Sashe 2
Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru sukayi ba wanda yace kala. Sun dauki wajen minti goma a haka, Sai numfashin su dake tashi kawai.
Ido ta lumshe, Tana me tunanin kyakyawar fuskar sa.
"Baby nah!"
Yayi maganar da wata irin murya. Dan numfashin ta dake tashi ji yake kamar a jikin sa dumin sa ke sauka.
Kiran sunan ta da yayi shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
"Na'am!"
Ta amsa da wata murya me rikita me sauraron ta.
"Baby na ina kika shiga, duk na rikice. Gashi number su Mami na kira duk sunki shiga."
Numfashi ta sauke,
"Ayyah Yayana Dan Allah kayi hakuri, ina wajen Dady nah ne."
Ajiyar zuciya ya sauke,
"Dady ya dawo kenan."
Itama ajiyar zuciyar ta sauke, tare da yin murmushi.
"Eh!"
"Ki gaishe shi."
Ido ta lumshe,
"Zai ji."
Murya ya kara yin kasa da ita,
"Baby na son ki zai haukatar dani fa."
Ido ta bude da sauri, tare da zaro su ta mike zaune.
"Ya Salam Yayana tayaya?"
Wata ajiyar zuciyar ya sauke dan duk lokacin da *Asma'u* na magana tana kashe masa jiki ne.
" *Husnah* son ki yayi mun kamu sosai. Baki ji yadda naji dana kira bakya nan ba. wallahi *Husnah* nasan bazan taba daina son ki ba."
Murmushi tayi, tare da sauke ajiyar zuciya.
"Shine kuma zai haukatar da kai."
Tayi maganar cikin shagwaba.
"Baki ji yadda naji a time din bane."
Kai ta girgiza tana murmushi.
"To am sorry Yayana Banyi dan na bata maka ba."
"Kar ki damu nasan da haka. Nasan yanzu kuma ana gun Dady mantawa nayi na neme ki."
Murmushi tayi. Ta lumshe idon ta, dan yana da saurin fahimta da bawa mutum uzuri.
"Nagode da fahimta ta da kayi."
"Nagode da son da kike min."
Sukayi murmushi a tare.
"To Baby kije kiyi
alwala kiyi addua ki kwanta."
"Toh!"
ta fada tana tashi daga zaune da take. A speaker ta saka wayar ta wuce ban daki.
Sai da tayi, addu'ar shiga sannan ta shiga.
Alwalar tayi, sannan ta dawo Dakin.
"Nayi Yayana."
"To maza yi Addu'a naji muryar ki."
"Toh!" Tace, ta bude tafukan hannayen ta ta fara karantowa.
Falaki da Nas da Kul huwallahu Ahad
Kafa uku uku sannan ta tofa a hannun ta ta shafe jikin ta dashi.
Sai ta karanto Ayatul Kursiyu, sannan ta daura da amana Rasuli,
*Bismika rabi wa da'atu. Janni wa bika arufa'uhu fa ina amusakutu nafsi daru jamha wa ina aru salutaha fa hufazuha bima tahufazu bihi ibadakal salihina*
*Allahumma fina axabaka yauma tabu'asu ibadaka ×3*
*Bismikallahumma Amutu wa ahaya.*
*Subhanallah ×33*
*walhamdililah ×33*
*wallahu akbar ×34*
*Allahuma Fadiri samaqati qal'ard raba kulli sha'in wa malikatu. Ashadu al la'illa anta a'uzu bika min sharri nafsi wa min sharri shaidanu wa shirukihi. Wa an aftalihu ala nafsi au adillahu illa muslim*
"Shafe jikin ki ki kwanta da dama."
Yin yadda ya umarce ta yayi sannan ya karanto mata shima.
"Rufe idon ki."
Rufewa tayi,
"to kiyi bacci me dadi tare dani."
Murmushi tayi tana gyara kwanciyar ta.
Kissoshi ya dinga karanto mata. Tin tana ji har bacci ya dauke ta.
Sai da ya tabbatar tayi bacci sannan ya kashe wayar sa.
Alwala yayi yai addu'a ya kwanta da tunanin Babyn sa a ransa.
Karfe sha daya Mami ta leko dakin nata, bacci ta same ta tana yi.
A gefen ta ta zauna, kanta take shafawa ta zuba mata ido. Ido ta lumshe sannan ta bude.
