← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 61

Sashe 36

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi kyau sosai duk wacce ta kalle shi sai ta so shi.

Har ya zauna bata san da shigowar sa ba. Ganin bata san ya shigo ba yasa ya mike ya matsa kusa da bencin ta.

Dan bubbugaga table din ta take, yayi tai saurin dagowa idon ta da hawaye.

Kallon ta ya tsaya yi. Ran sa abace. Ganin sa yasa ta fara kokarin goge hawayen ta.

Zama yayi ya ce,
" *Husnah* ke fa bakya ji ko? Wai bakya son lafiyar ki ne, kita sa damuwa a ranki. To in ba ki damu da rayuwar ki ba ni na damu da ita. In bakya son cigaba da rayuwa ki ina son kici gaba da ita dan wani ne farin cikin ki ni kece farin ciki na. kece farin ciki na. Kece buri na."

Sai kuma yai shiru. Kallon da take da mamaki a fuskar ta.

Kai ya gyada mata ya ce,
"Eh! Wallahi *Husnah* tin san da na fara ganin ki naji ina son ki. Son ki tin a lokacin ya shige ni. Na rasa ta yadda zan sanar dake ne. Ki bani dama *Husnah* zan yaye miki dukkan damuwar ki zan maye miki gurbin Aslam da yaddar Allah."

Kai ta girgiza ta ce,
"Sir baza ka iya ba. Kasan waye Yaa Aslam a guna kuwa. Duk da abinda yai min jin sa nake har yanzu yana zuciya ta. Jin sa nake a rai na. Kasan tin ban san kai na ba Yaa Aslam ke so na. Da son sa na girma da son sa na san wace ni. Da shi kadai na taba soyayya. Sir ko ban auri Yaa Aslam ba to nasan bazan kara soyayya ba. Bazan taba daina son sa ba. Son sa ya riga ya zama jinin jiki na raba ni da shi bazai taba yiyuwa ba. Kayi hakuri nagode da soyayyar ka."

Ta mike tana goge hawayen ta tana gogewa yana kara zubo mata. 

Jakar ta, ta dauka ta fita daga office din da sauri.

Yanzu ita tasan  soyayyar maso wani take.

Tinda ita take son sa shi kuma baya son ta.

A haka ta shiga motar ta, tayar da motar tayi ta nufi gidan su zee dan yin rabon kati da zasu fara.

Tana shiga ta gaida Maman Zainab sannan ta shige cikin dakin ta.

Tana kwance tana waya da Yaa Buhari sai soyayya suke yi.

Asma'u kuwa na zaune abin duniya ya isheta.

Jin hirar da Zainab take a waya shi yasa ta fara zubar da hawaye.

Wacce soyayya ce bata samu ba. Amman yanzu ita ce a halin soyayya ta juya mata baya.

Tana son Yaa Aslam baza ta taba daina son sa ba.

Dan addu'a take Allah ya cire mata son sa amman sai son sa dake daduwa.

Bata san lokacin da Zainab ta gama wayar har ta zo gaban ta ba.

Sai da ta dafa ta sannan ta dago kanta. Damuwa fal a fuskar Zainab ta ce
"Haba Asmmy mene kuma?"

Hawayen ta goge ta ce,
"Kar ki damu. Ina kati nan. Ina son zan kaiwa Maimuna yau dai naje gidan su."

Kai Zainab ta gyada mata ta ce
"Karfe biyu ai dai kya yi sallah kici abinci sai muje ko?"

Mikewa tayi ta shiga bandakin dake cikin dakin.

Alwala tayo tazo tai sallah ta ci abinci sannan ta mike.

Mikewa Zainab tayi suka fita. Duk inda suka san da yan class dinsu sai da suka kai musu.

A hanya Asma'u ta ce,
"Wato baza ki zo ki karbi aiki ba sai kinyi aure ko?"

Kai ta gyada mata ta ce,
"Ki bari naje na gama cin amarci na tukkuna sai na fara. Yanzu haka kawai a ban hutun sati biyu mai naci."

Kwafa Asma'u tayi ta ce,
"In ma zan baki ba."

Dariya Zainab tayi ta ce,
"Oh sai kin bani. kinsan zan iya tafiya ta ai ba tare da an ban ba ko My husband yazo ya amsar min. Ko Mami nah ta ce na je na huta."

Duka Asma'u ta kai mata ya ce,
"Wallahi yarinyar nan kin min wayo."

Zainab ta ce,
"Wace yarinyar? Anty dai."
Suka sa dariya.

Daga nan suka wuce gidan su Maimuna.

*INDABAWA*
[1/18, 14:29] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR

  *Asma'u Husnah*

*part 2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*

Dedicated to *My Lovelly Momy*

*26-30*

Sabir kuwa tinda Asma'u ta fita ta bar shi da tunani kala kala.

Allah ya sani yana son Asma'u kuma yana son ya aure ta.

Mikewa yayi ya rufe mata office din shima ya fita ya tafi gun Buhari suna shirye shiryen biki.

Washe gari da safe Buhari ya dau hanyar Abuja a mota

Asma'u yau ma daga Wajen aiki ta wuce Gidan su Zainab.

Yaa Buhari ya isa Abuja lafiya. Momy sai nan nan take da shi.

Ta cika masa gaban sa da kayan abinci kala kala.

Suna zaune suna hirar su Mami. Tana kara tambayar sa ina 'yar ta.

Da yake haka take kiran Asma'u. Buhari ya ce,
"Tana nan ai su Asma'u an zama busy daga wajen aiki sai shirye shiryen biki.
Dan cewa tayi dama sai bayan biki aka bude. Damuwa dai ba laifi ta rage ta duk da tana cikin ta mu take nunawa ba ta cikin ta."

