← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 61

Sashe 15

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba ya ce,
"Asma'u kinsan ance karfen nasara bai da tabbas motar nan lafiya muku fito amman kinga ta tsaya taki tashi."

Fitowa tayi ta duba agogo tara saura minti biyar.

Waya Baba ya dauka ya kira mai gyara motocin gida ya fada masa inda yake

Kallon sa Asma'u tayi ta ce,
"Baba bari na hau napep dan na makara gashi zanyi submitting aasignment "

"To bari na tsayar miki da Napep din.'

"Aah Baba na gode."
Ta fada tana dan matsawa.

Mamaki take ganin karfe tara amman ji yan makaranta sai zirga zirga suke bama maza yan makarantun gwamnati.

Duk Napep din da zai zo a cike yake zuwa.

Wata Mota ce ta tsaya a gaban ta. Matsawa Asma'u tayi.

Kara binta akai ta kuma matsawa. Fitowa yayi daga cikin motar.

Wani hadaden saurayi ne ya fito. Fari ne, yana sanye da Ash kalar shadda kafar sa da bakin takalmi haka hannun sa daure da bakin agogo.

Kansa bbabu hula sai gashi dake kwace luf luf. Yana da idanu, haka nan hancin sa dogone har baki.

Karasawa yayi gun ta cikin nutsuwa ya ce,
"Assalamu Alaikum."

"Wa'aikulum salam!"
Ta fada tana dan matsawa daga wajen.

Kara bin ta yayi ya ce,
"En mata ina zaki?"

Ko kallon sa batai ba ta fara tsaida wani Napep.

Bai tsaya ba sakomakon cikar da yake.

"Naga kamar makaranta zaki kizo na rage miki hanya."
Dagowa tayi ta watsa masa wani irin kallon sannan ta matsa wajen wani napep da ta tsayar.

Kallon ta yayi har ta shige ciki sannan yayi murmushi ya shiga motar sa ya tafi.

Tana zuwa ta tadda har an yi submitting ga wani malamin yana musu lacturrle.

Kuka ta saka. tana zaune har lecturer ya fito.

Ta shiga ajin ta kifa kanta a benci tana cigaba da kuka.

Zainab ta matso gun ta tana bata hakuri sai ga. sir Sabir nan.

A haka ya shigo har ya gama lecture Asma'u bata dago ba.

Sai da zai fita ya dan matso gefen ta ya ce yana son ganin ta. Sannan ya tafi.

Asma'u duk ta tsure dan tasan akan bai ga assignment din ta ba.

"Zainab Allah bazani ba ni nagaji da kullum complain wallahi."
"Kiyi hakuri kije baki san me zai faru ba."

Da haka Zainab ta lallabata ta tafi office din nashi.

Da sallama ta shiga bayan tai knocking an bata izinin shiga.

Kai daga kallon ta ma zaka san ta sha kuka dan idon ta yayi ja dashi.

Sir Sabir ne zaune a wata kujera sanye da Wata brown shadda. Gefen sa gayen da ta gani dazu a hanya ne yaso ya rage mata hanya.

Waya taji Sir sabir yana yi yana cewa,
"Ki nifa ban san ta ba a ranar nima na taba ganin ta."

Shiru yayi sanna ya ce,
"Sai kinzo. In kuma na fita ne shikenan."
Ya kashe wayar.

Kallon sa ya maida kanta ya ce,
"Mene?"

Kallon sa ta tsaya yi ta ce,
"Uhmm uhmm!"

Sai ku a tayi shiru. Fauwaz dake, gefen sa ya dago dan ganin da wa yake.

Ido ya zaro ya ce
"Kai kece?"

Kallon sa tayi ta dauke kai ta ce,
"Sir kace nazo."

"Me yasa banga assignment dinki ba."
Shiru tayi.

Sai da ya kara nanata tambayar sannan ta dago ta kalle shi

Fauwaz ne ya dago ya ce,
"Friend ita ce wacce nake baka labarin na hadu da ita fa dazu. Motar suce ta lalace,"

Hararar sa Sabir yayi ya kalle ta ya ce,
"Ke me yasa kullum kina da matsala ne, in tayi baki makara ba yau abu kaza ya faru me yasa ne *Husnah* "

Fauwaz ya ce,
"Haba aboki kayi hakuri man."

Ya kalli Asma'u ya ce,
"Beauty mene matsalar ki yanzu?"

Banza tai masa tai kasa da kai idon ta na cikowa da kwalla dan ita da kai mata fada gara ka dake ta. Bata son fada a rayuwar ta yanzu zata fara kuka.

Kallon ta Sabir yayi ya ce,
"Mikon Assignment din naki kuma ki kara samun matsala na rashin submtting ko makara ki gani."

Da sauri ta dauko ta mika masa. Ta ce,
"Nagode!"

Tayi hanyar fita da sauri Fauwaz ya mike zai bita Sabir yai saurin riko hannun sa.

kafin ta bude kofa aka bude. Maryam ce ta shigo cikin shigar ta mai kyau ta saka doguwar rigar atamfa a mata dinkin mai dogon hannu.

Mayafin ta dan yafa kai ba dan kwalli sai jaka dake kafadar ta.

Tana ganin Asma'u ta saka dariya ta ce
"lah Asma'u!"

Sai kuma ta kama hannun ta. Ta kalli Sabir ta ce,
"Uncle kace, baka santa ba a ranar ka taba ganin ta."

Sai a lokacin Amsa'u ta tuno da statement din sa da ta shigo taji yana waya.

Kamo hannun ta tayi suka shigo office din ta ce,
"Ke nazo nema muyi sallama gobe zan koma garin mu gashi ban da number ki."

Murmushi Amsa'u tayi wanda Fauwaz ya kasa dauke ido daga kallon ta.

