Sashe 6
Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kanwar su kuma autar su Mariya wacce take aure a kaduna itama mijin ta soja ne. Ya'yan ta uku duk maza. Umar, Usman, Aliyu.
Amina Maman *Asma'u* ta kasance yar aminin Kakan *Asma'u* wato Baba Haruna.
Amina su biyu Allah ya bawa mahaifin ta Malam Isah da matar sa Hafsat. Da yayan su Fatima da Amina.
Yayar ta na auren minister of Agriculture wanda suke zaune a Abuja.
Aslam shi kadai ne danta. Wanda shi kuma yayi karatu a Kasar waje fanin asibiti wato medicine kwararen likitane.
Amina da Suleiman sunyi auren soyayya ne wamda har yanzu suke shan soyayyar su.
Zuri'ar ta kasance ba mace a cikin ta illa *Asma'u Husnah*
*Asma'u Husnah* ita kadai ce jika mace ga Haruna da Isah, wannan yasa dukkan family din suke son ta da kaunar ta.
Bama Aslam da yake da son yara. Dan da aka haifi *Asma'u* sai da kyar ya bar gidan shima dan makaranta ne.
Soyayyar ta dai da ita ya tashi. Sai kuma Allah yayi *Asma'u* irin yaran nan ne masu shiga rai.
Dukkan yan uwan ta son ta suke. Yarinya ce wacce tin da aka haife ta take da kyan ta duk da baka ce amman bakin ta me kyau ne su ake kira da black beauty.
Dan *Asma'u* komai Allah ya bata. Shekarar ta biyu aka sa ta a makaranta. Inda tana da shekara biyar tana nursery two.
Allah ya bata kokari duk da karancin shekarun ta inda aka dinga mata jumping din classes.
Shekarar ta takwas ta gama primary ta tafi secondary. Tana da shekara goma sha hudu tayi candy.
A lokacin Ta fara girma dan ta fara kirgar dangi. Kyawun ta ya dada fitowa.
Tana yin candy ta samu admission inda take karantar medicine yanzu haka Asibiti zasu tafi.
Tin tana primary ta sauke alkur'ani inda yanzu haka tana da haddar sa akai.
Kuma bata daina yi ba. tana kanyi dan duk juma'a take bawa Mamin ta haddar. Karatun ta baya hana ta haddar ta. Kamar yadda duk asabar da lahadi take zuwa isilamiyya da safe.
*Asma'u* yarinya ce me fara'a da barkwanci da son jama'a. Koma abin hannun ta be rufe mata ido ba.
Akwai tarbiyya dan duk yadda mutum ya girme ta zata bashi girman sa.
Akwai ta da son zumunci. A duniya tana son Dadyn ta kamar yadda shima duk duniya bai da wacce yake so irin ta.
Kullum bata da buri sai na ganinnta kyautata masa. Yan uwa kuwa kowa ya samu abin mata ko ya burgeshi sai ace *Asma'u!*
Kowa sha'awar ta yake. Tin tana karama tayi mugun sabo da Aslam wanda in yaxo shi ke rainon ta gaba daya.
Da anyi magana zaice *Asma'u* matar sa ce. Wannan yasa Dadyn *Asma'u* shaidawa zuri'ar su cewa ya bawa Aslam *Asma'u* ko yana da rai ko be da rai *Asma'u* ta Aslam ce.
Aslam yaji dadin wannan hadin da akayi musu. haka ma Dadyn sa da Momyn sa.
Inda sauran yan uwa masu son ta kowa ya janye kudurin sa yana sanya musu albarka
Sam *Asma'u* bata san anyi ba dan a lokacin tana da karancin shekara bata san anyi ba.
*ASLAM*
Aslam saurayi ne dan shekara talatin kuma kwararen likita. Yana da katon asibitin sa wanda Mahaifin sa ya gina masa.
Aslam yaro ne me farin jini, shima akwai fara'a da son yan uwan sa.
