← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 61

Sashe 31

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Momy ta jinjina ta ce,
"Kinga kar ki damu. Kin san ance jinin ki ya hau ki rage tunanii zan kira sa naji kinji. Ki kwantar da hankali ki."

Kai ta gyada ta mike ta hau gado ta kwanta.

Zuciyar ta in banda bugawa ba abinda take.

Gaskiya tana son Yaa Aslam bata san inda zata sa kanta ba.

Tana kwance Mami ta shigo mata da kunun da ta dama mata.

Amsa tayi ta dan sha sannan ta mika mata.

Kwanciyya ta koma tayi sannan ta dasa daga inda ta tsayaa a tunanin ta.

Washe gari Mami da Momy suna zaune a falo. Momy ta dubi Mami ta ce,
"Amina wata matsala ce ta kawo nifa."

Kallonta Momy tayi ta ce,
"Wacce irin matsala?"

Ajiyar zuciya Momy ta sauke ta ce,
"Akan Aslam da Asma'u ne."

Kallon ta Mami tayi ba tare da ta gani me take fadi ba.

Momy ce ta gyara zama ta fada mata duk abinda yake faruwa.

Kai Mami ta jinjina tana mamaki anya Aslam ne kuwa.

Mami ce ta ce,
"Kinga Anty kuyi masa yadda yake so, Allah yasa haka ne mafi alheri ita Asma'u sai ta hakura."

Kallon ta Momy ta yi ta ce,
"Wai ke Amina meyasa ko da yaushe kike son nuna min banbanci tsakanin ya'yan nan namu ne, kina zaton in nice Asma'u tayi ba dai dai ba zan barta ne, amman ke sai ki ce Allah yasa haka ne yafi alheri. Ai nasan daman da wannan addu'a."

Mami dai shiru tayi fana sauraron fadam da Momy ke mata.

Sai da ta gama sannan ta ce,
"Kiyi hakuri Anty amman ni ba abinda kike nufi bane, nasan tsakanin Aslam da Asma'u ba mai shiga ne, bansani ba ko wani abun ya shiga tsakanin ne ko sun samu sabani."

Kai Momy ta gyada, ta ce,
"Ki tuntubar min Asma'u "

Mami ta ce,
"Toh!"

Buhari da tin da Momy ta fara bawa Mami batun yana jin su har yanzu yaji jikin sa yayi mugun sanyi.

Garden yayi dan bazai iya shiga ciki ba a halin da yake ciki.

Yana zuwa ya hango Asma'u kwance a kan wata kujera. Ta kudundune jikina ta.

Idon ta a rufe kamar mai bacci. Juyawa yayi zai bar wajen ta mike tana kiran sunan sa.

Juyowa yayi yana sakar mata murmushi, ya ce,
"Ai na zata bacci kike."

Kai ta girgiza masa ta ce,
"Ina kwance ne kawai."

Dawowa yayi ya zauna gefen ta yana kallon ta cikin tausayawa dan yanzu da ya kara jin maganganun su Momy sai ya kara tausayawa Asma'u.

Kallon ta yayi dan ya bugi cikin ta ya ce,
"Ina Yaa Aslam kuwa? Kwana biyu bamuyi waya ba."

Murmushi ta dan ta ce,
"Yana lafiya."

Kallon mamakki ya bita da shi. duk yadda yaso ya bugi cikin ta bata fada masa komai ba.

Haka ya hakura ya barta sai kallon tausayi da yake mata dan yasan Asma'u ta ji Aslam zai aure ba karamin damuwa zatai ba.

Yasan zata iya shiga wani hali. To shi da me zai taimakawa kanwar sa kar ta shiga damuwa.

Ya jima yana tunanin nan kafin ya mike ya koma cikin gida.

Asma'u kuwa har lokacin number Aslam take ya kira amman No Answer.

Aslam kuwa duk kiran da take masa yana gani dauka ne yake gagarar sa. Dan shima ba karamin sun dauka yake ba amman sai ya kasa.

