Sashe 26
Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To Mami Allah yasa mu gama da duniya lafiya. Allah ya mana makoma da gidan Aljanna in lokacin yayi."
"Ameen *Husnah* dan Allah kar ki manta kina sa ya'yan ki suna min addu'a."
"Insha Allahu. Dady ka daina sa wannan a ranka. Kai ma zaka rayu da su. Su sanka insha Allahu."
Murmushi Dady kawai yayi, daga haka suka cigaba da taba hira.
Aslam fa ba zama lafiya tinda abin nan ya kara karatowa ya kara burkice ya duk wani plan nashi na auren su ne.
Bai da magana da shirye shirye in ba na auren su ba.
Katon Gidan sa da ya gama dankarawa yasa akai masa fenti aka gyare shi.
Lokaci kawai yake jira.
Preety ce kwance akan kujera gefen ta kawar ta ce, Nene, kallon ta Nene tayi ta ce,
"Haba Pretty ki hakura da yaron nan kina ganin ya kusa yai auren shi ma."
Mikewa Pretty tayi ta ce,
"Wallahi sai Aslam ya aure ni. Kinji na rantse ko zan yawo tsirara sai na aure Aslam. Ita kuma Asma'u take ko *Husnah* zata gamu dani sai ta dandani irin yadda naji da yake son ta ni baya so na."
Ta fada tana girgiza kafa, Nene ta ce,
"Pretty ki dai yi a hankali kinsan komai zakiyi akwai karshen sa ko?"
Kallon ta Pretty tayi ta ce,
"Ke dallah ya isa kuma daman ance makashin ka yana tare da kai. In ba haka ba duk yadda muke dake xaki ce na rabu da su ko me? To naki. Wallahi sai na samu Aslam ko da me zai faru daga baya."
"Allah baki hakuri. Ban fada dan na bata miki rai ba."
Tsaki Pretty tayi ta koma ta kwanta ranta a bace kamar me.
Ita fa bata da buri da ya wuce ta ganta gata ga Aslam.
Tana son Aslam ko dan gayun sa da iya shigar sa da kyan sa.
Ba abinda ya yafi rudar ta kamar kyan sa.
Ido ta lumshe tana murmushi ta ce,
"Wa ya ga Pretty amaryar Aslam!"
Ta bude ido ta yin shewa. Kallon ta Nene kawai tayi ta dauke kai.
Asma'u ce kwance akan gadon ta tana amsa wayar Aslam.
Sai murmushi take, ko magana ta kasa daga ta ce, 'Eh' sai kuma ta ce, 'A'ah' sun jima suna hira sanna sukai sallama.
Kwanciyya ta gyara tana ayano gata ga Yaa Aslam anyi auren.
Ido ta rufe da hannun ta alamar taji kunya.
Can ta bude su, ta kurawa saman dakin ido.
Tunanin yadda suka tashi tare da Yaa Asalm ta dinga yi har yanzu da suka girma har a kai maganar auren nasu.
Murmushi tayi kafin ta ce,
"Ni *Asma'u Husnah* in na rasa Yaa Aslam ya zanyi."
Da sauri ta mike idon ta sun kawo ruwa ta ce,
"Allah na tuba Allah kada ka jarabace ni da rasa Yaa Aslam. Allah ka bani Yaa Aslam."
Ta koma ta kwana sai kuma kuka sai kace an dake ta. Sosai take kuka. bacci ne ya dauke ta shine aka samu tayi shiru.
Tin lokacin jikin ta yai sanyi ta rasa me yake damun ta.
Karfe sha dayan dare Bayan Mami da Dady sun tafi daki.
Zama sukai Dady yana bata takardun kadarorin da ya mallaka musu.
Mami ta ce,
"Ai Dady da kabar su agunka."
"A'ah ku rike abinku. Gara ki saba dan in bana nan yazai adana muku."
Amsa Mami tayi ta ce,
"Alhaji kenan."
Yai mata murmushi.
