← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 61

Sashe 24

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya yayi ya ce,
"Toh Ashe kuwa abin xai xo muga bamu tanadi komai ba my.
Indai haka xakina cewa my."

Asma'u tayi murmushi ta yi kasa da kai ta ce,
"Haba To ni me zance?"

Dariya Aslam ya karayi ya ce,
"ke kuwa kike da abinda xaki ce, My just ra'ayin ki xaki fada da abinda kike ganin ya dace musa acikin tsari Wanda may be ni hankali Na be kawo kai ba."

Asma'u ta ce,
"kamar me?"

Ya ce,
"Kamar ace a ra'ayin ki, May be akwai wani event da kike ganin kina bukata ayi."

Kan Asma'u a kasa ta ce,
"fadin ra'ayin ka naji."

Ya ce,
"My ina so if possible ace ran Friday xa'a daura mana aure after mosque."

Murmushi Asma'u tayi dan itama tana sha'awar daurin auren ranar juma'a.

Kai ta daga ta ce,
"Yayi kyau nima ina son haka."

"Yauwah koke fa. Sai batun sauran event me da me kike ganin za'ayi."

Dariya tayi ta ce,
"Duk yadda My yake so haka za'ayi."

Numfashi yaja ya ce,
"Kinsan sauran Event duk naku ne, daurin aure da dinner sune kadai namu."

"To ni dai nasan Mami zata yi yini da kamu daga haka bansan me kuma ba."

Murmushi yayi ya ce,
"Shigar da zamuyi kuma fa?"

"Wayoo Ya Aslam ni bansan yadda za ayi ba."
Ta fada yana turo baki.

Aslam ya yi dariya ya ce,
"Wallahi *Husnah* zamu bata, sai kace bakya son maganar auren tamu. Oya fada min wane kalar dressing kike so muyi ran dinner."

Baki ta turo tana kun kuni. Dariya yayi ya ce,
"Eh sai kin fada. Kaji yarinya daga an mata maganar aure ta maidani sirikin ta. Maza fada min ko na fadawa Dady ayi auren ending month din nan."

Dariya tayi ta ce,
"Ayi man."

"Haka kika ce?"
Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah!"

Ya ce,
"To fada min."

Shiru tayi sannan ta dago ta ce,
"Ran Dinner ina son dressing din gloding kala. Ran Daurin aure kuma farar shadda zaka sa ko blue?"

Kallon ta yayi ya ce,
"Ke nake son ki zabar min. Amman gani nake fara zata fi saboda ranar farin ciki ce kamar yadda zuciya ta take fara haka nake komai nawa ya zama fari."

Murmushi tayi ta ce,
"To kaga ka zabi abin ka."

"Haka ne, sai na ranar yini."
Dariya tayi ta ce,
"Duk kalar da ka zaba."

"Ok ranar zan saka blue din shadda dan haka kema ki saka something da zai hau dashi."

Kai ta daga ya ce,
"Gobe zan sa Momy ta tanadar mana kayan."

Kallon sa tayi tana dariya. Ta ce,
"Ya Aslam duk saurin nan fa."

"Kedai bari wallahi ji nake kamar na matso da kwanan nan kusa "

Dariya tayi ta ce,
"In kana wannan zumudin sai ina jin tsoro kar wani abu ya faru."

"Kefa haka kike. Dan Allah ki daina sa haka a ranki za'ayi komai lafiya a gama lafiya da izinin mazon Allah (SAW)"

"Allah yasa to!"
"Ameen!"

Kallon ta yayi yai.murmushi.
"Lafiya?"

Ta tambaye shi. Murmushi ya karayi ya ce,
"Wai ya zanji ranar da My ta zama mallaki na."

Kasa tayi da kai. Ya ce,
" *Husnah* duk ranar da kika zama tawa wato mallaki na sai nayi azumi guda bakwai na godiya ga Allah da ya mallaka min ke."

Dariya tayi. Ya ce,
"Ranar zan yi abinda ban taba sanin me zan yi ba har yanzu amman ranar zata zama rana mafi soyuwa a rayuwa ta."

"Yaa Aslam kenan!"
Murmushi yayi ya girgiza kai ya ce,
" *Husnah* kenan amman dai baza kizo kina min kuka ba ko? Tinda gaki a gun life partner din ki."

Murmushi kawai tayi. Aslam ya ce,
"Wannan murmushin naki make me go crazy."

"Allah ko Yaa Aslam kana kashen bakin magana ne."

Murmushi yayi ya ce,
"Plz don't u ever forget I love u. (Dan Allah kada ki taba mantawa ina son ki.)
Plz promise to never leave me even if there are thousand and one reason to. (Dan Allah ki min alkawarin baza ki taba bari na ba ko da akwai dubun nan dalilai da huja da zaki)
Plz promise to stay with me no matter how hard or difficult the relationship might be. (Dan Allah kimin alkawarin zaki kasance dani duk rintsin yanayin da zamu tsinci kan mu a ciki.)
Do u konw why am saying all this? (kinsan saboda me nake fadan duk wannan)
Because I never ever want to loose u My,
If I loose u, I have lost a grate part of me (saboda bana son na taba rasa kine tawan, in na rasa ki na rasa wani babban bangare daga gareni.)
Idan na rasa ki
Nayi mummuna rashi My
To me u are the perfect wife and I just want to make u mine. (A waje na, ke ce cikakiyar mata. Kuma kawai ina son na mai dake tawa.)"

Kasa tayi da kanta. Mikewa yayi ya dawo gaban ta. Kan ta ya dago idon ta a lumshe.