Yan mata da yawa na son sa amman shi sam bai basu fuska.
Dan yakan ce shi yana da *Husnah* sa kowa yasan sa da *Husnah*
Daga cikin yan matan nashi ne ya hadu da preety wacce ta nace masa kuma tai wa kanta alkawarin duk daren dadewa sai ta aure shi.
Aslam kyakyawa ne na karshe. Dan sai ka zata balarabe ne. wannan ya samo asali ne saboda, kakarsa dan yar libiya ce.
Fari ne dogo jikin sa a murde dashi. Idanun sa manya, da siririn hanci sa da pink lips din sa.
Duk jikin sa gashi ne kwance luf luf. Haka nan kansa suma ce cike a cikin ta. Wacce ita take karasawa ake ce masa balarabe.
Aslam na son *Asma'u* sosai dan bai hada son ta da komai. Duk abinda zai faranta mata yana mata sai dai in yaga ba dai dai bane.
Shi yake kara daura ta akan karatun ta dan ta waya zai mata bayanin duk abinda bata gane ba.
Haka fanin addini ma duk takan tambaye shi koma meye dan ya riga da ya sabar mata.
Dan ko wankan tsarki shi ya koyamata kafin ayi musu a isilamiyya.
Haka wasu hukunce hukuncen duk yana sanar da ita dan babu kunya tana daukar sa tamkar Ya Buhari.
Aslam shi ya hana a sanar da ita maganar bashi ita da akayi duk da yaga ta girma.
Ya fadawa Dady kan a bari ya janyo hankalin ta tukunna. Dan haka bai dade da sanar da ita kudurin sa akanta ba.
Lokacin da ya tare ta ba karamin nauyi abin yayi mata ba sai daga baya da kyar ta sanar masa ta amince.
Amman duk son da yake mata in tayi masa laifi sai ya mata fada haka in koyar karatu ne ya tashi zasu ajiye batun soyayya a gefe. ya koya mata kome inda ya kamata ya koya mata.
Haka in fanin soyayya ne ba a baya ba wajen fitar da duk abinda ke zuciyar sa ya fada mata
Yasha fada mata.
"Wallahi *Husnah* duk abinda nake fada miki wallahi daga cikin zuciyata yake ba koya ko kwafar na wasu nake ba. Abinda nake ji game dake, shi nake fada miki."
Sosai yake mantar da ita duk damuwar ta da abinda yake damun ta ya faran ta mata.
*Asma'u* kanji duk duniya ba wanda ya kai ta wajen samun soyayya.
*INDABAWA*
[1/18, 14:08] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*
BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*
🌐 *HAJWO* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
*Gidan Hakuri da juriya, tare da kawar da kai.*
Facebook @ Indabawa Hausa Novel
Wattpad @ Msindabawa
instagram @ Maryam S Indabawa
*31-35*
DEDICATED TO *MAMAH NAH* Allah kara miki lafiya da imani yasa ki gama lafiya.
*Ameen!*
*Manzon Allah (SAW) Yace "Kuyi sahur domin a cikin sahur akwai albarka"
Kamar ko yaushe tin asuba da ta tashi bata koma ba, bare yau da tasan suna da Sir Sabir.
Da wuri ta sauka kasa ta gama duk abinda ya kamata tayi. Ta dawo dakin ta tayi wanka ta shafe jikin ta da mai.
Durowar ta ta bude, ta tsaya kallon ta tayi minti Biyar a wajen sannan ta samu ta zaro wata bakar doguwar riga.
Hannun rigar an masa irin dinkin babbar riga da wani yadin material me multicolour (Kaloli daban daban.) Sai gaban rigar da aka masa ado da stone (duwatsu) aka jere wasu manyan jajayen stone (duwatsu) guda takwas suma.
Dago rigar tayi tana kare mata kallo, Ya Aslam ne ya siyo mata da yaje dubai. Juya ta ta kara yi, sannan ta dire akan gado.
