← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 61

Sashe 50

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matsawa tayi ta zauna a kasa ba dan zata cin ba. Fulas din ya matsar mata dashi ya ce,
"Bismillah!"

Agogon hannun ta kalla sannan. Ta ce,
"Zan je nayi Assignment fa."

Ta yi maganar murya a shagwabe dan har ga Allah ta riga da ta saba da shagwaba in tana abu. bama in tana bukatar abu.

Sabir kuwa jin muryar da take magana da ita yasa nan da nan tsigar jikin sa ta mike.

*INDABAWA*
[1/18, 14:38] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

?? *HAJOW* ??

Dedicated to *My lovelly Mum*

*96-100*

Kina Ina Fateema kibiya. A gaakiya ina yaba hankalin ki. Da kokarin ki. Allah ubangiji ya kara basira da zakin hannu ni Maryam ina son ki

Mikewa yayi ya durkusa a gaban ta. Hannun sa ya daura a kan cinyar ta

Da sauri ta bude idon ta. Kallon sa ta tsaya yi kamar yadda shima ya kasa dauke idon sa daga kallon ta.

Hannun ta ya kamo ya fara murzawa a hankali.
Ya kira sunan ta a hankali. Ya ce,
"Husnah ki yadda dani wallahi ina son ki. Duk abunda ya faru ki manta da shi."

Ido ta rufe dan ita ta kasa mantawa da abinda Yaa Aslam yai mata.

To wai mema tai masa da har ya guje ta bayan yasan bazata ta iya rayuwa ba shi ba.

Bayan yasan duk farin cikin ta yana gare sa.
Bayan yasan shine ruhinta. Shine sirin ta daga mahaifinta sai Mami sai Shi da Yaa Buhari sune kadai gatan ta.

Amman shine ya juya mata baya. Ko yasan halin da ta shiga.
Ko yasan irin jinyar da tasha. Ko yasan irin azabar da take sha a duk sanda lokacin kiran sa ko turo mata da sako yai bai turo mata ba.

Duk shekarun nan da suka wuce in dai zata kwanata bacci sai tai kuka. Dan ya riga da ya sabar mata shine mutun na karshe da yake saka ta bacci da kishoshin Annabawa da sahanabai.

Amman duk a lokaci daya ya rushe duk abinda ke tsakanin su.
Tabbas ya dawo gareta ne dan ya raina mata hankali.

Ina dayar matar tasa. Ya dawo gare ta ne dan yasan irin son da take masa.

Ya dawo gare ta ne dan yasan da shi kadai zata iya rayuwar aure.
Ya dawo gare ta ne dan yasan duk lagon da zai amshi zuciyar ta.

Ya dawo gare ta ne dan yasan irin son da take masa.
To yayi karya duk son da take masa baza taba sakar masa ba.

Inda da ya nuna baya sona nima yanzu na hakura da shi.
Zan zauna da koma waye amman banda da Yaa Aslam.

Bazan zauna dashi ba Yaa Aslam ya wahalar da ni.
Tana tuna irin hirar rakin su da yakan ce bazai taba rabuwa da ita ba.

A lokacin in ta kawo misalin abinda zai iya raba su har haushi yake ji.

Amman lokaci daya ya rabu da ita. Ta kan tina irin alkawarin da yake mata da irin son da yake mata to duk suna ina.

Lallai in ta kara yadda da Yaa Aslam zai kara yaudarar ta ne.

Tasan tana son Yaa Aslam amman zata danne zuciyar ta ta nuna masa ita yanzu ba son sa take ba.

Sai ta kwatar wa kanta yanci a gun sa.
Idon ta ta bude jajir da su. Aslam dake rike da hannun ta ya zuba mata ido ya kara bude idon sa ganin yadda idon ta ya kada yai jajir.

Kuka ta fashe masa da shi. Nan da nan ya hau lallashi amman sam taki yin shiru.

Sai da kyar ta yi shiru nan ma ta mike ta yi cikin gida tana sharar hawaye.

Mami dake falo ta ga wucewar ta. Kai kawai ta girgiza.
Dan tasan Asma'u na son Aslam. Tana lura da yadda take rufe daki kuma duk tasan akan sa ne.

To ai dai jikin ta yai sauki dan haka tazo su shirya su tafi dan ta fara tausayawa Aslam. Bama da tasan kafiyar ta.

Tana zaune Aslam ya shigo shima duk yanayin sa ya sauya.
Kallon sa Mami tayi ta ce,
"Ya dai?"

Kai ya dan sosa ya ce,
"Ba komai!"

Mami ta ce,
"Shikenan ka fara shirin tafiyar ku. Tinda jikin nata yai sauki nan da jibi sai ku tafi ko?"

"To Mami Allah kaimu."
Ya fada yana mikewa.

Sama ya hau Mami ta bisa da kallo.
Asma'u ta shiga daki ta shiga bandaki ta watsa ruwa tai alwala.

Tana fitowa ta shafa mai tai salla. Tana kan sallaya Mami ta shiga dakin da sallama.

Dagowa tayi ta amsa tana gyara zama. Zama Mami tayi agefen gadon ta ta ce,
"Asma"u jikin ki yai sauki dan haka ki hada kayan ki nan da jibi sai ku tafi ko?"

Wata faduwar gaba ce ta zowa Asma'u dan har sai da ta dafe kirji jin kamar zai fadi.

Dagowa tayi ta ce,
"Mami Allah da saura na."

Mami ta ce,
"Asma'u ba inda yafi dakin mijin ki dadi da gatan ki. Ki tafi ke karasa warke acan. Allah baki lafiya. Allah miki albarka."