Hannun Maryam ta kama suka fita kallo Fauwaz da Sabir suka bisu da shi.

Wajen Zainab suka karasa ta zauna sannan sukai musayar number sai hira ta balle.

Dan har lecture tare suka shiga suka fito sukaje sallah sannan suka je cafteria suka ci abinci.

Sai karfe biyar sannan suka rabu shima dan an tashi.

Har bakin office din Sabir suka rakata suna daga mata hannu sannan suka juya.

Sabir da ya zata ma ta tafi ta shiga ta zauna akan kujera ta ce,
"Wash! Wallahi Uncle na gaji haka nima zan sha fama in na fara karatu."

Kallon ta yayi ya ce
"Daman baki tafi ba."

Kai ta daga masa ta kalli Fauwaz ta ce,
"Uncle Fauwaz ya kake?"

"Ni ba ruwana da ke. Kin tafi kin barni."
dariya tayi ta ce,
"Ayi hakuri wallahi Uncle Fauwaz. Asma'u ce ta burge ni na dawo amsar number ta kasan gobe zamu shige."

Kai ya daga ya ce,
"Dan bani number na gani."

"Tab ta ce, kar na bawa kowa wallahi."
Sai lokacin Sabir ya ce,
"In ba kwana zamuyi ba mu tashi mu tafi dare na yi biyar da rabi fa."

Mikewa yayi ya dauki jakar sa da basket ya mikawa Maryam Amsa tayi suka fito tana ta basu labarin Amsa'u in ka kalli Sabir zaka zaci ba jin ta yake ba amman gaba daya hankalin sa na ga ita yana jin abubuwan da take fada.

Da haka suka je gida haka tai ta bawa Mamah labarin Asma'u ranar dai har dare bata da magana sai Asma'u daga ta ce, tayi kaza sai ta ce tayi kaza.

Ta ce,
"Mamah baki ga ba yarinya karama ta na karanta medicine kuma a final year wallahi ta burge ni ga kokari da muka shiga lecture ita ke bada asma."

Mamah ta ce,
"Sai ki koyi da ita to."

"Ai insha Allahu Mamah kuma nayi 'kawa."
Shi dai yana zaune yana ji yana kara jin Asma'u na kara burge shi.

Asma'u ma da taje gida sai da ta bawa Mami labarin yarinyar.

Mami ta ce,
"Daman haka rayuwa take wani na son ka wani kuma kin ka yake yanzu dai ita kince daga haduwa Allah ya sa mata son ki. To Allah ya bar mu ga masoyan mu."

"Ameen!"
Ta mike ta hau sama.

Yaya Aslam ne ya kira ta bayan sun gaisa yake tambayar ta makaranta ita ma take tambayar sa wajen aiki.

Soyayyar Asma'u da Aslam abin sha'awa ce da burge wa dan ba karamin son juna su suke ba kowa da son dan uwan sa son da basa son su taba rabuwa da junan su.

Kowa na kula da tarairayar juna. Ga shi soyayyar su mai tsabta da kyau suke.

*Haka rayuwa yake wani daya ganka yake jin son ka a zuciyar sa. Son Allah kenan wanda wani dabi'un ka su suka burge shi. Wani kuma halayar ka abubuwa da yawa dai. Allah ka bar mu da masoyan mu,*

*Ameen!*

Mutane na tambayata wai *Sabir* Mijina ne ko saurayi nane to daga *Sabir* har *Aslam* da *Fauwaz* all are my lovelly children. Really love then.

*Husnah* kuma ina son sunan ne.

*Masoya na nagode nagode Allah bar soyayya.*

*Muje zuwa ga wani ya dadu a masoyan Asma'u shin ya kenan*

*Ina mai bada hakuri na jina shiru da kukai jiya da night da na morning da ban ba. Nagode*

*INDABAWA*
[1/18, 14:15] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*

By *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*

Dedicated to *My whole Number. My Momy!*

*Allah kara girma da daukaka. Allah yasa ki gama da duniya lafiya. Ur love is special.*

*81-85*

*_An Tambayi *, *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa: *"Kuyi Aiki Domin Kowwa Ana Saukake shi ya Zuwa Abinda Aka Halicceshi Donshi ne"* (Bukhari da Muslim)._*

Pretty ce zaune a gaban wani boka. Kai sufar bokan ma kanta abar kyama ce da tsoro bare kuma warin da yake yi.

Abinda take bukata ta gama fada masa.
buga kasa yayi yai dube duben sa sannan ya ce,
"Kin kawo aiki me wahala dan mutanen nan ba a zaune suke ba wajen ibada sai dai zan san yadda zamu yi muga ta wacce hanya zamu bi."

"Yauwah ni na fi so ma ita yarinyar a haukata ta yadda dole zai hakura da ita ko ta mutu ma."

"Kull!"
Yai mata wata tsawa ya ce,

"Wannan yarinyar har tafi Aslam tsari da riko da addini baza mu iya da ita ba. Tafi karfin mu."

Da haka ta zube masa kudi masu waya sannan sukai akan nan da wata daya ta dawo.

Daga nan ma Pretty ba gida tayi ba wajen wani bokan ta karayi suka karai mata alkawarin komai zai wakana yadda take so.

Da haka ta koma gida da murna abinda take so zai zo gare ta.

Dan har ta fara shirye shiryen auren ta da Aslam.

Aslam kuwa bai son wainar dake soyawa ba.

Shi dai bai da buri da muradin da ya wuce ya ganshi tare da Asma'u.

Kowa da yasan Aslam yasan Asma'u dan kowa yasan irin son da yake mata.

Abokan sa har tsiya suke masa su ce, ya makalewa karamar yarinya me ya gani agun ta.
Chapter 15 · 0% Book details