Yanzu kuwa kullum yana tare da Prety daga sune can sai sune can.

Duk abinda ta lissafa tana so ya siya mata.

Buhari ne kwance ya kasa gaskata abinda yaji su Mami na fadi.

Mikewa yai zaune ya janyo wayar sa. Number Aslam ya kira.

Bugu daya ya dauka. Gaisawa sukai kamar yadda suka saba sai dai bai tambaye sa Asma'u ba kamar yadda ya saba.

Buhari ne ya ce,
"Yaa Aslam daman Asma'u ce ba lafiya naji ba ka kira ya take bane."

Shiru Aslam yayi na dan wani lokaci kafin ya ce,
"Ai mata sannu. Yanzu ina wani aiki ne amman in na samu lokaci zan zo. kaji labarin aure na nan da sati biyu ko?"

Dif Buhari yayi jin abinda Aslam ya fada. Kai ya girgiza sannan ya ce,
"Au bikin naku har an matso dashi amman ban sani ba."

"A'ah ba wannan ba wata xan aura anan."

"Wata zaka aura!"
Buhari ya fada da mamaki sosai. Aslam ne ya katse masa tunani ya ce,
"Buhari kai ne dan uwana wanda kake kani a guna. Wallahi bansan me yake damuna ba. Lokaci daya naji ina son Pretty kuma ni ba son Asma'u ne bana yi ba kawai bansan me yake damuna ba."

Sosai Aslam ya bawa Buhari tausayi. Tabbas yana tausayawa Aslam amman yafi tausayawa Asma'u ita da take haukan son sa.

Shiru yayi. Aslam ya ce,
"Dan uwana dan Allah kada hakan ya zamo sanadin yanke zumuncin mu ka fuskance ni. Momy da Dady sun kasa fahimta ta."

Take Buhari ya gane Aslam ba acikin haiyacin sa yake ba.

Shiru yayi kafin ya ce,
"Ba komai Allah tabbatar da alherin sa."

Wayar ya kashe yai shiru. Sai ga hawaye na zubowa daga idon Buhari.

Tabbas dole yasan abinda zai ya kubutar da Asma'u daga damuwa.

To tayaya dole ta damu in har Aslam baya kiran ta. Kuma dole ta damu in bata ganshi a wajen ta na kwanaki ba.

Ya jima yana saka da warwarar yadda zai bullowa alamarin har da sai da ya samu mafita sannan ya samu sauki a ransa.

Zainab ya fadawa duk halin da suke ciki sosai ta tausaywa kawar tata.

Asma'u ce zaune a falon Dady ta zuba tagumi, Mami ce ta shiga ta same ta.

Zama tayi a gefen ta, ta ce,
"Asma'u jikin ne, Asma'u dan Allah ki rage damuwa kinji."

Kai Asma'u ta daga ta zare hannun ta da tai tagumi dashi.

Kallom Mami tayi ta sakar mata murmushin da bai kai zuciya ba.

Mami ta ce,
"Wai kuwa kin fadawa Aslam baki da lafiya.?"

Shiru Asma'u ta danyi ta ce a ranta.
"To ita yanzu wa zata na fadawa damuwar ta in ba Mami ba. Tinda ba Dady dole Mami ta zama kawar shawarr ta."

Kallon Mami Tayi idon ta sun kawo da kwalla ta ce,
"Mami bansan me yake damun Yaa Aslam ba. Kwata kwata baya kira na ko na kira sa baya dagawa. Bansan laifin da nai masa har yake hukunta ni haka ba. Mami wallahi ko bacci bana iya wa saboda ya sabar min shine mutum na karshe da nake magana dashi na kwanta bacci."

Sai ta fashe da kuka. Sosai Mami ta tausayawa yar ta ta. Lallashin ta tayi sannan ta ce
"Kiyi hakuri ki dage da addu'a kinsan haka na faru amman addu'a ita zata tsairatar da ke."

