Sashe 5
Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawar tata tace
"Preety ina bayan ki. Amman ina zakije wajen malamin?"
"Kinsan gobe zamu tafi Dubai ni da Moma. To da mun dawo zan shirya zuwa nijar."
"Allah dawo daku lafiya."
Kwance *Asma'u* take akan sofar dake dakin ta. Waya ce a kan cikin ta.
Sanye take da dogon wando, sai riga purple wacce da kadan ta wuce gwiwar ta.
An mata ado da stones sai kwalli suke yi. Kanta hula ce baka.
Idon ta a lumshe sai kace me bacci.
"Kina jina."
Ya fada daga cikin wayar. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan. Ta amsa masa da.
"Eh! Ina jinka."
Ya cigana da fadin.
" *Husnah* wallahi kin sacen zuciya ta gaba daya. Ban da tunani da buri in ba na na mallake kiba."
Shiru tayi,
"Wallahi zan iya sadaukar da kome nawa dan samuwar farin cikin ki. Na miki alkawari ba abinda zai raba mu sai mutuwa."
"Yayanah na yadda dankai kuma nasan kai me sona ne. Nima bazan taba barin ka ba ko juya maka baya ba."
"Nagode *Husnah* Allah miki albarka. Allah mallakamin ke."
"Ameen Ya Allah!'
Aslam ya ce,
"Toh yanzu me kike."
Asma'u ta ce,
"Ina kwance ne."
Aslam ya ce,
"To maza tashi kije kiyi alawala kinga magariba ta kusa kiyi ta lazumi."
Asma'u tayi murmushi ta ce,
"Toh Yayanah."
Shima murmushi yayi ya amsa mata da
"Aha Sai Anjima."
Mikewa tayi ta shige bandakin ta tayo alwala. Akan sallaya ta zauna tana lazimi. Sai da taji kiran sallah sannan ta mike ta tada. Tana idarwa ta dauko alkur'ani ta fara karantawa.
Sai da aka isha'i sannan ta mike tayi sallah. Ta jima tana addu'a sannan ta shafa ta mike ta fita falo.
Tin daga bene ta fara cewa.
"Dady nah Oyoyo!"
"Oyoyo *Husnah* ta."
Ta sauko ta karasa wajen sa.
"Dady Ina yini?"
"Lafiya!"
"Dady ya aiki."
"Lafiya Alhamdulilah! Ya makaranta."
"Makaranta lafiya Dady!"
"Masha Allah! Badai wata matsala ko."
"Babu!"
"To Allah yayi albarka."
"Ameen!"
Ta juya wajen Ya Buhari.
"Ah Na Anty Zee barka da dawowa."
Hararar ta yayi ya dauke kai.
Dariya ta saki.
"Dady kaga ina masa sannu da zuwa ya harare ni."
Murmushi Dady yayi, ya ce,
"Wai wace Zee din nan ne?"
"Sis yi hakuri dan Allah!"
Ya Buhari ya fada yana marairace mata.
Asma'u ta kanne ido daya tace,
"Yo Dady ai ka gane kawai."
kai Dady ya dan daga ya ce,
"Oh nagane yar gidan Dady."
Suka yi dariya gaba dayan Dakin.
"Ai ni gara ya kawon surikar wallahi."
Mami ta fada tana kallon sa. Shi dai kasa yayi da kansa kawai.
"Ai fah!"
Dady ya fada yana kallon *Asma'u*
Gira ta dage masa. Suka saki murmushi tare.
"Uhmm Abban nah tashi muje kaci abinci."
Ta kama hannun sa.
"Mami ku taso muci abinci."
"To!"
Kamar kullum bayan tagama tsokanar Yayan ta ta haye sama. Tai wanka tayo alwala ta shirya cikin kayan baccin ta.
Kwanciya tayi tana jiran kiran sa. Ai kam ko minti uku batayi ba sai ga kiran sa nan.
Murmushi ta saki wanda ya kara fito mata da ainihin kyauwun ta.
Muryar Aslam ce ta daki kunnen ta bayan ta kara wayar. ya ce,
"Hello! Baby nah!'
Gyara kwanciyya tayi ta ce
"Na'am my Yaya."
Murmushi yayi ya ce,
"Ina matukar kaunar ki Habibaty."