Mami ta girgiza kai ta ce,
"Allah sarki. Allah kawo miji na gari. Ni ina tunanin ma na samo mata miji da kaina dan na wuce haushin da aka bamu."

Dariya Buhari yayi ya ce,
"Haba Momy."

Momy ta ce,
"Wallahi."

Buhari ya ce,
"Ai kam tinda nazo naje na dubo Yaa Aslam da amarya."

Shiru Momy tayi kawai. Momy ta ce,
"To ni me kake so nai maka ne."

"Duk abinda Momy tayi nagode."
"To ai shikenan. duk abinda ka gani ka godewa Allah tinda kaki zaba."

Dariya Buhari yayi. Momy ta ce,
"Kaje ka huta ko?"

Kai ya dan sosa ya ce,
"Aah tukkuna dai zanje gidan wani aboki na daga nan zani gidan Yaa Aslam,"

Momy ta ce,
"Toh!"

Momy ya tambaya address din Aslam sannan ya fice.

Yana fita yayi gidan abokin sa anan duk ya bashi katin nan ya rabawa sauran abokan su.

Daga nan yayi gidan Aslam. Gida ne mai kyau ya hadu, yana zuwa ya ce,
"Oh ikon Allah da tini Asmmy na ce a gidan Yaa Aslam. ikon Allah ance matar mutum kabarin sa ko nan gaba zasuyi aure waya sani sai Allah."

Yana parking ya kira number Aslam. Aslam na dagawa ya suka gaisa kamar yadda suka ssaba.

Buhari ya ce,
"Yaa Aslam gani a compound din gidan ka."

Aslam da sauri ya mike ya ce,
"Da gaske."

Ya ce,
"Kazo ka gani."

Da sauri ya katse wayar ya fito. Yana ganin Buhari ya rumgume shi.

Dariya ya saki ya ce,
"Amman naji dadi mu shiga daga ciki."

Suka shiga. A falo suka zauna. Aslam shi ya kawo masa ruwa da lemo. Sanna suka zauna hira yana tambayar sa ya Mami da Mutan gidan.

Dan sunan Asma'u ma ya kasa ambata. Duk da a cikin ransa yana son ya tambayi Ya Asma'u take amman ya kasa.

Buhari ganin bai ga Matar Aslam ba ya ,
"Yaa Aslam Ina Anty nawa."

Kai Aslam ya dan sosa ya ce,
"Ta fita unguwa ne."

Buhari ne ya mikawa Aslam katin bikin sa. Amsa Aslam yayi yana washe baki yana ta sanya albarka.

Har magariba suna tare dan a gidan sukai sallah.

Buhari ya tashi zai tafi kenan sai ga Pretty ta shigo. Cikin shigar riga da wando, kayan sun matse ta sai wani mayafi da ta yafa abin ba kyan gani.

Buhari da farko bai gane wace ba sai da ya ga Aslam ya ce,
"Madam! Barka da zuwa."

Kallon su tayi a yatsine ta watsar ba tare da ta ce, Uffan ba ta wuce ta kwanta akan kujera tana kwallawa daya daga cikin yan aikin ta kira.

Da sauri ta karaso. Ta bata umarni ta dauko mata lemo.

Mikewa tayi da sauri ta miko mata ta dawo.

Buhari kuwa ya baki ya saka yana kallon ta.

Kallon su tayi a yatsine ta ce,
"Ina zaka ne?"

Kai Aslam ya girgiza ya ce,
"Raka shi zan yi."

Tsaki Buhari ya saki yayi waje. Da sauri Aslam ya biyo shi a baya.

Yana karasawa ya shiga motar sa. Aslam ne ya leko ya ce,
"To bro nagode a gaida gida da su Mami. Sai munzo bikin ko?"

Kai Buhari ya daga ya ce,
"Allah kawo ku."

Yai gaba. A ransa yana mamakin wacce irin mata Aslam ya aura.

Anya kuwa haka ta bar shi. Da wannan tunani ya karasa gida.

Yana zuwa Momy ya tadda a falo. Abinci ta bashi ya ci sannan suka tsaya hira.

Can Buhari ya ce,
"Momy daman haka Matar Yaa Aslam take?"

Momy ta ce,
"Ta maka rashin mutuncin ko?"

"Uhmm batai min komai ba. Ni ko kallo na ma batai ba. Amman Momy kinga da shigar ta take yawo. Bayan nasan Yaa Aslam ba yason shigar banza. Kuma Momy sam bata da tarbiyya kinga irin kallon da take mana kuwa."

Ajiyar zuciya Momy ta sauke ta ce,
"Wallahi kowa complain din da yake min kenan in yaje gidan Aslam. Bansan me yake damun Aslam ba. Amman abin ba dadin ji. Ka ganni nan ban taba ganin ta ba ma bare na san ya take."

Kai Buhari ya girgiza ya ce,
"Momy bafa kiga ba."

Momy ta ce,
"Uhmm wallahi Buhari na rasa ya zanyi, ni yadda aka ce min ma ita ta zama mijin ma. dan sai ta ce yayi zai yi in kuwa ta ce, A'ah bazai taba yi ba. Baka ga ba duk ya zama wani iri abin tausayi. Anan fa kullum yake cin abinci dan wata rana ma ni nake aika masa har gida. Wallahi al amarin Aslam yana bani mamaki sosai."

Buhari ya ce,
"To Momy bakya ganin ba haka suka barshi ba. In ba haka ba, abin ai yayi yawa."

Shiru Momy tayi tana nazari ta ce,
"Kuma fa haka ne, wallahi ban taba kawo haka ba. To yanzu ya zanyi."
Chapter 36 · 0% Book details