← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 61

Sashe 51

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaa Buhari ya ce,
"Eh man wallahi aka zan fitar da ke."

Mikewa tayi ta fara zubar da hawaye. Murmushi Mami tayi ta ce,
"To mene na kuka. Haba Husnahn Dady ki daina kuka bayan ga Momyn ki can tana jiran zuwan ki."

Kai tai kasa da shi amman hawaye ya kasa daina zuba.
Yaa Aslam kuwa kukan da take ji yake kamar yai me dan sam baya son kukan Asma'u.

Zainab ce ta kama ta ta ce,
"Haba Asma'u ki daina mana."

Suka mike suka fita har da mami ta raka su compound sannan ta dawo.

Asma'u kuwa sai jikin ta ya kara sanyi na jin rabuwa dai zatai da gida

Sai da suka fita daga gida Aslam yaji Asma'u na kuka.
Motar yasa Buhari ya tsayar sannan ya koma gidan baya.

Jikin sa ya jata yana lalashi ta a hankali a hankali.

Sannu a hankali tayi shiru. Tana rasa dalilin da yasa in har tana tare da Yaa Aslan take jindadi a ranta. Ko taji ta samu relief.

A haka suka karasa airport ba tare da sun san anje ba. Har sai da su Yaa Buhari suka fita sannan yai musu knocking.

Dogowa sukai yai musu nuni da waje. Jikin ta ta kwace daga nashi ta fita da sauri.

Jakar ta ya dauka ya fita yana murmushi. Suna zuwa aka fara kiran su.

Ba jima ba suka tashi. Asma'u na hawaye dan sai Yaa Aslam ne ya tallabe ta yana lallashi har suka shiga jirgi.

A cikin jirgin ma jugum tayi tana kwance a kan kafadar sa.

Suna sauka har motar gida tazo daukar su.

Gida sukai. Asma'u duk sai taga gidan ya canja da ta jima bata je ba. Ba kamar da da ta samu hutu taje ba.

Amman yanzu a kalla tai shekara biyu zuwa uku ba tazo ba.
Suna fitowa Momy ta fito ta kama ta. Cikin gidan ta shige da ita aka bar Aslam da daukar jaka.

Sama ta nufa da ita tana. Dakin guda aka kai ta.

Ruwan wanka Momy ta hada mata sannan ta sauka.

Bandaki ta shiga. Kafin ta fito an jere mata kayan abinci.

Mai ta shafa ta saka wata bakar doguwar riga da ta gani akan gado.

Sallah tayi tana zaune akan sallaya ya shigo dakin.

Dagowa tayi ta kalle shi ta dauke kai. Sanye yake da wando three quarter daga alamu shima wankan yayi.

A gaban faranti da aka jero mata abinci ya zauna.

Ya ce,
"Bismillah"

Kai ta girgiza ta ce,
"Alhmdlh"

Murmushi yayi ya ce,
"Humm! Ai gwara ma kici domin nasan baki ci komai ba duk yinin yau ga idanunki duk sun kumbura saboda kuka"

Fuska ta bata ta ce,
"Wa kuma yace maka banci abunci ba"?

Kusa da ita ya matsa daf ya d'ora tsinin dogon hancinshi akan nata. Ajiyan zuciya ya sauke. Yana kallon ta ido cikin ido yace,
"Nasan Husnah d'ita fiye da yanda take zato. Idan tana fad'amin gaskiya ina ganewa idan kuma tana fad'amin karya ma ina ganewa. Dan haka kina sanin abinda zaki fada min. Oya So let's eat, drink and....."

Bai karasa fadar abinda xai fada ba ta ce,
"Me?"

Bai bata amsa ba sai kiss da yai mata a kumatu. Harshenta ta fito dashi a waje.

Ai kam Charaf Yaa Aslam yasashi a baki. D'an kokarin tureshi ta farayi ganin ya fara sarrafata yasa tai la'asar. Har cikin kwanyar kanta take jin kiss din da yakeyi mata. Sai daya gama da kanshi ya d'an ja da baya kad'an.