Asma'u ya ce,
"Nima haka Yaya nah."
Aslam ya ce,
"Kinsan me?"
kai ta girgiza kamar yana ganin ta ta ce,
"A'ah!'
Aslam ya danyi jim sannan ya ce,
"Wani abu na gama tunani."
Da sauri ta ce,
"Na mefa?"
Aslam ya ce,
"Hmm tunani nayi a duk cikin duniyar nan duk cikar ta sai Allah ya hada mu a soyayya bayan nasan kin fini komai da komai. Allah nagode maka."
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce,
"Haba Yayana me nafika, kai ma kasan ka fini. ni zan yiwa Allah godiya da ya hada ni da miji kamar ka."
Aslam ya ce,
"Baby kin wuce duk inda nake tunani. Ke ta daban ce. Haka son ki ma na daban ne a cikin zuciya ta."
Ta ce,
"Yayanah nima haka kake a zuciya kana da matsayin da ba wanda yake dashi a guna. Kana da gurbi na daban a cikin zuciya ta."
Murmushi yayi. ya ce,
"Kisani dake kadai zan so na rayu kuma na mutu. Har abadan da ke nake son na kasance."
Shiru tayi! Tana me sauraron sa tare da lumshe ido fuskar ta na fitar da wani murmushi na nishadi da farin ciki.
Ya cigaba da magana,
" *Husnah!* Zuciya ta da taki abokan juna ne da basa taba rabuwa ko agun bacci Ido biyu ko a cikin bacci na ke nake tunani haka ma a fili. Wallahi son ki ya zama jinin jikina rabani dashi tamkar raba ni da rayuwa ta"
Ido ta bude ta ce,
"Yayanah na yadda dakai haka duk abinda zaka fada suma na yadda dasu. Kar ka damu insha Allahu ni taka ce har abada."
Aslam ya ce,
"Nagode *Husnah* zan miki alkawarin bazan taba rabuwa dake ko juya miki baya ba."
Asma'u tace,
"Nima insha Allah bazan taba barin kaba sai dai in har ka ka bukaci hakan."
"Shittt!"
Ya fada da karfi.
"Indai nine bazan taba bukatar hakan ba."
"Allah ya sa."
ta fada a sanyaye
"Baki yadda ba."
ya tambaye ta
"Haba dai na yadda da Yayanah. Kai dai kawai kace Ameen."
Ta fada duk yanayin ta a sauye.
"Toh Ameen ya Rabbi."
"Yauwah ko kai fa."
Dariya ya saka.
"Lalai Baby nah. Kin mai dani kamar Baby ko."
Murmushi tayi ta ce
"Oh to mene in na maida kai Baby nah!"
Dariya yayi ya ce,
"Ba komai nasan zan sha gata ne ma."
Ta ce,
"Ashe ka gane."
"Eh! Amman fa kece Baby."
"Wai nice Baby shekarata nawa."
ta tambaya taba turo baki
Murmushi yayi dan yasan *Husnah* da son girma ya ce,
"Ni a wajena ina kallon ki kamar yar shekara biyar dai dai lokacin da yara suka fi shagwaba da rigima."
Baki ta bude ta ce,
"Lalalah! Ni din biyar fa kace."
Dariya Aslam yayi ya ce,
"Eh man."
Asma'u ta ce,
"Yaya ka manta shekara tane."
ya ce,
"Shine nace a wajena ai."
Ta ce,
"Oh! Saboda me to?"
"Saboda Babies abin rarashi ne da tarairaya da shagwabawa. Wannan yasa nake kallon Baby nah ahaka saboda na mata duk abinda na lissafa."
"Oh inkuwa haka ne. Na yadda ni Babyn kace."
Dariya yayi ya ce,
"Yauwah Baby nah."
"Toh nima kai Baby nane. Tinda ina son ina maka abubuwan da ka fada."
" *Husnah* kenan. Dare yayi aje ayi alwala azo ai addu'a"
"Toh"
Ta fada tana mikewa.
*Morning My Yan uwa*
Hhh wai da gaske Asma'u life na burge ku. To haka ake so mutum ya kasance kar ya dulmiya da duniyar nan sosai. A komai kana riko da alkur'ani kariya ne gare mu sosai.