Addu'a ta kara tofa mata ta ja mata bargo ta fita tare da rufe mata kofa.
Karfe biyar da kwata, ta mike, ban daki ta shiga tayo alwala.
Tana fitowa, taji karar wayar ta.
Murmushi tayi da taga me kiran nata.
"Asssalamu Alaikum!"
"Wa'alaikum salam My Ra'isul khalbi."
"Kin tashi kenan."
"Eh na tashi."
"Masha Allah kije kiyi ibada kiyi mana addu'a."
"Insha Allah!"
Kan sallaya ta zauna sallah tayi raka'a biyu sannan ta dauko alkur'ani.
A dai dai lokacin Mami ta shigo dakin nata.
Akan sallaya ta ganta tana rairo karatun al kur'ani.
Ganin tana karatun yasa ta juya ta fita.
Jin za'a fara kiran sa yasa ta mike tayi raka'atanil fijir.
Tana idar wa ta mike tayo sallah. Ta jima tana addu'ar sannan tajawo kur'anin ta ta cigaba da karanta wa.
Sai da takai izifi biyu sannan ta mike ta dauko littafin makarantar boko tayi bitar karatun ta.
Tana son karatun bayan magariba dana asuba dan in ta karanta ji take, kamar an bude kan ta an zuba mata dan sauki da yadda take fahimtar sa.
Sai shida da rabi ta sauka kasa. Ko ina tsab sai tashin kamshi yake yi.
Murmushi tayi, Mamin ta akwai tsafta da son kamshi.
Kitchen ta shiga, Mami ta gani tana gyara nama.
Murmushi tayi, ta karasa. Durkusawa tayi sannan tace,
"Mami ina kwana?."
Juyowa Mami tayi, ta kalle ta tare da yin fara'a
"Kin tashi lafiya?"
"Lafiya lou."
"Kawo na taya ki."
"A'ah jeki wajen Jamila, ki amso dankalin dana bata ta feraye."
"Toh" ta amsa,
Fita tayi wajen masu aikin gidan ta karbo ta dawo.
kara wanke shi tayi sannan ta soya shi sama sama. Ta tsame shi ta kada kwai ta zuba kayan hadi ta dinga dibar soyayen dankalin tana zubawa cikin kwan tana soyawa.
Tana gamawa ta hadawa Dadyn ta kunun gyada da yaji madara yai fari tas da shi.
Tana gamawa ta gyare kitchen din sannan ta wuce sama.
Dakin ta kara gyara wa ta saka room freshner da turare da dadi sanyin AC dakin nata.
Kayyan jikin ta ta cire, ta shige ban daki danyin wanka. Sai da ta fara wanke bandakin ta sannan shima ta bade shin da kamshi. Sannan tayo wankan.
Tana fitowa ta tsane jikin ta, mai ta shafa, sannan ta hade jikin ta da kamshi. Body spary ta dauko na Alharaman da na man sa ta shafe jikin ta dasu.
Hoda kawai ta shafa sai kwalli da ta saka ya kara fito mata da manyan idanun ta. Sai man lebe da ta saka shima, ya amshi leben ta.
shirya wa tayi, cikin wata, bakar doguwar riga da akai mata ado da ruwan hoda.
Ruwan hodar mayafi da takalmi ta dauko, sai bakar jakar ta.
Dakin Dady tayi,
"Dady ina kwana,"
Ta fada tana karasawa wajen sa.
"Lafiya lou *Husnah tah* "
Tea da yake hadawa ta karba ta karasa hada masa.
Fulas ta bude ta zuba masa soyayen dankalin da tayi sai, farfesun duk ta hada masa.
Dankali ta dauka guda daya taci.
"Dady na tafi."
"Ina zaki?"
"Makaranta."
"Kin karya ne?"
"In naje naci a makaranta."
Fuska ya bata. Dawo wa tayi,
"Menene Dady?"
"Zauna kici kinji ko?"
"Toh,"
Ta fada tana daukar kofi zata hada tea.
"Karbi wannan."
Murmushi tayi,
"A'ah! Dady gashi ma zan hada."
"Toh!"
Tana gama hadawa ta saka hannu suna karyawa. Kadan taci ta zare hannun ta.
"Dady na koshi."
"Haba *Husnah* wai meyasa bakya son cin abinci ne."