Alwala sukai suka kwanta.
Can wajen karfe ukun Dare Dady ya farka da wani irin ciwon ciki.
Ciwon ciki ne, wanda bai taba jin kamar sa ba duk da kwana biyun nan yana yin sa a dadafe a dadafe amman na yau ya banbanta.
Tin yana daurewa har ya tada Mami daga Bacci.
Mami na ganin sa a halin da yake ta mike da sauri tana tambayar sa, lafiya.
Kasa magana yayi. Da sauri Mami ta mike ta kunna fitila.
Ciki ta ganshi dafe dashi, maganin Ulcer, ta dauko ta bashi yasha.
Dan lafawa yayi dan har ya fara bacci sai ya kuma tashi.
Na wannan karan har yafi na dazu ganin wahalar da yake sha yasa Mami ta tafi dakin Buhari ta taso shi.
Da sauri ya biyo bayan ta a durkushe su ka tadda shi ya dunkule gu daya sai juyi yake.
Buhari ya ce,
"Mami bari a fito da mota mu tafi asibiti kawai."
Ya fita da sauri shi ya kama Dady, Mami kuma ta shiga dakin Asma'u.
Zaune ta same ta akan sallaya, Asma'u na ganin Mami ta mike da sauri ta ce,
"Mami lafiya?"
Mami ta ce,
"Dady ne ba lafiya."
Da sauri Asma'u tayi waje. Mami ce tabi bayan ta.
Mami ta ce,
"Sunyi waje."
Kasa ta nufa ta sauka daga benen. Tana zuwa har Buhari ya shigar dashi.
Da sauri ta shiga mota ta zauna kusa da Dady. Tana rike hannun sa.
Mami ce ta shiga ta zauna. Asma'u kuwa ganin halin da Dady ya shiga duk sai ta fita daga hayacin ta.
Kuka take tana cewa,
"Sannu Dady. Sannu"
Duk bayan minti biyu sai ta kara ce masa sannu.
Pls don't forget to press on start to vote.
*INDABAWA*
[1/18, 14:21] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*
Dedicated to *My Lovelly Momy*
*Momy nah a koda yaushe addu'a ta bazata taba karewa gareki ba.*
*Kece komai nawa. Ina nufin komai fa.*
*Masoya a ko da yaushe kune silar dariya ta. Bama in ina karanta comment din ku.*
*To Alhamdulilah Da soyayyar ku a gareni. Allah ubangiji ya bar ni da ku.*
*Gaskiya ina jin dadin yadda kuke bibiyar labarin nan.*
*Masoyan Aslam*
*Masoyan Sabir*
Kuna ina ne?
*136-140*
An Kar6o Daga *Anas (ra)*, Lallai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *“Idan Aka Gabato da Abincin Dare, to Ku Fara Dashi Kafin Ku Sallaci Magariba”*. (Bukhari da Muslim)_
Suna zuwa asibiti aka amshe shi. Sun jima akan sa dan har akai sallar asuba.
Sallah Asma'u tayi ta jima tana wa Dady Addu'ar Allah ya bashi lafiya.
Dady kuwa ganin jikin sa sai wasiya yake bayar wa yana cewa,
"A kira masa *Husnah* ku kira min matata da 'da na da Auta tah *Husnah* "
Da sauri Dr ya karasa ya kira su. Asma'u na shiga da gudu ta karasa wajen Dady ta rike hannun Dady tana jijigawa tana cewa
"Dady gani. Dady ga *Husnah* ka."
Dady dake kwance yana fitar da numfashi sama sama, ya kalli Mami da Buhari. Ya ce
"Amina Allah miki albarka. Allah ya baki aljanna madauka. Buhari kai ma Allah maka albarka Allah ya saka a gidan aljanna Allah baka mace ta gari."