Kuka Asma'u ta saka ta ce,
"Mami bana son na tafi na barki. Mami na rasa Dady kema kada na rasa ki Mami ni a nan zan zauna."

Murmushi Mami rayi ta ce,
"Haba Husnan Dady. Kinsan sai kwana yayi ake tafiya. Kuma kinsan Dadyn ki bai da wani buri da ya wuce ya ganki a gidan Yayan ki matsayin matar aure. To ki daure ko dan Dadyn ki ki zauna lafiya a gidan mijin ki. ni kuma ki kwantar da hankalin ki zan na zuwa ganin ki akai akai. Kuma ga Yaa Fati nan ma. Ki daina kuka in ba so kike hankali na ya tashi ba."

Da sauri ta hau goge hawayen fuskar ta.

Bangaren Sabir da Nusaiba kuwa zaman lafiya suke sosai take kula da shi shima kuma so sai yake kula da ita.

Sai a yanzu yake jin son ta sosai a cikin jikin sa.

Perty kuwa tana can ta koma ga Allah yanzu Aslam take so ta gani ta roki gafarar sa

Tasan taci zalin Asma'u dan tasan soyayyar dake tsakanin su amman ta raba su.

Dole ta nemo Asma'u itama ta nemi gafarar ta

wannan dalilin ne yasa ta tafi kano dan neman inda Asma'u take.

Har gida Zainab ta zo jin Asma'u zata tafi.
Kayan gyaran jiki ta hado mata sosai, inda ta bata wasu ta ce ta tafi da su.
Haka ma Maimuna har gida tazo tai mata sallama.

Ana gobe zasu tafi suka je gidan Sabir. Gida ne mai kyau wanda aka zuba masa kayan more rayuwa kala kala.

Tinda suka je Nusiaba sai nan nan take da Asma'u duk Asma'u ta kasa sakin jiki saboda kallon da Aslam yake tsare ta dashi.

Shi yana mamakin Asma'u kamar ba ita ba.
Duk ta canja masa. Anya kuwa Asma'un sa ce wannan.

Shifa ko a gida baya ganin ta. Bare ya samu damar mata magana

To in ya ganta ma ya samu fuskar magana man.
Haka suka dan zauna sanna suka tafi gidan Mamah mahaifiyar Sabir.

Sosai Mamah tai mata nasihar zama da miji sanna ita ma ta hado mata kaya ta bata.

Gidan su Zainab suka je tayi wa mahaifiyar Zainab sallama.

Daga nan kuma suka koma gida
Duk tafiyar nan da suke kallo ne kawai nashi amman ya kasa koda mata magana.

A haka suka karasa gida ta debo kayan ta ta shige.
Sama ta hau ta ga Mami ta fito da akwati nan ta da na wajen Yaa Aslam da na wajen Sir Sabir da ya ce ya bar mata.

Zama Asma'u tayi ta ce,
"Mami na gaji. Sai kace ban saba fita ba."

Mami ta dago ta kalle ta ce,
"Kinsan jikin naki ne. Ya kamata kije asibiti yau."

"Eh sai anjima zan leka."
Asma'u ta fada dai dai shigowar Sabir.

Mami ta kalle shi ta ce,
"Kaga masu dibar kaya a kasa ko?"

Kai ya gyada, Mami ta ce,
"Kaje kace su zo so dauki kayan an gama."

Mikewa yayi ya fita. Mami ta ce,
"Tinda kince ke sai kayan Dady gasu can an saka miki su a mota."

Murmushi Asma'u tayi ta ce
"Mami ba haka bane, kinga Dady dan kar ya daurawa kowa nauyi ya siyon kayan nan. Kuma kayan nan da kyan su, bayan haka masu tsada ne to me za a canja ayi dasu. Kuma naga su aje yayi Mami dan zaman duniya dai kawai wani ma neman wanda bai kai shi ba yake amman bai samu ba."

"Haka ne! Kayan na da kyau masha Allah."
Mami ta fada.

Suna zaune aka shigo aka kwashe duk kayan.

Sai a lokacin jikin Asma'u yai sanyi ganin da gaske dai tafiya zatai.
Daki ta mike ta shiga.

Daren ranar tare suka kwama da Mami tana tai mata nasiha akan aure. Asma'u ji take kmar tace ta fasa. Wwai da da bata da burin sai ta ganta a gidan Yaa aalma amman yanzu duk bata so

Washe gari da safe Mami da kanta ta hada mata ruwan wanka.

Tai wanka ta shirya cikin wata Farar atamfa wacce akai mata adon da ja da baki.

Simple make up tayi, ta saka jan mayafi da jan takalmi sai bakar jaka.

Sosai tayi kyau. Ba abinda tta dauka saboda komai nata an tafi mata dashi.

A falon sama ta samu Mami da Yaa Aslam wanda ya saka wata milk din shadda tai masa kyau.

Sai tashin kamshi yake yi. Yaa Buhari a gefen sa. Sai Zainab dake dakin Mami.

Gefen Mami tayi ta zauna. Yaa Buhari ya kalle ta ya ce,
"Ji 'ya Malama tashi zakiyi dan yanzu zaku tafi."

Baki ta turo ta dan harare shi. Daga kan da zatai sai taga Yaa Aslam ya zuba mata ido baki da hanci yana kallon ta.

Kai ta dauke ta kalli Mami ta ce,
"Mami ni kam in nace na fasa ai ya fasu ko?"

Kai Mami ta daga. Yaa Buhari yai dariya ya ce,
"Karya kike wallahi."

Mami ta ce,
"Ku tashi ku tafi."

Kwanciyya tayi akan kafar Mami. Zainab ta fito ta ce,
"A'ah me zan gani!"
Chapter 50 · 0% Book details