Kallon ta yayi da idon sa da sukai jajir ya ce,
"Now let's eat"

Asma'u da jikin ta yai sanyi sosai tai kasa da Kanta ta dauki cokali ta fara cin abincin a hankali.

Kallon ta ya tsaya yi. Sannan ya bude dayan fulas din naman kazan ne a ciki. daukowa yyai ya mika mata. Amsa tayi tana ciki a hankali duk jikin ta a sake.

Lemo ya mik'a mata, cikin sanyin murya tace
"Na koshi."

Cup d'in yai gefen bakin ta da shi. karba tayi ta kai bakin ta ta sha kad'an ta janye ta maida ta aje.

"Duka zaki shanye"
Yaa Aslam ya fad'a yana murmushi.

Hararar sa tayi ta ce,
"Haba dan Allah ni ina zan iya shanye wannan? Wallahi na koshi."

Aslam yai murmushi ya ce,
"Kokartawa xakiyi ko in maki d'ore kamar yadda da nake miki."

Kai ta dauke, tana hararra sa ta kasan ido.

Yau Kwata kwata sai take jin Yaa Aslam ya koma mata wani sabo daban. Ga shi tana kasa hana shi duk abinda yake mata.

Ba yanda ta iya illa ta sha kamar yanda yake so. Shima kai ya kafa yasha nashi. Tashi yayi ba tare dayace mata komai ba ya fara cire rigarshi. Idanu ta zubawa kirjinshi da kwanjunan hannunshi.

Murmushi Yaa Aslam yayi ya nufi wajen ta.

Duk'awa yayi da niyar daukar ta. Ta mike za tayi waje.

Kamota yayi ya dauketa ya direta kan gadon ya kura mata idanu. Cikin sanyin murya yace
"Kina sona Husnah?"

Banza tai masa kamar ba da ita yake ba.
Murmushi yayi, ya zura hannun shi ta cikin rigar ta yai kark'ashin bayanta.

Sannu a hankali ya fara d'age mata rigar jikin ta. Tana jinshi tai lamo kaman wadda batada rai. Kirjin ta sai dukkan uku uku yake

Tana son ta hana shi amman ta kasa.

Fuskan shi ya d'aura a kan nata ya fara gogo mata hancinshi. A hankali ya tallabota ya fara cire mata rigan. Tsotsan kunne ya fara yimata cikin natsuwa yana hura mata iska a ciki. Jin sanyin AC na ratsata ta ko ina na jikinta yasa ta farga batada riga.

Jawo Hijab din ta tayi ta rufe kirjinta. Ajiyan zuciya Aslan ya sauke. Kara matseta yayi da kirjinshi sosai. yana shafa bayanta a hankali hadi da mazaunanta.

Sanin zata iya guduwa a ko da yaushe yasa ya kara matsa ta a jikin sa.

Hannu ya d'ora akan gashin ta ya 'dago fuskanta ya kaimata sumba a wuya, lips d'inshi ya tura cikin bakin ta a hankali ya fara tsotsawa yana zare bra dinta... Hannunshi ta rike gam. Chaan kuma ta saki ta zubawa sarautar Allah ido...

Tasan ita halak dinsa ce to amman kuma tana tuna abunda yai mata.

Tana can tunani taji ya fara wasa da ita sosai da sosai.

Sosai jikin ta ya fara rawa, Duk sun fita a cikin hayyacinsu daga ita har shi.

Hannun sa ta rike tana girgiza masa kanta. Ta ce
"Dan Allah ka daina Yaa Asl......"

"Shhhhhhhhhhh. Enough" ya fad'a yana k'ank'antar da murya chan k'asa 'kasa.

Fuskantar ta juyar saboda ya matse ta ba damar tashi. ta fashe da wani irin kuka.