Ya karasa maganar da kyar. Cikin sa ya kara rikewa ya kalli Asma'u ya sakar mata murmushi ya ce,
"Ga *Asma'u Husnah* nan ku kula da ita. Ita ce, yarinyar karama kar ku bar ta tai kuka. Amina Allah miki Albarka. *Husnah* Allah ya miki albarka. Allah baki zuri'a ta gari Allah ya saki a Aljanna."
Hannun Buhari ya kamo tare da na Mami. Kallon Asma'u yayi ya sakar mata murmushi.
Kalamar shada ya dinga fadi a hankali. Mami ita take tayasa amsawa. Su Asma'u da Buhari kuwa gaba daya sun rikice da kuka.
Can Dady ya saki hannun su idon sa ya lumshe, cikin firgice, Mami ta kwadawa Dr kira.
Dr ne ya shigo ya duba shi. Kai ya girgiza kawai.
Kallon sa Asma'u tayi ta ce,
"Dr ya jikin nashi ne?"
Kallon su Dr yayi ya ce,
"Sai dai kuyi hakuri Allah ya amshi rayuwar sa."
Asma'u dake tsaye wata juwa taji tana dibar ta. Daga nan duhu ya rufe mata idon ta.
Zubewa tayi a kasa. Mami ma faduwar tayi. Buhari kuwa ya rasa ya za yi.
Da sauri Nurse suka yi wani Daki aka kai Mami da Asma'u aka kwantar da ita. Suna kokarin ceto rayuwar su.
Buhari kuma ya buga waya ya fadawa Uncle Abubakar kanin Dady da uncle ilyasu da kanwar sa.
Sai Momyn Aslam da sauran yan uwa. Cikin minti kadan gida ya cika da jama'a.
Mami da Asma'u kuwa suna Asibiti. Momyn Aslam a lokacin suka taho a jirgi.
Karfe sha biyu aka sa za ayi jana'idar Daddy.
Momyn Aslam na zuwa, ta zarce asibiti. tana zuwa Mami ta farka.
Kuka Mami ta saka. Momy ta kama ta ta ce,
"Haba Amina, me yasa zaki kuka ki sani kukan ki ba abinda zai karawa Abban Asma'u. Addu'a ce kadai zaki taya shi da ita Allah yai masa rahama.dan Allah ki daure kar ki bari ki saba da zubar masa da hawaye. Allahn da ya bamu shi yafi mu son shi dan haka hakuri zamuyi muna taya shi da addu'a."
Sosai Momy tayiwa Mami nasiha mai ratsa jiki.
Kukan ta daina amman fa zuciyar ta kamar zata fashe.
Damuwa karara akan fuskar ta. Da haka suka mike suka yi gadon da Asma'u take.
Tana kwance har lokacin bata san inda kanta yake ba.
Momy ce ta zauna da ita aka tafi da Mami gida dan ganawa da gawar Dady.
Aslam kuwa da suka taho Dadyn sa bai sanar da shi halin da Asma'u ke ciki ba.
Dan haka duk yadda yaso ya ganta ya ga a halin da take ciki bai samu ba.
Momyn sa ya kira ya ke tambayar ta ina Asma'u dan Allah ta fada masa halin da take ciki.
Dan yasan a wannan lokacin Asma'u zata fi kowa jin mutuwar Dady.
Duba da irin shakuwar dake tsakanin ta da shi.
Komai in zatayi Dady ko abu zata yi tace Dady.
Tafi yin shawara dashi akan da Mami. shiyasa yake son yasan a halin da take ciki.
Haka ta ce masa tana asibiti in ta dawo zata duba masa halin da take ciki. Amman ya kwantar da hankalin sa tana lafiya.
Suna cikin waya aka kawo Mami gida. Da sauri ya karasa gun Mami.
Duk tausayin ta ya kama shi. Shi ya kamata suka shiga cikin dakin da aka kwantar da Dady.
Addu'a Mami tai masa sosai, sannan aka zo aka dauki gawar ta shi.
Duk yadda taso kar tayi kuka sai da hawaye ya zubo a idon ta.
Kanwar Dady ita tazo ta shiga ciki da ita.