Murmushi tayi
"Dady duk abincin da naci."
"Kina cin abinci kinji yar gidan Dady."
"Insha Allah Dady nah."
Mami ce ta fito daga daki.
"Iyye wai meyasa kike son kina deben ladan nawa, kici nawa kije kici naki."
Murmushi *Asma'u* tayi,
"Mami duk abinda nayi na bar miki ladan."
"Toh kinji dai."
Dady ya fada.
"Naji amman tana bari na ina yin aikina."
"Da kika samu me son yin aikin ma."
"Rabu da ita dai Dady, haka take cewa in nayi aure bata san ya zatayi ba duk ta sangar ce fa."
" 'Ka niyar ki. Yaushe na ke fadan haka."
"Haba Mami kin manta ne."
"Ina ji dai!"
Ta fita. Tana dariya,
"Dady bari naje kar na makara."
"To *Husnah* a dawo lafiya."
"Allah yasa,"
"Karbi wannan."
Juyowa tayi,
"Dady ka barshi da kudi a hannuna."
"Haba *Husnah* ki karba, kika san wanda zai nemi taimakon ki kuma kika san abinda zai taso miki na kudi."
"Toh Dady nagode Allah kara budi ya jikan mahaifa."
"Ameen! Ameen! *Husnah* "
"Na tafi Dady nah."
"Allah kiyaye hanya. Ayi karatu da kyau."
"Insha Allah."
Dakin ta ta wuce, ta dauki jakar ta. ta dauki waya tayi. ta dauki hoton kanta.
Dakin yayan ta, ta wuce.
Yana kwance akan gado ya rufa da bargo. Murmushi tayi ta karasa kan gadon nasa.
Yaye masa rufar tayi,
"Yaya nah!"
Ta kwala masa kira a kunnen sa. A gigice ya mike. Kallon ta ya tsaya yi.
Baya taja. Tana murmushi.
"Ina kwana Yayana."
Hararar ta yayi,
"Allah *Husnah* ki shiga hankalin ki, ina bacci kizo ki tashe ni."
"Yi hakuri Yayanah, makaranta fa zan tafi shiysa naxo na gaishe ka."
"Wai ke tin yaushe na fada miki bana son kina tadani ina bacci."
Wayar tace tayi kara, tana dubawa taga Zainab ce.
Murmushi tayi ta dauka.
"Besty ya aka yine."
"Kin tsaya tsokanar taki ko? Bayan kinsa Yau Sir Sabir ne damu kuma kinsan baya bari a shiga in an makara, ki kalli agogo karfe tara saura minti goma fa."
Ido ta zaro,
"Wayyo Sis gani nan."
Ta fice a dakin da sauri. Mami taje taiwa sallama sannan ta dawo dakin Ya Buhari.
"Ya please! Kazo ka kaini wallahi Baba baya sauri."
"Naki."
"Dan Allah!"
Ta fara masa magiya. Har da su zubewa a kasa.
"Tashi muje."
yai gaba tabi shi a baya.
*pls don't forget to vote*
Tnc
*INDABAWA*
[1/18, 13:55] Maryam S Indabawa🥰: *ASMA'U HUSNAH*
BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*
🌐HAJOW📝🌐
👩👧👧👩👧👧👩👧👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾
*11-15*
DEDICATED TO MY WHOLE NUMBER *MOMMY*
ALLAH YA FARANTA MIKI YA KARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA YASA KI GAMA LAFIYA.
ALLAH JIKAN IYAYEN KI
*AMEEN*
*Manzon Allah (SAW) Yace, "Indan dayan ku zai ci abinci. Yaci da dama.
Idan dayan ku zai sha ruwa yasha da daman sa."*
*Wallahi a littafin nan nasha fama dan na rubutashi tsab duk ya goge. Sai da na kara wani abun duk ba kamar wancan ba. Sai dai nayi kokari ganin na tuno amman wani dole na manta shi.*
Ina gaishe ki Anty Rash da fatan alheri. Allah ubangiji ya dafa miki Ameen. Amman muna jiran cigaban *Yafi dare dugu* a taimaka mana*
Dole na yabe ki AMRAH A MASHI PrincessAmrah. Gaskiya littafin nan Amrah nake so yayi kina kokari Allah ubangiji ya dafa Allah yasa a gama lafiya
*Ameen.*