← Book details Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 61

Sashe 11

Asma'u Husnah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kaga Yaya muje ka kaimu dare nayi."
Gaba yayi Zainab tabi bayan ta shi ya bude mata mazaunin ta gaba ta shiga.

Asma'u ta tsaya ta ce,
"Ai kuwa nima sai an bude min in ba haka ba bazan raka ku ba."

Rankwashi Yai mata ya ce,
"In na bude me zai cijeni."

"Babu!"
Asma'u ta fada tana zama a cikin motar.

Suna tafe suna hira suka bar Asma'u ganin haka yasa ta dauko waya ta kira Yaa Aslam.

Waya suke tana bashi labarin zuwan Zainab da abinda suke mata.

Hakuri ya bata ya ce,
"Dadin ta kema kina da wanda zaki hirar dashi ko?"

"Eh man."
Daga nan suka dinga waya har aka zo gidan su Zainab.

Sai da Asma'u ta rakata gida ta gaida Momin ta sannan sukai sallama Momi na mata godiyar kayan da Mami ta bata.

A mota ma wayar ta taci gaba dayi tabar Yaa Buhari yana ta surutun sa shi kadai.

Sai da ta gama waya da take yai ta mita ta ce,
"Kaji Yaya kai lokacin da kukai min banza me nace nima ramawa zanyi."

Dariya yayi ya ce,
"Wai wane wannan sirikin nawa ne?"

"Bazan fada ba."
Dariya yayi ya ce
"kinsan dai dole na sani ko?"

"Naji lokacin ka sani."
Daga haka suka cigaba da hirar su abin sha'awa har suka koma gida.

A falo suka tadda Dady suka masa sannu da zuwa sannan ssuka ci abinci.

Sannan kowa yayi daki sa dan yin bacci.

Kamar yadda ta saba haka tana kwanciyya Yaa Aslam ya kira.

Sai da sukai waya sannan sukai awala tai addu'a suka kwanta yana mata tarihin sahaban mazon Allah (SAW)

*Indabawa*
[1/18, 14:11] Maryam S Indabawa🥰:  *LABARIN E
RAYUWAR*
ASMA'U HUSNAH

By *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*

Dedicated to *My Mommah*
*Uwata gari mai burin ganun cugaba da ingantuwar tarbiyyar ya'yan ta.*

Na gauda duk wata *UWA* Allah kuma yai muku kyakyawan karshe ya bamu ikon muku biyayya yasa mu gama daku lafiya.

*56-60*

*Wanda kame harshensa, ya kiyaye farjinsa, ya shiga taitayinsa, ba zai ta6a yin Danasani a Duniya ba.*

Yau kamar kullum tin asuba bata koma bacci ba sai da ta gama komai tayi wanka sannan ta shirya cikin jar doguwar riga mai dogon hannu. Sai bakin mayafi da ta yafa.

Bakar jaka ta dauko ta ciro littafan ta ta zuba a ciki. Turare ta fesa ta dauki bakin cover shoe ta saka ta tafi dan yiwa Dady sallama.

Dady ya amsa yana kallon ta ya saki murmushi ya ce,
" *Husnah* kinyi kyau!"

Murmushi tayi ta zauna suka gaisa, anan yake fada mata ginin asibitin da ake mata ya kammalu dan haka zai je yayo order kayan da za'a zuba.

Asma'u baki yaki rufowa sai murmushi take tana ta godiya ga Dady.

Ba abinda Dady yake so kamar yaga ya farantawa iyalan sa.

Hannun ta ya kamo ya ce,
" *Husnah* ki kara gwazo ba abinda bazan miki ba in dai bai fi karfi na ba kome ne indai kina so zan miki."

Murmushi tayi ta ce,
"Dady nagode!"

Abinci ta hada masa, kallon ta yayi nan da nan ta gane abinda yake nufi dan haka ta fara hada tea.

Agogo ta kalla taga har karfe takwas tayi. Yau za'ai submitting assignmenat din Sir Sabir gashi ya ce in takwas da rabi tayi monitor yakai masa.

Tana rasa dalilin da yake sata tana yawan makara.

Ba yadda zatai yiwa Dady haka ta zauna ta dinga cusa abinci har ta gama ta mike.

Kudi ya bata ta amsa tana godiya tai masa sallama ta yi dakin Yaa Buhari,

Yau taci sa'a ta same shi yana shiryawa. Murmushi tayi tana murna zai rage mata hanya. ta ce,
"Na Anty Zee barka da safiya!"

Kallon ta yayi ya ce,
"Barka kadai ya kika tashi?"