Wani jan skin tied ta dauko sai jar bra da pant, saka su tayi a jikin ta. Sannan ta dauko rigar ta saka ta daure ta, ta ciki.
Jan hijab ta dauka wanda iya kar shi saman kirjin ta. Wani jan sandal ta dauko tasaka a kafar ta.
Sai bakar jaka da ta zuba abin da take bukata. A kan gado ta ajiye jakar da wayar ta.
Dakin Dady ta nufa, sai da yasa ta ci abinci sannan ya barta ya tafito.
Jakar ta ta dauka, sannan wayar ta.
Sakon Ya Haidar ta gani, budewa tayi tana murmushi.
" *Assalamu Alaikum*
Da fatan Baby na ta tashi lafiya, yasu Mami da Dady da Buhari. Ina fatan duk kuna lafiya.
Daman zan fada miki ne ina kan hanyar Kaduna, ina bukatar addu'ar ki, in na isa zan kira dan nasan yanzu ba kya kusa."
Murmushi tayi sannan ta nemi waje ta zauna.
Sakon fatan alheri da isa lafiya tayi masa sannan ta tura masa.
Ta jima tana tunani sannan ta tuna fa makaranta zata tafi.
Da gudu ta fita tayi dakin yayan ta. Bacci sa yake kamar kullum, gadon ta fada.
Da sauri ya mike,
"Ya Salam!'
Ya fada yana dafe kai. Murmushi ta saki,
"Ina kwana yayanah."
Harara ya wulla mata, ya mike ya shige ban daki. Zama tayi jiran sa.
Wayar ta ce tayi kara, ta dauka.
" *Asma'u* tara saura minti goma dai."
Ido ta zaro waje tana mikewa,
"Dan Allah da gaske,"
"Duba agogo ki gani."
"Innalillahi wainna illahir rajiun. Gani nan gani nan."
Ta fada tana nufar kofar ban dakin.
"Yayah! Yayah!"
Banza yayi mata. Kuka ta fashe masa dashi.
"Yayah!"
Ta fada cikin kukan. Shiru ya kara yi mata. Ya cigaba da cuda jikin sa.
Sai da ya gama sannan ya dauro shawul ya fito. Tana jikin kofar a tsaye.
Kallon ta yayi ya dauke kai ya fara goge jikin sa. Yana zama a gaban mudubi.
Karasawa wajen sa tayi da sauri, ta durkusa akan gwiwo yin ta tace,
"Yaya da Allah ka zo kakai ni makaranta na makara."
Mai ya cigaba da shafawa. Kuka ta saka masa sosai.
"Rufe min baki."
ya fada fuskar sa a bace.
"To Yaya dan Allah ka kaini makaranta."
ta fada tana hade hannun ta gu daya.
"Ina Baba da yake kai ki makaranta."
tace,
"Yaya na makara kuma Baba makara zamu yi dan baya gudu wallahi."
"Ni ba inda zan kai ki."
Kuka ta kuma saka masa.
"To ya isa tashi bari nasa kaya. Toh ta fada tana fita, dakin Mami ta ttafi dan mata sallama.
Kallo Mami ta bita dashi ganin idon ta yayi ja.
"Me yasami idon ki, kuma daman baki tafi ba."
Asma'u ta ce,
"Yaya ne yasa ni kuka."
Mami ta ce,
"Akan me?"
Tace,
"Na makara yaki yazo ya kai ni."
"Kin je tsokana har kika makara ko."
"A'ah!"
"Yanzu yana ina?"
"Shiryawa yake, yanzu zai zo ya kaini."
"Ok jeki same shi."
Juyawa tayi, sai gashi nan ya shigo, cikin blue (ruwan omo) din shadda wacce akai mata aiki da dark blue, (ruwan omo me turuwa) blue hula yasaka, da bakin takalmi sai bakin agogo a daure a tsintsiyar hannun sa.
Sosai yayi kyau, ya fito kamar wani tauraro, sai tashin kamshi yake.