Sashe 23
Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dady ya ce,
"Kafin nan ina son na tambaye ki shin *Husnah* kina da wanda kike so ne?"
Faduwar gaban ta ce ta tsanan ta, wani gumi ya karyo mata. A gaskiya tana jin kunyar Dady dan ji take baza ta iya ce masa akwai wanda take so ba.
Shiru tayi Dady ya kuma tambayar ta tayi shiru sai da ya tambaye ta sau uku bata bashi amsa ba sanna ya ce,
"Wannan ya nuna min baki da wanda kike so kenan."
Da sauri ta dago kai ta kalli Dady sai kuma ta kalli Yaa Aslam da ya zuba mata ido.
Kasa tayi da kanta. Murmushi Dady yayi ya ce,
"To Alhamdulilah! Akwai wani alkawari da na dauka tin kina shekara shida. Ba wani alkawari bane sai na bawa Aslam auren ki,"
Da sauri Asma'u ta dago tana kallon Ya Aslam.
Murmushi ya sakar mata ya kanne mata ido daya. Dady ya ce
"Aslam shi ya hana a fada miki ya ce, sai ya nemi soyayar ki gashi kuma ba tambaye ki ba Wanda kike so kinyi shiru."
Fuska Amsa'u ta rufe da tafin hannu. Dady ya kalli Aslam ya ce,
'To kai har yanzu baka nemo soyayyar taka ba dan haka ka sake zage dantse."
Dariya dakin sukai gaba daya. Dady ne ya kara yin gyaran murya ya ce,
"To yanzu Aslam yazo akan batun auren ku. Ya ce, so yake da kinga gama karatu ayi komai a gama, dan haka na kira ki na shaida miki an bada ke ga Dan uwan ki Aslam."
Kai tayi kasa dashi tana jin wani sanyi kamar zai me murnar ta taki ta rufu. Kamar yadda Aslam ma bakin sa ya kasa rufuwa.
Dady ya ce
"dan haka muna addu'a Allah ya tabbatar da alherin sa a cikin wannan al amarin."
Dakin gaba daya suka amsa da
"Ameen!"
Dady ya ce,
"Yau nafi kowa farin ciki da na sauke wannan nauyin a kai na da kaina. Allah yasa Asma'u ta zama matar ka ta sunna."
Suka kara amsawa da
"Ameen!"
Dady ya ce,
"Zan fi kowa farin ciki ko a yau na mutu nasan *Husnah* ba zatai maraici mai yawa ba dan na tabbata Aslam da Buhari zasu kula dake iya kar iya yawar su. Ina fatan *Husnah* ki zama mace ta gari ga mijin ki. Aslam yana son ki so tsakani da Allah nasan duk wanda zai zo ya so ki bai zai kai kamar yadda Aslam ke son ki ba. To Alhamdulilah kema kina son nasa naji dadi. Allah yai muku albarma."
"Ameen!"
duk suka amsa
Dady ya ce,
"Shikenan kuje daman kiran kenan."
Asma'u ce ta mike ta fice duk kunya ta kamata.
Dariya Dady yayi ya ce,
" *Husnah* kenan."
Mikewa Aslam yayi shima yayi dakin sa. Waya ya bugawa Dadyn sa yana cewa ya shirya, auren sa ya kusa fa.
Dariya yabawa Dadyn sa Dadyn sa ya ce
"Allah tabbatar da alheri,"
"Ameen!"
Ya amsa
Tin lokacin Asma'u ta kasa fitowa falo sai bayan la'asar da taji gidan shiru shine ta mike ta shiga wanka.
Fitowa tayi ta shirya cikin bakin dogon siket sai wata riga mai dogon hannu Ash kala wacce akai mata ado da bakaken stone. Hula kawai ta saka ta fita daga dakin.
Mami ta gani zaune a falo. gefen ta ta zauna ta ce,
"Mami sannu da gida"
"Yauwah!"
Mami ta amsa. ta mike ta fice.
Garden ta nufa ta zauna a inda suka saba zama ita da Yaa Aslam.