Kuka sosai takeyi. Ganin ya kasa shawo kanta yasa Aslam sakin ta yana maida numfashi yana ajiyan zuciya.

Da sauri ta mike ta saka kayan ta ta fice da sauri.

Yana kallon ta ya saki ajiyar zuciya ya gyara kwanciyya.

Tabbas yasan da duk abinda ya faru bai faru ba da yanzu yaga jinin sa a tare da Asma'u.

To amman ji yadda Asma'u ke gudun sa kamar dodo.
Asma'u da inda yaje gida suke tare kullum amman yanzu sai dai daga nesa.

Har gara yau ma ya samu damar zama kusa da ita har ya umarce abu tayi.

Yana son Asma'u so bana wasa ba. Amman ya rasa ta yadda zai nusar da ita ta yadda.

Asma'u na fita tayi dakin Momy, Momy na zaune suna waya da Mami tana fada musu sun sauka lafiya.

Asma'u na shiga ta ce,
"Ga ta nan ma."

Ta mika mata wayar. Gaisawa sukai tai musu ya hanya.

Kan gadon Momy ta hau. Momy ta kalle ta ta ce,
"Kinci abincin ne?"

"Eh naci."
Momy ta ce,
"Me kike bukata?"

"Ba komai!"
"To kwanta ki huta."

Ta kwanta.

*MS Indabawa*
[1/18, 14:39] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐

Dedicated to *My lovelly Mum*

*101-105*

Yau kwanan su biyu a gidan Momy amman zai iya cewa rabon sa da Asma'u tin ranar da suka zo.

Kullum tana daki a rufe bata fitowa falo ko da fito da ta ji shi take komawa.

Ya zuba ido yaga Momy ta ce, su koma gidan su amman Momy tayi shiru.

Haka ne yasa aka je aka share gidan a goge dan ya kagu ya tare.

Momy kuwa tana can tana shirya musu walima da za'ayi ne kafin su tare tinda ba wani biki akai ba.

Yau ya cire kunya ya ce zai fadawa Momy shi ta bashi Asma'u su tare.

Yana shigowa ya same ta akan kujera tana duba wasu takardu.

Yana zama ta mika masa wasu takardun. Amsa yayi yana dubawa.

Dagowa yayi yana kallon ta. Murmushi tai masa ta ce,
"Eh ai dole a hada maka walima Allah yayi Asma'u matar ka ce."

Murmushi yayi ya koma gefen Momy ya kama hannun ta sai hawaye.

Kallon sa tayi ta girgiza masa kai. Ta ce,
"Mene na kuka?"

"Dole nai kuka Momy. Momy kina sona Allah ya biya miki bukatun Alheri Allah yasa ki kyakyawan karshe."

"Ameen! Duk wannan addu'ar ta mece?"
"Momy kina sona da Asma'u kiga lokacin da nace bana son ta ke kika ce A'ah amman na ki sam. Wallahi Momy ban san me ya raba ni da Asma'u ba dan ban taba jin kin ta ba. Kullum da ita nake kwana nake tasho. Ina son Asma'u Momy."

Asma'u da fitowar ta kenan taji yana maganar tai saurin komawa daki.

Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ga hawaye nan ta rasa hawayen me take yi.

Momy kuwa, hawayen sa ta share masa ta ce,
"Ai Allah zaka godewa da yada Asma'u taka ce, gashi har ka mallake ta."

"Haka ne Momy ina gode masa a ko da yaushe. Kuma ina gode muku."

Ya mike ya ce,
"Bari naje na fara rabo."

Momy ta ce,
"A'ah sai na ji ta bakin ta tana son naka ne har yanzu ko aah."

Dariya yayi Ya fice, yana cewa,
"Momy tsokana"

dariya Momy tayi dan a duniya tana son dan nan mata daya guda tilo. Duk farin cikin sa shi take fata.
Chapter 51 · 0% Book details