"Ameen Ya Allah Yaya na. Ka fita ne."
"Gani a hanya."

"To kaje ka duba mutane sai anjima."
Ta fada.

"Toh ki kular min da kanki kar ki bari kowa ya kalli fuskar ki."

"Hmm ka kular min da kanka nima."
Ta sauka a online. Titi ta kalla.
"Haba Yaya."

"Mene?"
Ya tambaya yana kallon ta. Fuska ta dan bata ta ce,
"Baka sauri fa."

Murmushi yayi ya ce,
"Karbi tukun."

"A'ah yi hakuri. Amman dan Allah ka dada sauri kaga har tara tayi."
ta fada tana marairaice masa fuska.

Sauri ya dada sukayi gaba, yana direta ta bude kofar da sauri.
"Nagode Yayana ka bada sako ga Besty nah."
Ta fada tana murmushi

Hararar ta yayi.
"Ban da wayar ta ne ko baki."

"Allah sarki Yayanah ji zanyi ko da gyaran da zan maka ne dan nasan na fika iya love."
ta fada tana kanne masa ido daya.

Kokarin bude kofa yake ya fito.
"Yi hakuri!"

Ta fada tana yin gaba da sauri.

Kofar ajin ta karasa. Wani kyakyawan saurayi ne a ciki baki ne amman yana da kyau ba kadan ba.

Sai kayi tsamanin irin black american nan ne.

Sanye yake da farar shadda kansa ba kula sai gashi da ya kwanta luf luf akan sa.

Lekawa take yi jifa jifa. Ganin sun hada ido yasa tai saurin dauke kan ta.

Fita yayi ya zuba mata ido. Kai ta dukar kasa. Kallon ta ya cigaba dayi.

"Wa kike nema."
Ya tambaye ta da turanci.

"Uhmm daman yanzu nazo ne."
ta bashi amsa tana in ina.

"Shine kuma me?"
Ya tambaye ya.

"Ba komai."
Ta fada jiki a sanyaye

"Karfe nawa kuke da lecture?"
Magana yake cikin turancin da ya kware a bakin sa.

"Sir karfe tara."
ta fada masa kan ta a kasa.

"What say's d time now (Karfe nawa yanzun)."
"Ban sani ba."

Kallon ta ya tsaya yi. Sannan ya duba agogon hannun sa. Karfe tara da rabi.

"9:30am yanzu ne lokacin zuwan ki."
"I am sorry Sir."

"Naji daga yau kika makara kar ki kara dosan kofar ajina kinji ko?"
Kai ta gyada masa.

Kanta a kasa taki yadda su hada ido dan wani kwarjini yayi mata.

"Shigo ciki."
Ya fada yana yin gaba

A gaban allo ya tsaya tayi hanya zata shige ciki.

"Come here (zo nan),"
Ya fada yana nuna mata wajen da zata zauna. A gaban sa.

Komawa tayi ta zauna, duk dagowar da zatayi idon sa na kanta. Kuma duk tambayar da zaiyi ita yake jefawa.

Sosai take bashi amsa dan *Asma'u* akwai kokari.

Sai karfe sha daya yabar ajin nasu. Tana zaune a inda take zaune sai ga Zainab ta karaso wajen ta.

" *Asma'u* amman fa kinyi sa'a har malamin nan ya bar ki kika shigo."

"Nima nayi mamaki dan kinsan haka yan wacan shekara suka sha fama dashi."

"Dan Allah kina dai kula."
zainab ta fada cikin damuwa dan bata son kawar tata ta rasa aji.

"Kar ki damu yau ma akasi aka samu ne."

Wani malamin ne ya shigo musu, yai musu lectures dan sai karfe daya ya fita.

Yana fita suka shige, masallaci. Sai karfe daya sukai sallah sannan sukayo cafeteria.

Lemo kawai ta karba, sannan ta tambayi Zainab me take so. Ta siya mata.

Suka samu wajen zama.
"Sis wannan gayen fa ya dame ni da maganar ki."

Murmushi *Asma'u* tayi,
"Wane gaye fa."

Hararar ta Zee tayi,
"Wai har kin manta."

Asma'u ta ce,
"Wallahi na manta."

Zee ta ce,
"Wannan Nasir din dan unguwar mu."

Murmuahi Asma'u tayi ta ce,
"Oh na tina. Ya akayi."

Dan hararar ta zee tayi ta ce,
"Wallahi ya dame ni ne."

Kallon Zainab Asma'u tayi ta dan saki murmushi ta ce,
"Ki bashi hakuri kinsan dai irin karatun da muke ciki ko?"

Zainab ta ce,
"Haka ne, amman ai karatu mun gama tinda asibiti zamu tafi, ya kamata ki maka ma miji da mun kammala sai mu shige gidan mu ko."

"Haka ne Zee amman nifa nayi karama da yawa!"
Hararar ta Zee tayi.

"Shekara sha tara din shine kike karama. Da da akewa yan shekara goma aure fa suce me."

"Haka ne, Sis ina tsoron aure ne, kuma dai bari kinji na fada miki. Nayiwa kai na miji kuma nasan shi zai fahimce ni ya kuma gatan tani."

Murmushi Zee tayi,
"Masha Allah wane wannan."

"Ya Aslam mana."
Asma'u ta bata amsa tana lumshe ido.

Dariya Zainab ttayi ta ce,
"Wane ma Ya Aslam."

"Ke Zee har kin manta shi. Dan gidan Yayar Mami nah fa. Ta Abujar nan."

"Oh nagane shi. Abinda har gida sun zo tare da Love dina."

Murmushi *Asma'u* tayi.
"Dan haka ki bashi hakuri. Nasan Nasir nada hankali da ilimi komai dai ya hada. Amman ki bashi hakuri."

