← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 61

Sashe 37

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Buhari ya ce,
"Zan fadawa Mami da Asma'u bama Asma'u tana da sani sosai a addini. Nasan zata san abin yi. Amman dai ya dage da addu'a muma mu dage da taya shi da addu'a."

Mami ta ce,
"Insha Allah!"

Haka suka tashi suka tafi kowa ran sa ba dadi.

Buhari kuwa sosai yake tausayawa Aslam dan ya kasa sukuni.

A haka yai bacci. Cikin dare ma ta shi yayi ya dinga masa addu'a.

Asma'u kuwa Sai magariba ta koma gida. Tana shiga taga motar Sir Sabir.

Kai ta dauke tayi cikin gida. Yana zaune a falo yana cin tuwon da Mami ta dafa.

Tana shiga suka hada ido. Durkusawa tayi ta gaishe shi ya amsa yana binta da wani kallo wanda tasan Yaa Aslam na mata.

Ido ta dauke har zata wuce sai kuma taga Mami ta fito daga kitchen hannun ta rike da lemo da ruwa.

Karasawa tayi ta amsa, sannan ta zauna.

Mami ce ta kalle tace,
"Kun dawo?"

Kai Asma'u ta gyada. Mami ta ce,
'Buhari ya kira ki ne?"

"A'a! Ya na ina ne banga motar sa ba."
Mami ta ce,
"Ya tafi Abuja,"

Wata faduwar gaba taji dan tasan wajen Momy yaje, kuma zai hadu da Yaa Aslam.

Shiru kawai tayi ta jingina da kujera tana lumshe ido.

Mami ce ta lura da canjawar da tayi. Kallon Sabir tayi shima Asma'un yake kalla.

Mikewa Mami tayi ta hau sama. Yana jin shigar war Mami daki ya matso kusa da ita ya zauna.

Asma'u bata ji zaman sa ba sai kawai muryar sa da taji a dai dai kunnen ta.

Ido ta bude da sauri. Ido suka hada yana kallon ta ido cikin ido.

Duk sun kasa dauke idanun su. Shi wani kallo yake aika mata.
Ita kuma wani abu taga yana fitowa daga idon sa yana shiga nata.

Da sauri ta lumshe ido dan baza ta iya jure kallon da yake mata ba.

"Husnah!"
Ya kira sunan ta cikin sanyin murya.

Ido ta bude a hankali ta sadda kan ta kasa.

"Husnah! Wai haka kike so ki cigaba da rayuwa ba farin ciki. Ke kenan baza ki samu wanda zai sa ki farin ciki ba. Ki tattara komai naki kin bawa Yaa Aslam, husnah ba haka rayuwa take ba. A duk sanda wani ya ce baya yi da kai a lokacin wasu keyi dake, ki dauri ki ban dama zan kasance miki yadda kike so na kasance."

Shiru Yayi yana kallon ta. Idon ta alumshe kuma daga dukkanin alamu tana jin sa. Kuma maganar ta ratsa ta.

"Husnah!"
Ya kara ambatar sunan ta.

Bude idon ta tayi da sauri jin kamar muryar Yaa Aslam.

Sai dai me ba shi bane, mikewa tayi da sauri tayi hanyar bene.

Har ta hau sai kuma ta juyo. Kallon sa tayi shima ita yake kalla.

Murmushi ta sakar masa kawai ta haye sama.

Mamaki ne ya lullube shi. Ya rasa murmushin nata me yake nufi.

*MS Indabawa*
[1/18, 14:29] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer's*

Dedicated to *My lovelly Mum*

*31-35*

*Ba abinda zzan ce da masoya karanta littafai na sai godiya mai tarin yawa.*
*A gaskiya ina alfahari da ku. Allah ubangiji ya bar zumunci. Ina kaunar ku saboda Allah*

Zama yayi shima yai murmushin kawai.

Mami ce ta sauko. Hira suka dan taba sannan yai masu sallama ya tafi.

Zuciyar fal da tunanin Asma'u. Yana kaunar Asma'u son Asma'u yai masa wani irin kamu.