Kai ta daga ta ce,
"Mami bazan iya rayuwa ba Yaa Aslam ba. Yaa Aslam ya sabar min da son sa yadda bazan iya cigaba ba tare da shi ba."

Janta jikinta Mami ta yi ta ce,
"Ki daina fadar haka, ki sa a ranki ko da Aslam ko ba Aslam zaki rayuwa. Kina addu'a Allah zaba miki abinda yafi alheri a rayuwar ki."

Sosai Mami ta kwantar wa da Asma'u hankali.

Suna Zaune Buhari ya shigo. Ganin idanun Asma'u da hawaye ya tada masa da hankali.

Zama yayi a gefen ta ya ce,
"Hussyn Dady menene kuma?"

Jikin sa ta fada ta fashe da kuka mikewa Mami tayi ta fita.

Asma'u ce, ta ce,
"Yaa Buhari. Yaa Aslam ne, bansan me nai masa ba."

Ta fashe da kuka. Lallashin ta ya dinga yi. Ya ce,
"Baby nah ki kwantar da hankalin ki. Ba abinda kikai masa. Kuma insha Allahu Aslam naki ne, kinji."

Kai ta daga ta ce,
"Yaya da Gaske."

Kai ya daga mata ya ce,
"Kinga ki taso muje nai miki visa ki tafi saudiya. Daga nan ki yo addu'a tinda kinga kun gama karatu. in kin dawo a bude asibiti a fara aiki. Daga nan zzan zo muje wasu kasashen kar ki damu kinji."

Kai ta daga masa. Ta mike ta wanke fuska suka fita.

Mami kuwa tana fita itama sai da ta dan zubar da hawayen

Tana tausaywa 'yar ta. Tasan 'yar ta bata saba da son kowa ba. Da Aslam ta bude ido ta san rayuwa gashi yanzu wani al amari na shirin faruwa.

Dakin da Momy ta ke ta shiga jiki a sanyaye.

Kallon ta Momy tayi ta ce,
"Ya kukai da ita."

"Uhmm Anty ni a gani na kawai kibar Aslam ya aure wacce yake so. In yaso daga baya in Allah yayi Asma'u matar sa ce sai suyi auren. Yanzu dai ita ta ce, ba abinda ya hada su kawai dai baya kiran ta baya daukar number ta ne."

"Inna illahi wainna illahir rajiun!"
Momy ta dinga nanatawa.

"Shiken Amina tinda haka kika ga yafi shikenan. Zan je zanyi iya bakin kokari na a daura auren nan da Asma'u amman ni ba yawu na a auren Aslam da wata."

"A'ah Anty kada kiyi haka, kada ki so ma hakan ba kyau. Ki sa masa albarka kawai baki san mene alheri a rayuwar mu ba. In kika ce haka sai kiga wani abu mara dadi ya faru."

Shiru Momy tayi ta ce,
"Shiknan dole na tafi gida yau din man."

"A'ah Anty dan Allah ki bari gobe. Kuma dan Allah kada ki tada maganar nan."

Shiru Momy tayi kawai.

Buhari kuwa da suka dawo gidan su Zainab ya biya da Asma'u duk dan ta samu farin ciki.

Duk da jikin ta ba kwari. Ita kanta fitar da sukai ba karamin debe mata kewa tayi ba.

Dan ya dan samu sanyi a ranta duk da da tayi shiru abin yake fado mata a rai.

Basu dawo gida ba sai dare da siyayyar da Yaa Buhari yai mata.

Kayan ta ta hau hadawa wanda za tai tafiya dasu.

Sai da ta gama ta kwanta. Tana kwance nan sai tunanin Yaa Aslan ya fado mata

Na yadda yake jaddada mata son sa da yadda yake kwantar mata da hankali.

Kuka ta fashe da shi ta jima tana kuka sannan ta mike tayo alwala sanna ta zo ta tada sallah,

Kwana tayi tana sallah tana rokar Allah ya shige mata cikin al amuransa.
Chapter 31 · 0% Book details