Sashe 8
Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Bari na karbo maka lemo."
Ta mike.
Kamo hannun ta yayi ya ce,
"A'ah yanzu na gama cin abinci ga naku can ma a mota."
Murmushi tayi,
"Kai Yayah."
"Eh!"
"Zakaje gida ne."
"A'ah! Daga nan zanyi gida."
"Ok."
"Ina sonki Baby nah."
Murmushi tayi ta dukar da kanta.
"Baby kunyar nan taki tana dada miki kyau."
Kai ta kuma dukar wa.
"Bari na wuce kar nayi dare. Tinda naga Baby nah ai nagodewa Allah."
Murmushi tayi.
"To nagode."
"Nike da godiya Baby nah "
Suka mike suka nufi motar. Dai dai karasowar Sir Sabir zai dauki motar sa.
Kallon juna suka yi, ya shige motar sa.
"Waye wancan."
Juyawa tayi,
"Sir Sabir wani lecturern mune."
"Kuna magana ne?"
Ya tambaya fuska a dan hade
Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah!"
"Ina zee kuwa?"
Ya tambaya.
Kallon gun da suke tayi ta ce,
"Gata can bari na kira ta."
Ta tafi wajen su Zee,
"Zee kizo inji Ya Aslam!"
Ta fada tana kamo hannun ta.
Wajen su suka karasa.
"A bamu waje ko?"
Ya fada yana kallon *Asma'u* baki ta tabe ta bar wajen. Dariya yayi, yace,
" *Husnah* rigima."
Sannan ya dawo da hankalin sa kan Zee.
Bayan sun gaisa yake bata amanar *Asma'u* sannan sukayi sallama.
Wajen *Asma'u* yayi,
"Haba Baby na yanzu da Yayan naki kike fushi. Kiyi hakuri kinji."
Shiru tayi masa. Murmushi yayi, ya koma gaban ta,
"Ko so kike na rumgume ki na rarashe ki."
Ido ta zaro, tana girgiza kai. Ya jawo ta. Saurin janye hannu ta tayi. Tayi wajen motar sa.
Bayan ta ya bi, yana Murmushi ya shiga motar. Leda ya miko mata.
"Gashi ni zan tafi."
Amsa tayi ta ce,
"To Allah kiyaye hanya."
"Ameen nagode!"
Ta rufe masa kofar tana daga masa hannu. Tare da murmushi akan fuskar ta.
Sai da taga bata hango shi sannan ta koma wajen kawayen ta.
Ido suka bita dashi,
" *Asma'u* waye wancan."
Hafsat ta tambaya fuskar ta a hade. Kallon ta *Asma'u* tayi sannan ta dauke kai.
Zainab ce, tace,
"Yayan ta ne."
Khadija tace,
"Amman fa ya hadu. Wai meyasa ke kike baka ne."
Amina ce, tace,
"To ko zaki canja mata halitar ta ne,"
Harara ta Khadija tayi,
"Ni na tambaye ta, ta wani haden rai da dauke kai."
Hafsat ta fada, Mikewa *Asma'u* tayi ta kalle ta.
"kin tambayen an amsa miki ba shikenan ba. ko kin manta wa kike tambaya ne. *Asma'u* da batai miki komai bace kika dau gabar duniya kika daura mata, kin manta in nayi miki magana ko kallo na bakya yi shine kuma yanzu zaki zo kina tambaya ta. Kuma cikin isa sai kace ni yar kice. Ke bama zan fada ba. Kiyi abinda xakiyi."
Ta fada tana kama hannu Zainab suka shige hall.
"Haba *Asma'u* me kenan kika yi ke da bakya fada."
Kuka *Asma'u* ta fashe dashi,
"Ya zanyi kema kinsan dai Hafsat ta kaini bango ne. Duk makarantan nan ba wacce ta tsana kamar ni tin ina dauke kai sannan yanzu tazo tana min gadara. Akan abinda be kai ya kawo ba."
"Ya isah toh mene na kukan!"
Ta fada tana jan ta jikin ta tana rarashin ta.
Ta jima tana addu'a cikin ranta sannan taji sanyi. Kan ta, ta dago ta kalli Zainab.
"Nagode besty."
"Ba komai."
kasa ta duka zata dauki jakar ta. Sai a lokacin ta tuna da abinda Ya Aslam ya kawo musu.