Muna godiya da Allah yayi mu a matsayin musulmai kuma yake bamu ikin karanta sakonnin sa. Wanda duk karantawa da zamuyi muna samun lada mai yakai wannan dadi.
Kana karantawa kana jin dadi da annushuwa da nishadi. Sai alkur'ani.
Alhamdulilah
*Muje zuwa*
*INDABAWA*
*love u wujiga wujiga masoya na.*
[1/18, 14:06] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*
BY. *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*
*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍✍✍
*Da farko ina mai bada hakuri dan zan canja sunan littafin nan daga *Asma'u Husnah* zuwa *labarin rayuwar Asma'u Husnah* wanda dalilin haka yasamu ne na wata yar uwa marubuciyya da tayi littafi mai suna *Asma'ul Husnah* wanda ni na canjawa nawa suna yanzu.
Ina fatan xaku cigaba da karanta *labarin Rayuwar Asma'u Husnah*
Nagode
*26-30*
Dedicated *FIRST AND LAST LOVE. MY MOMMY*
*Manzon Allah (SAW) Yace, "Idan watan ramadan yazo ana bude kofofin aljanna ana rufe kulle shaidanu" (mu yawaita abinda zai samu samun rabauta duniya da lahira)*
Da wuri ta kamala abinda zasuyi ta shirya tayi wajen Dadyn ta.
Tare sukai break, sannan ta tafi. Da wuri ta shige ajin su.
Text din Ya Aslam ne ya shigo.
"Morning Pretty nah. Ya kike tin dazu nake son kiran ki. Nasan kina aiki. in kingama ki turon hoton ki. Sannan naje Lagos ne Dady ya aike ni. Ina bukatar addu'ar ki."
Murmushi tayi ta maida masa da sakon.
"Na tashi lafiya Yaya nah. Kaima ina fatan kana lafiya. Ya hanya. Hotona yana can na tura maka yana jiran ka."
Ta tura tana murmushi, Zee ce ta taba ta,
"Sis Lafiya kike ta zuba murmushi haka."
"Lafiya lou wallahi. Kin karaso kenan."
"Eh!"
Dai dai shigowar malamin su. Sai karfe sha biyu ya fita wani ya shigo yai musu awa daya sannan suka tafi sallah.
Suna fito wa suka shiga cafeteria suka siyo lemo da snack, a nan kofar hall din su suka zo suka zauna. Karkashin wata bishiya.
A jaka suka saka abincin su dan ba lokacin zasu ci ba, kawayen su ne suka karaso wajen su uku.
"Ah *Asmy* da Xee."
Su ka fada suna dariya.
Murmushi sukai masu,
"Ya kuke?"
"Lafiya lou. Ya karatun."
"Alhamdulilah."
"Masha Allah!"
Suka zauna suna dan taba hira.
Sai karfe biyu suka koma aji dan daukar wani darasin.
Karfe hudu sun gama kowa yayi gida.
*WACECE ASMA'U HUSNAH*
*Asma'u* 'ya ce ga Alhaji Suleiman. Alhaji suleiman dan kasuwa ne duk da yana da kwallin masters a hannun sa. Ya karanci fanin kasuwanci. amman yafi sha'awar kasuwan ci da aikin gwamnati.
Sai daga baya ne ya nemi aiki sannan yake hada kasuwanci da aikin nasa.
Alhaji Suleiman dan gidan Malam Haruna ne, Malam Haruna malami ne, kuma dan garin kano ne. Cikin garin Madobi.
Yana da matar sa daya Aisha, Allah ya azurta su da Ya'ya uku maza sai autar su mace.
Alhaji Suleiman shine babba da matar sa daya hajiya Amina. Ya'yan su biyu, Buhari da *Asma'u Husnah*
Sai Abubakar me bi masa, yana aiki a banki matarsa daya masa'uda, da ya'yan sa biyar duk maza.
Abubakar, Suleiman, Abdulhakim, sai yan biyu. Dukkan su sun girma kowa ya kama aiki. yana zaune anan katsina shima.
Ilyasu shima matar sa daya soja ne. Yana da ya'ya uku duk maza suna zaune a kaduna.
Muhammad, sai yan biyu shima. Shima dukkan su sun girma suna aiki.