Asma'u kuwa tana shiga daki ta fada kan gado.

Ido ta lumshe ba wanda ya fado mata sai Yaa Aslam, Ta jima tana juyi duk ranta ba dadi sannan ta mike ta shiga cire kaya.

Tana gamawa ta fada bandaki wanka ta fara. Tana gama wa ta tayi alwala.

Sai da ta shirya cikin kayan baccin ta dogon wando da riga fare tas sannan ta tada sallah. Ta jima tana addu'a kan Allah ya kawo mata dauki sannan ta Mikewa jiki a sanyaye ta bude firij.

Lemo ta dauko ta koma kan gado ta zauna. Wayar ta ta dauka ta latsa number Yaa Buhari.

Da sauri ya dauka. Murya ta shagwabe ta ce,
"Yaya shine ka manta dani ko?"

Murmushi yayi ya ce,
"Tayaya zan manta dake Sis. Na ta neman number ki ke da wife ban same ku ba."

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce,
"To Yaya Ya hanya yasu Momy da Dady."

"Suna lafiya. Ince kuma kuna lafiya."
Kai ta gyada masa.

"Asma'u me yake dumun ki?"
Dan yaji muryar ta ba dai dai ba.

Damuwar ta tai kokarin kawar wa sannan ta danyi murmushin karfin hali ta ce,
"Ba komai."

"Kin tabbata?"
ya tambaye ta.

Kai ta gyada masa. Yace
"To sai da safe."

Sukai sallama. Kwanciyya tayi tana tunanin Sir Sabir kuma.

"To tinda na rasa Ya Aslam me yasa ba zan karbi duk wanda ya so ni ba. Sir Sabir bai da makusa. Yana da kyau ga ilimi ga addini ga nutsuwa me kuma zan nema bayan nan."

Tayi juyi, ta kuma fadin,
"Duk da haka dai ina son Yaa Aslam ko ba komai Yaa Aslam yayanah ne,"

Hawaye ne ya zubo mata. Ta jima tana kuka sannan ya mike tayo alwala ta tada sallah.

Ta jima tana kai kukan ta gun Allah. Sannan ta hau karatun Alkur'ani.

Har akai sallah asuba tana kan sallaya. Wanka ta kara yi sannan ta dawo ta tada sallah.

Tana idar wa ta fada kan gado sai a lokacin wani bacci mai nauyi ya dauke ta.

Mami tinda ta tashi bata ga Asma'u ba ta leko ta tadda tana bacci ta sauka kasa kawai. Dan tasan ba zata aiki ba tinda bata sauko ba.

Aiki tayi ta hada musu break sannan ta yi wanka.

Har karfe biyu Asma'u bata sauko ba. Mami Ta hau sama ta dubo ta yafi sau uku amman bacci take kuma jikin ta ba zazzabi.

Wannan ne yasa Hankalin Mami ya dan kwanta.

Karfe biyu da rabi Zainab ta karaso gidan. Mami ta gani zaune a falo.

Har kasa ta durkusa ta gaishe ta cikin jin kunya.

Mami ta amsa cikin sakin fuska da soyayya.

Mami ta ce,
"Ki hau sama yau tana can ko aikin ma bata je ba."

Zainab ta ce,
"Mami lafiya dai ko?"

Mami ta ce,
"Lafiya lau, ina jin dai abin ne ya fado mata kuma."

"Allah sarki."
Zainab ta fada tana mikewa. Ta ce,
"Mami addu'a dai xamu ta taya ta da ita."

"Haka ne, Zainab Addu'a kuma kullum yi muke. Sai dai fatan Allah ya amsa.'
"Ameen!"

Ta hau sama. Asma'u na kwance ta daka mata duka. Da sauri ta mike tana sosa wajen da ta dake ta.

Tana mutsuka ido. Kallon ta Asma'u tayi ta ce,
"Zainab har kin zo?"

"Eh! Kinsan karfe nawa kuwa?"
Ta fada tana kallon idon ta da suka kumbura saboda kuka.