Murmushi tayi ta dauki ledar tana dubawa. Takeaway yayi musu, guda uku sai dayar ledar kuma kaji ne guda biyu a ciki da lemuka na jarka.
Raba su tayi gida biyu ta mikawa Zainab.
"Besty dan Allah mikawa su Amina kayan nan."
Karba tayi tayi waje.
Su *Asma"u* na barin wajen, su Amina suka farayiwa Hafsat fada.
"Haba Hafsat, meyasa kike haka, yarinya bata tsare miki komai ba amman kin tsane ta gaskiya ki daina haka."
Hafsa ta ce,
"Tayaya zakice bata taren komai ba, yarinyar da ta shigo ta same ni sannan tazo tafi ni kokari shine bata fini komai ba."
Khadija ta ce,
"Yo dan tafiki kokari, ai kema dagewa ya kamata kiyi ba ki tsane ta ba."
Khadija ta fada tana bata fuska.
"To ku dake ni mana."
Hafsat ta fada.
"A'ah A'ah ba abin duka anan. Sai dai muyi miki addu'a Allah ganar dake."
Dai dai nan wata daliba da tayi kaurin suna a makarantar ta karaso gun su
"Hae Babies."
"Hae!"
Gefen Hafsat ta zauna.
"Dan Allah wa naga ta tsaya da yaron nan da yazo yanzu. Dan bayan ta na gani banga gaban ta ba."
"Oh ai *Asma'u* Suleiman ce."
Hafsat ta bata amsa.
"Wane department take,"
Suka fada mata tai musu godiya ta bar wajen
Zainab na fitowa Munasha na shiga Hall wajen *Asma'u* ta dosa kai tsaye,
Toh masoya *Asma'u Husnah* naga sakon ku na gode, ba ma yan threestart u always love my story tnc Allah bar kauna.
Hhhh yan facebook comment naku na min dadi ngd
Afternoon yan uwa
Don't forget to vote pls
*INDABAWA*
[1/18, 14:09] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
ASMA'U HUSNAH
BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*
🌐 *HAJWO* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Na gaida ku, yan 'kungiyar mu, Allah kara hade kan mu tare da dada mana hakuri da juriya da al umma.
Hajiya Nafisa na gaida ki. Allah kara daukaka Ameen.
Mamanah.
*41-45*
Dedicated to *My sweet Mum*
Allah kara miki imani da daukaka.
An Ruwaito Cikin Littafin Ibn Sinni, Daga *Buraidah (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: "Duk Wanda Yayi Wannan Addu'ar a Yayin da ya Wayi Gari da Kuma Lokacin da Yayi Yammaci, *{Rrabbiyallahu Tawakkaltu Alaihi La'ilaha Illah Huwa Alaihi Tawakkaltu wa Huwa Rabbul Arshil Azeeem, Lã'ilaha Illallahu Aliyul Azeem, Mãsha Allahu Kana, Wama Lam Yasha Lam Yakun, A'alamu Annallaha Ala Kulli Shai'in Qadeer, Wa Annallaha Qad Ahad'a Bi Kulli Shai'in Ilma},*
Sannan Ya Mutu Zai Shiga Aljanna
Tana karasawa wajen, tace,
"Hae Bae!"
Murmushi *Asma'u* tayi.
"Sannu!"
"Yauwah! Uhmm daman nace wanda yazo din nan sunan sa nake son ji."
Murmushi *Asma'u* tayi,
"Ya Aslam Sunan sa."
"Ok toh nagode."
Ta fada tana mikewa dai dai karasowar Zainab.
Kallo Zainab tabi ta dashi, ta karasa gun *Asma'u*
Fuskar ta a daure take tambayar ta.
"Me ya hada ki da waccan?"
Bin ta *Asma'u* tayi da kallo.
"Tambayata tayi."
"Akan wa?"
"Ya Aslam mana."
" *Asma'u* kin san wace wannan kuwa?"
ido Asma'u ta bude alamar tsoro. Ta girgiza kai ta ce,
"A'ah wace?"
"Toh! Ita ce wacce ake kira Munasha! Kinsan dai Munasha ita ce wacce ba abinda bata aikatawa, ki kula da ita dai."
Ido *Asma'u* ta zaro, saboda tsoro.
"Wallahi ban sani ba."
"Ki dai kula."
"Insha Allahu."
Daga nan suka fara cin abinci, suna gamawa aka fara taruwa a hall din. Gaba suka koma, sai ga lecturer su nan.