Ido ta lumshe kamar me bacci ta tafi can duniyar tunani.
Aslam kuwa tin da ya dawo daga massalaci ya nufi garden din shima.
Da farko zama yayi sai da yaga ba kowa sannan ya mike yana zagaye garden din. Iska mai dadi tare lumlume na ratsa sa.
Yanzu haka gajiya yayi, ya juyo ya dawo dan ya zauna.
Kamar a mafarki ya hangonta kwance ta lumshe idon ta.
Wani dadi yaji ya lulube shi. A hankali ya karaso inda take.
Zama yayi a kujerar dake gefen ta sannan ya hura mata iska a kunnen ta.
Ido ta bude da sauri Yaa Aslam ta gani zaune a gefen ta sai murmushi yake sakar mata.
Mikewa tayi zaune ta kasa dauke idon ta daga kallon sa.
Murmushi yayi ya hure mata idanun ta da iskar bakin sa.
Murmushi tayi ta dauke kanta daga kallon sa cikin jin kunyar sa.
Ya ce,
"Baby ya kamata muje naga asibitin ki,"
"To muje."
Ta fada tana mikewa.
Kamo hannu ta yayi ya ce,
"Ina kuma zaki?"
"Mami zan fadawa."
Sakar ta yayi ya ce,
"Ina jiran ki a mota."
Cikin gida ta shiga ta dauki after dress sannanta sanar da Mami inda zasu.
Adawo lafiya Mami tai musu suka fita.
A hanya ba wanda yace da dan uwan sa kala.
Ita Asma'u sai yanzu take jin kunyar Yaa Aslam dan yanzun ta tabbatar da gaske dai shi zata aura.
Shi kuma ya rasa me ya hanashi jan ta da hira sai da lokaci kadan kadan ya kalle ta ko ya kamo hannun ta ya murza.
Da haka har suka karasa asibitin. Katon Asibiti wanda Dady yasa akai mata ginin zamani mai kyau.
Komai na cikin asibiti mai kyau da tsada ne.
Har office din ta sai da suka shiga.
Ya Aslam sai yaba wajen yake. Duk da nashi asibitin yafi nata girma amman tsarin nata ya burge shi sosai.
Sai da suka gama kalla ya ce,
"Baby na kince dai in munyi aure yau muna kano gobe muna Abuja ko?"
Kallon sa tayi dan bata gane maganar tasa ba. Ya ce,
"Eh man ai dole muna zuwa duba asibitin mu ko?"
Murmushi tayi ta daga masa kai,
Gida suka koma ana kiran sallah magariba.
Asma'u ce kawai ta shiga ciki shi kuma ya tafi massalaci.
*Muje zuwa*
*INDABAWA*
[1/18, 14:20] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*
Dedicated to *My Lovelly Momy*
*121-125*
An Ruwaito Daga *Abdullahi bn Mas'ud (ra)* Ya Kasance Idan Ya Samu Labarin Fitowar Rana Yana Cewa:_
*{ﺍﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟِﻠَّﻪِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻭَﻫَﺐَ ﻟَﻨَﺎ ﻫَﺬَﺍ ﺍﻟْﻴَﻮْﻡَ ، ﻭَﺃَﻗَﺎﻟَﻨﺎ ﻓِﻴﻪِ ﻋَﺜَﺮَﺍﺗِﻨَﺎ}*
_*"Alhamdulillahil Lazi Wahaba Lanã Hazal Yauma Wa Aqãlanã Min Atharãtinã²".*_
Yana dawo daga massalaci ya kira ta awaya kan ta same shi a garden.
Mikewa tayi ta fita ta kofar kitchen ta shiga yana zaune akan kujera ta karasa gun sa.
Zama tayi ba tare da ta ce kala ba.
Kallon ta yayi yai murmushi ya ce,
"Baby na ya kika ji batun Dady dazu."
Murmushi tayi ta ce,
"Me Dadyn ya ce?"
Murmushi yayi ya ce,
"Wallahi baza ki kunna ni ba. Kinji komai da ya fada yanzu kin kara tabbatar da irin son da nake miki."