Asma'u ta ce,
"Uhmm wallahi bacci na sha ban sani ba."

Ta fada tana mikewa tsaya, kallo Zainab tabi ta dashi har ta shige bandaki.

Kai ya girgiza, a rayuwar ta tana son Asma'u tana jin Asma'u kamar kanwar ta, duk abinda ya damu Asma'u itama damun ta yake.

Ta rasa tayaya zata shawo kan Asama'u har ta daina damuwa. Duk da tasan da wuya.

Mikewa tayi ta gyara gadon ta share dakin sannan ta koma ta zauna.

Tana zama Asma'u ta fito tana tsane jikin ta. Kallon dakin tayi ta kalli Zainab ta ce,
"Ke dai bakya gajiya wallahi."

Ta zauna tana shafa mai, ta ce,
"Yau ina zamu?"

"Ke dai ki sauri zamu je, madobi fa."
Kai Asma'u ta gyada.

Mai kadai ta shafa ko powder bata shafa ba ta mike ta saka wata doguwar rigar Atamfa. Mai A shape. Tana da dogon hannu. Mayafin after dress ta yafa ta dau wayar ta da mukullin mota ta ce,
"Muje ko?"

Zainab ta ce,
"Kin karya ne?"

"A'ah muje zan dau Maltina ta ishe ni ma."
Mikewa tayi tabi bayan ta.

Mami tana falo tana ganin su ta saki murmushi ta ce,
"Kun fito."

Asma'u ta ce,
"Eh! Mami ina kwana?"

Mami ta amsa, da
"Lafiya lou kin tashi lafiya?"

Kai ta gyada ta mike ta nufi firij din falo ta dauki Malt guda biyu ta ce,
"Mami mun fita zamu je Madobi wajen yan ajin mu."

Mami ta ce,
"To a dawo lafiya. Allah kiyaye hanya."

Suka fita. Suna fita suka ci karo da Sir Sabir zai shigo.

Wajen sa suka karasa suka gaishe shi cikin girmamawa. Amsa yayi yana bin Asma'u da kallo. Bai taba ganin ta da irin wannan shigar ba.

Zainab ya kalla ya ce,
"Amare ina zaku ne?"

Asma'u, Zainab ta kalla ta ce,
"Wallahi kati zamuje rabawa daga nan mune har madobi."

Kallon su yayi ya ce,
"Madobi da kanku. A'ah muje na kai ku. Daman Buhari yai min maganar zuwa Madobin."

Asma'u, Zainab ta kalla ta ce,
"Sis kinga Sir Sabir ya rage miki aiki."

Asma'u dake danna wayan ta, ta dago ta kalli Zainab sannan ta kalli Sir Sabir da ya zuba mata ido.

Murmushi ta dan saki ta ce,
"Da ka huta ai."

Dan Hararar ta yayi ya ce,
"Ku shige muje."

Ya bude mata gidan gaba. Zainab dai kallon su ta tsaya yi tana cewa Allah yasa Sir Sabir ya so Asma'u dan ba karamin dacewa sukai ba.

Ga wani kallo da taga yana binta da shi.

Da haka ta shiga gidan gaba. Zainab ta shiga cikin gidan baya.

Maltina ta mikawa Zainab sannan ta mikawa Sir Dabir dayar ta hannun ta.

Bai amsa ba ya ce,
"Ke fa?"

Murmushi tayi ta ce,
"Na koshi."

Ya ce,
"Ban yadda ba sha ki rage min."

Zata ce A'ah ya ce,
"Ki sha ki ragen in ba rowa zaki min ba."

Fasawa tayi ta sha kadan ta mika masa, hannu ya kawo zai amsa ya hade da hannun ta.

Kallon sa tayi ya kashe mata ido daya. Kai ta dauke ta cigaba da kallon titi.

Shiru tayi sai Zainab da Sir Sabir da suke hira.

Sai dai shi da yake dan tabo ta, in anyi abu ya ce,
"Ko Husnah?"

Da haka har suka karasa gidan su Hafsat.
Chapter 37 · 0% Book details