Sai karfe hudu ya fita, sallah sukayi suka shige library dan yin karatu.
"Sis Koyan lecture da Sir Sabir yayi muku yau."
Asma'u ta fadawa zee
"Toh!"
Ta fada tana koya mata, sosai take ganewa. Sai karfe biyar da rabi sannan suka fito, lokacin har anzo dibar su.
Sallama sukayi, suka wuce.
Tana komawa gida ta tadda Mamin ta a falo.
Kanta ta haye,
"Mami na ya gida?"
"Lafiya Alhamdulilah, Ya makarantar?"
"Lafiya Mami."
"Tashi kije kici abinci nasan baki ci komai ba."
"Lah Mami naci Abinci. Mami kinga yau Ya Aslam ma yazo makarantar mu."
Ta fada tana murmushi, fuska Mami ta dan hade, ta ce
"Wajen wa yaje?"
"Wucewa zai yi ya biyo."
Asma'u ta bata amsa.
" *Asma'u* ban yadda ki kara bari ya same ki a makaranta ba, ke bashi ba koma waye kar ki kuma haduwa da wani namiji a makaranta."
Fuska ta marairaice,
"Mami dan Allah kiyi hakuri, bazan kara ba."
"Ba komai baki bata min ba. Amman kika kuma shi zai batan rai."
"Kiyi hakuri insha Allahu bazan kuma ba."
"Kar ki damu tashi kije ki rage kayan jikin ki."
"Kin hakura toh!"
asma'u ta tambayi Mami.
Murmushi Mami tayi,
" *Asma'u* kenan. Na hakura, kinji."
Murmushi tayi ta tashi ta haye sama.
Murmushi Mami ta kuma yi, tana girgiza kai, *Asma'u* sam bata son bacin ran iyayen ta ko ya tayi musu laifi zata daga hankalin ta, har sai taga sun hakura.
Ita kanta Mami tasan ba wani abu bane dan Aslam yaje makarantar ba, amman in har bata tsawa tar ba nan gaba zata iya bawa kowa damar yin haka.
kuma hakan baya da kyau.
Tana shiga dakin ta ta fara lalubar number sa. Bugu daya ya daga.
"Yayanah ya hanya?"
"Hanya lafiya Alhamdulilah na kusa karasawa."
"Kai Yaya gudu kake yi ko?"
"So nake nayi sauri na karasa."
"Dan Allah ka rage gudun nan."
"To shikenan sai anjima."
"Aha! Ka kula da kan ka."
"Insha Allah!"
Ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya ne. Bandaki ta shiga tayi wanka sannan ta fito.
Kwalliya tayi me kyau, ta saka riga da siket yan kanti ruwan madara da dark brown.
Brown (Ruwan kasa) din hijab ta dauka ta saka sanna ta dauko jakar ta tana duba wa.
Tana gama dubawa ta mike ta hau kan sallaya, tana jan carbi. Kiran sallah da taji ya sanya ta mike ta tada sallah.
Tana idar wa ta janyo Alkur'anin ta, tana karantawa. sai da akayi sallah isha'i sannan ta mike tayo.
Tayi Isha'i sannan, ta mike tayi shafa'i da wuturi. Tana idar wa ta fara yin addu'a.
Wayar tace tayi kara dubawa tayi. Sakon Ya Aslam ne ya shigo.
*Baby nah, na sauka lafiya. Zan kira ki anjima.*
Murmushi tayi, ta mike tayi waje.
Tinda ya gansu a tsaye ya kasa sukuni sam ya kasa samun nustsuwa, waye wannan da yazo gun ta, sam shi abin damun sa yake.
Haka ranar ya gama, aiki duk jikin sa babu dadi, ransa a bace dan abin be masa dadi ba.
Haka ya tashi a aiki ya wuce gida.
Mamah na gani sa taji hankalin ta ya tashi, dan duk ya fita a haiyacin sa.
Gaishe ta yayi, ta amsa.
"Sabir lafiya kuwa?"
"Lafiya lou Mamah."
Kallon sa tayi, tana me girgixa kan ta.
"Wai Sabir mecece ni a gunka."
Kan sa ya dago, yana kallon ta.
"Eh! Tambayar ka nayi,"
"Mamah Mahaifiya tace ke."
"Ka tabbata?."
"Na tabbata Mamah."