"Ba komai zan san yadda zan sanar masa insha Allahu."
"Nagode."

"kar ki damu."
Wayar tace tayi kara,

Tana dubawa ta saki murmushi ta dauka.
"Assalamu Alaikum Baby "
aka dada daga can bangaren

"Wa'alaikum Salam."
Ta amsa masa murmushi dauke a fuskar ta.

"Kina lafiya dai ko?"
Ya tambaya.

"Lafiya kai fa?"
"Lafiya Alhamdulilah da fatan kinyi sallah kinci abinci."

"Yaya duk nayi biyu nake jira tayi mu shiga aji."
"Masha Allah abinda na kira naji kenan."

"Nagode da kulawar ka."
"Ba komai."

"To kai kaci abincin da sallah "
Na dai yi Sallah abinci kuma sai na gama aiki zan ci."

"Kai Yaya!"
ta fada a shagwabe
"Yi hakuri befi mutum uku ba kinji "

"Da gaske."
"Eh!"

"To dan Allah kana gamawa kaci."
"Insha Allahu!"

"Yauwah nagode."
"To sai ajima ko."

"Aha bye."
Ta katse wayar.

Zainab ce ta kalleta.
"Kece kuwa *Asma'u* "

"Me nayi?"
"Soyayya "

"Haba Aunty Zee ina wata soyayya anan. In ma soyayya ce ke kika koya min ai."

"Ni kuma?"
"Eh man yadda ko da yaushe kike yi a gabana."

Dariya tayi,
"Tashi mu tafi."

"Toh!"
Suka tafi hall din da zasuyi lectures.

Tinda suka shiga sai bayan hudu suka fito. Suna fitowa sallah sukayi su.

Lokacin har anzo daukar Zainab dan haka ta tafi ta bar *Asma'u* tana jiran azo daukar ta.

Ba tayi minti biyar da zama ba, aka zo daukar ta.

Tana mota Ya Aslam ya kira ta.
"Baby nah ya makaranta."
"Gani a hanyar komawa gida."

"Sannu kin gaji ko?"
"Wallahi, na gaji jikina sai ciwo yake min"

"Sannu kinji ai da ina kusa da nayi miki tausa ko."
Murmushi kawai tayi.

"Yaya nah kai fa ka tashi."
"Ina fa, aiki ma zan fita yanxu."

"To Allah bada nasara."
"Ameen! Sai anjima."

Ta kashe wayar. Idon ta ta lumshe, gaskiya tayi sa'a samun Yayan ta a matsayin me sonta, wanda tasan tin kafin ya fara son ta yake kula da ita da riritata bare yanzu kuma.

A rana sayi waya sau nawa banda text din safe na rana da na dare. Yayanta na son ta sosai da duk tafiyar da zaiyi tsarabar ta daban ce.

Haka nan Ga soyayyar Dadyn ta da itama take kara sa mata nutsuwa.

Tana shiga gida ta tadda Mami a kitchen dan haka kitchen ta shige ta fara taya ta aiki. Sai gab da magariba suka gama sannan ta mike ta hau sama.

Wanka tayi ta saka kaya mara sa nauyi. Turare ta feshe jikin ta sanna ta hau kan sallaya tayi sallah.

Tana idar wa ta dauko kur'ani ta fara bita sai da ta kai ixifi daya sanna taji kiran sallah isha'i mikewa tayi, tayi sannan ta fita zuwa falo.

pls don't forget to follow and vote @ msindabawa

Nagaishe ki ummu Ayda Allah bar mu tare Ameen

*INDABAWA*
[1/18, 13:56] Maryam S Indabawa🥰: *ASMA'U HUSNAH*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

Facebook @Indabawa novel
Wattpad @Msindabawa
Insta @Maryam S Indabawa

*HAJOW*

� *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* �

*16-20*

DEDICATED TO U *MOMMY NAH*

NO ONE LIKE U IN MY LIFE REALLY LOVES YOU *MY HAPPINESS*

*Manzon Allah (SAW) ya ce, "Kada dayan ku yayi tafiya da takalmi guda daya.
Ko ya saka duka. ko yacire baki daya"

Kamar kullum sai bayan isha'i na sauka. Da fara'a ta na karasa wajen Dady na.

'Barka da dawowa Dady ya aikin?"
Murmushi yake ta zubawa.

"Yauwah *Husnah tah* aiki lafiya Alhamdulillah! Ya makarantar."
"Makaranta lafiya Dady."

"Masha Allah!"
"Dady tashi muje kaci abinci kaxo ka huta."

"Toh yar gidan Dady."
Suka mike.

Wajen Mami ta karasa,
"Mami taso."

Itama mikewa tayi, sai tayi wajen Ya Buhari,
"Babban yaya taso"

Baki ya tabe ya mike. Gefen Dady ta koma ta kamo hannun sa ta hade dana Momy, suka nufi gun cin abinci.

Sai da ta zubawa kowa sannan ta koma gefen Dady,
"Yau tare zamu ci."

Suka fara cin abincin su.

Suna gamawa tayi kitchen dasu ta wanke sannan ta dawo falon.

Tausa takewa Dady a kafafun sa, yana tambayar ta harkar makaranta.

Karfe tara tayi dakin ta bayan ta gama tsokanar yayan ta tayiwa Dady da Mami sai da safe.

Tana shiga wanka tayi tayo alwala sannan ta murje jikin ta da mai, me kamshi tasaka kayan bacci a jikin ta.

Gado ta hau tana me janyo wayarta da ta ajiye.
Ido ta lumshe lokacin da tayi tozali da hoton Ya Aslam akan wayar ta.

Fita tayi daga galleryn ta duba screem din wayar sakon sa ne akai.
Chapter 3 · 0% Book details