"Dan Allah ki amshi alkawari na."
Dagowa tayi ta ce,
"Yaa Aslam komai naka ina son ya kasance gaskiya dan nima shine duk burika na. Ina addu'a Allah yasa duk abinda ka ambata ya zama gaskiya da nafi ko wacce mace farin ciki da samun soyayar gaskiya."

"Nagode *Husnah* Nagode Allah mallaka min ke."
"Ameen!"

Ta amsa. Mikewa tayi ta ce,
"Mu shiga ciki ko?"

Kai ya gyada mata yabi bayan ta.

*INDABAWA*
[1/18, 14:20] Maryam S Indabawa🥰:  *LABARIN RAYUWAR*

*Asma'u Husnah*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*

Dedicated to *My Lovelly Momy*

*126-130*

An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: “ *Manzon Allah(ﷺ)* Ya Hana Mutum Riqe Kwankwasonsa a Cikin Sallah”. *(Bukhari da Muslim)* a Lafazin Muslim: *“Shine Mmutum Ya Sanya Hannunsa a Qugunsa”.*_

Satin Yaa Aslam daya ya juya da shirye shiryen bikin su.

Dan yana komawa yasa Momy a gaba dole suje dubai su hadu kayan lefe.

Momy ta ce, ya bari lokaci ya kara karatowa. 'Ki yayi ya ce shidai su tafi.

A satin da ya dawo a satin suka tafi hado lefe.

Siyayya mai yawa da tsada sukayo. Duk abinda yaga ya burge shi ya ce a dauka. Haka nan Momy itama da ta iya zabe kaya masu kyau da tsada ta dinga siya.

Kaya sai da suka hada set akwati uku amma basu isa ba.

Sosai Momy ta hado mata kayan kwalliya da english wears dan ta san irin shigar da Asma'u take kuma tasan Asma'u yar gayu ce.

Haka suka dawo gida da niki nikin kaya. Shi Dady da ya gani ma cewa yayi sunyi kadan.

Kudi ya bayar a dado kayan da gwala gwalai. Har da Mota Dady ya ce a hada mata.

Momy tace,
"Dady ai ba yanzu za akai kayan ba."

Dady ya ce,
"Me za'a jira to. Kunga akai kaya ai sa rana kawai komai yazo daga baya."

Momy ta ce,
"To Dady in haka ne, ai kune masu kai kayan dan na fison maza suyi komai. Mu masha biki daga baya."

Dady ya ce,
"Zan fadawa su Alhaji Aliyu da Ahaji Abubakar da Dadyn Asma'un ma. Amman ni ban ga amfanin ajiye laifen ba akai musu kawai a huta."

Kai Mami ta gyada ita ma dai gara akai musun kawai. Amman kuma abu kusan shekara guda.

A cikin satin akai wa su Dady magana kan za a kawo kaya.

Dady cewa yayi baiyi wuri ba tinda abinda saura.

Amman Dadyn Aslam ya ce gara a kawo ai kamar yau ne.

Rana suka saka aka kai komai da komai. Aka sa ranar auren su nan da shekara daya.

Sai kayan lefe da aka kai. Kayan sosai Mami tayi fada wai sun zubo kaya da yawa.

Momy ta ce, to in bata kashewa Asma'u kudi ba wa zata kashe wa. Ta ce,
"Amina kada ki manta fa haka kawai ma kaya nake siyawa Asma'u bare kuma yanzu. Ki daina nuna min ke kika haifi Asma'u to wallahi ji nake kamar ni na haife ta. Kinsan dai uwa daya uba daya ba wasa bane."

Mami ta ce,
"Haka ne Yaya amman kun kashe kudi da yawa."

Momy ta ce,
"Akwai kayan fitar bikin su ma da za a aiko dan haka ki zuba idon zuwan su. Suna gun dinki na bada a dinka mata su."

"To Yaya angode Allah kara girma."

"Ameen! Zancen kayan kitchen kuma na gama da komai."

Haka suka gama wayar Mami na kara duba kayan da aka kawo.

Asma'u kuwa duk ji take kamar a mafarki wai kayan lefen ta ne.

Ji take kamar wasa kamar ba zata auri Yaa Aslam ba.

Tinda aka kawo kayan ta sanar da Zainab.

Zainab kuwa ranar da ta sanar mata tazo ganin kaya.

Sai zolayar ta take. Asma'u dai sai dai tayi murmushi. Bakin ta ya mutu sai dai dariya ko murmushi.

A kwana kin nan wata shakuwa ce ta kara shiga tsakanin Asma'u da Dady.

Dan yanzu wani lokacin baya zuwa office ko da yaushe tana tare da shi.

Kullum maganar sa daya ce
" *Husnah* ki rike Aslam. Aslam masoyin kine, bani da burin da ya wuce naga auren ku. To in Allah ya nuna min zanyi murna. Haka nan in Allah bai nuna min ba shima zanyi murna dan nasan na bar ki a hannun wanda zai kula dake ko ba aure a tsakanin ku."

Yayi shiru sunan ta ya kira ya ce,
" *Asma'u* "

Da sauri ta dago kanta. dan Dady baya kiran ta da Asma'u. Murmushi ya sakar mata, ya ce,
" *Husnah* ki kasance mace ta gari a wajen mijin ki. Kiyi koyi da halin Mahaifiyar ki.  Ni Nasan wace, *Husnah* to ina fatan halin da nasan ta da shiki koyi dashi."

Dady a ko da yaushe bai da maganar sai akan ta rike Aslam. Aslam masoyin ta ne.

Sai kuma nasiha da kullum suka zauna zai na mata kan ta.kula da mijin ta tai masa ladabi da biyayya.
Chapter 24 · 0% Book details