Kai ta gyada ta ce,
"Daman can na yadda da son da kake min."
Murmushi yayi ya ce,
"Alhamdulilah nagodewa Allah Zuciya ta ke kadai takewa na amince ki rike ta har abada."
"Ya Aslam kenan!"
ta fada.
Yace,
"Eh! Man kada ki taba zaton zan yaudare ki"
Tace,
"Nasan baza ka taba bama."
Yace,
"Yauwah Love."
Sukai murmushi a tare, Asma'u ta ce,
"Nima Zuciya ta kai kadai take yabawa dan tasan ka riketa ba da yaudara ba."
"Da gaske."
"Eh!" Ta fada tana dage masa gira.
ya ce,
"So hadi na Allah ne Asma'u, Zuciyata ke kadai ta nuna min. Na riga na sanarwa da Momy da Dady da Dady da Mami, da duk wanda muke mu'amala dasu in babu ke sai dai na rasa rayuwa ta."
Ido ta zaro,
"Su Momy,"
Yace,
"Eh! Mana ai kowa yasan son da nake miki in aka raba mu zan iya rasa rayuwa ta."
Murmushi tayi ta ce,
"Allah ma ya kiyaye."
Ya ce,
"Ameen!"
Tace,
"Tin da Dady ya bayyana, min son ka akan kai ne, mijina baka ji yadda naji ba. Saboda Allah yasa ga wanda nake so aka hada kaga yafi dadi ko."
Ya ce,
"Shiyasa nacewa Dady kar a fada miki sai na kama bakin zaren!"
Murmushi tayi, ta ce,
"Wane zaren kuma"
Ido ya kashe mata.
"Zuciyar ki man. Hmmm *Husnah* baki san yadda na riki soyayyar ki a raina ba. Ta zama abin yi dare da rana. Soyayyar daraja ne da ita. Samun irin taki shine burin ko wane me hankali. Bana son na taba yin nesa dake. Kin shiga zuciya kinyo kafuwa. Ni dake babu rabuwa koman dadewa."
Kallon sa ta tsaya yi.
"Kai ma kasan kaine zabin rai na. Zuciya ta, ta adana soyayyar ka ba wanda ze maye gurbin ta. Sa'a ni na sama tinda na samu gwarzon masoyi kamar ka. Kai ka ke sani addu'ar neman miji na gari, kuma nasan Allah ya amsa min da ya aikon da kai a matsayin masoyi wanda nake fatan shine miji na."
"Gaskiya ne. Dace da masoyi shine ribar soyayya. Nasan sabon da mukayi ni dake sai dai a kira mu tagwaye, ko yaushe in na tina ki nakanyi murmushi da jin farin ciki a cikin zuciya ta."
Murmushi tayi, ta sauke ajiyar zuciya me karfin.
Ya ce,
"Lafiya?"
Ta ce,
"Ya Aslam in na tuna da rabuwa ne sai naji zuciya ta tayi min rauni"
Kallon ta yayi ya ce,
"Haba *Husnah ba mun kashe wannan maganar ba ne."
Kai ta gyada masa ta ce,
"Eh!"
Ya danyi murmushi shima. Ya ce,
"To Bazamu rabu ba sai dai mutuwa itama insha Allahu tare zata dauke mu."
Kai ta langwabar tace,
"Allah yasa!"
Ya amsa da
"Ameen."
Dan shiri sukai sai kuma yace,
"Yauwah kinga tin yanzu sai mu fara tsara yadda bikin mu zai kasance ko?"
Murmushi Asma'u tayi tace,
"Kai Yaa Aslam tin yanzuu."
Yace,
"Eh man. please My love, let's talk about ourselves, our future My dear, sbd managers sun ce, he who failed to plan he plan to fail."
Kallon ta ya yi sannan ya cigaba da cewa,
'My love, ni yanxu bani da wata agenda da ta wuce naga mun gina rayuwa me kyau ni da ke my dear.
My yanxu misali nan da yaushe ya kamata ace mun fara shirin auren my?"
Asma'u ta dan ja numfashi ta ce,
"Ni ban sani ba."