Ta ce,"
"Lafiya Alhamdulillah! Yaya dan Allah...."
Sai kuma tayi shiru

Kallon ta yayi ya ce,
"Dan Allah me?"

Kai ta dan sosa tace,
"Wallahi na makara gashi malamin mu ya ce Takwas muyi submitting din Assignment."

"Ke kika sani!"
Ya fada yana taje kan sa.

Kallon sa tayi ta kalli agogon dake hannun ta. Ido ta zaro ta ce,

"Inna illahi wainna illahir rajiun!"
Ta fada tana fashewa da kuka.

Kuka take sosai, tana bubbuga kafa a kasa kai kayi zaton dukan ta akayi.

Kallon ta Buhari ya tsaya yi, dan inda sabo ya saba da halin Asma'u na shagwaba.

Sai da yaga da gaske dai take sannan ya mike ya kamo ta.

Kukan ta cigaba dayi shi dariya ma ta bashi.

Da wannan kukan da ta tsaya yi ta dauki kusan minti uku dama zuwa tayi Baba ya kai ta amman ta tsaya.

"Yi shiru yi shiru, shige muje!"
Ya fada yana daukar hular sa ya saka

Hannun ta ya kama sukai dakin Mami, gaisawa sukai ta tsaya kallon Asma'u ta ce,
"Wannan kuma fa?"

Ta fada tana nuna Asma'u. Dariyar Buhari ya danne ya ce,
"Shagwaba daga ta makara sai kuka."

Mami ta ce,
"Ai Asma'u akwai wasa wallahi kasan Allah tin asuba bata komawa amman da ta gama taya ni aiki ta shiga wanka sai ta dauki kusan awa tana wanka bare shiryawa kuma tayaya baza ta makara ba."

Murmushi Buhari yayi ya ce,
"Uhm Ai "Asma'un Dady sai Dadyn. Mami mun tafi sai mun dawo."

Ya kama hannun ta suka fice Asma'u na dagowa Mami hannu.

Murmushi Mami tayi itama ta daga mata hannu. A ranta tana cewa,
"Asma'u kenan."

A mota ma haka ta dinga a zalzala shi amman ina tin a gida takwas da rabin ma tayi.

Tana zuwa taga da malami a ajin a haka ta shiga ta zauna suka dinga amsar lecture.

Sai da malamin ya fita Zainab ta karaso gefen ta tana dafa ta.

Kallon ta Asma'u tayi fuskar ta dauke da damuwa. Ta ce,
"Kiyi hakuri ki tashi muje ki kai masa ki bashi hakuri."

Baki Asma'u ta rike ta ce,
"zai amsa."

Zainab ta ce,
"Insha Allahu."

Agogon hannun ta Asma'u ta kalla ta ce,
"Sis kinga fa har sha daya."

"Tashi muje insha Allahu zai amsa."
Mikewa Asma'u tayi jiki a sanyaye suka nufi wajen office din malamai.

Suna zuwa gefen office din Zainab ta ce,
"Kije ki fito ina jiran ki."

Fuska Asma'u ta bata zatai magana Zainab ta ce,
"Kiyi hakuri kisan dai malamai basa son rakiyar nan ko?"

Kai ta gyada ta tsaya ta kasa tafiya. Zainab ta ce,
"Haba Asma'u kije man."

Kamar bazata je ba kuma sai ta fara tafiya a hankali kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki.

Zainab na kallon ta tasan halin Asma'u zuwan ne bata sonyi. Take wannan tafiyar kamar me.

Murmushi tayi ta karasa karkashin wata bishiya ta zauna.

Asma'u kuwa ji take kamar ta juya gaban ta sai dukan uku uku yake a haka ta karasa har kofa office din da aka rubata *Sabir Marzuk*

A hankali tayi knocking wanda ita kanta ba dan ita tayi ba da bazata ji ba.

Sai da tayi irin knocking din nan sau uku sannan ta samu tayi da dan karfi.

Izinin shiga ya bayar. Handle din kofar ta murda a hankali ta bude.

Wani kamshin turare hade da sanyi me dadi taji yana tashi.

A hankali ta kutsa kai ciki tana yin sallama kamar bata so.
"Assalamu Alaikum!"

Dago kai yayi jin muryar ta. Kallon ta ya tsaya yi kafin yai saurin kawar da fuskar sa, ya amsa da
"Wa'alikum salam!"

Kai tayi kasa dashi ta kasa magana. Shiru ne ya biyo baya na kusan minti biyu.

Shi kam kallon ta yake kawai yana mamakin ta.

Tsaki tayi a zuciyarta ta ce,
"To me zan ce?"

Da kyar ta iya dago kanta ta ce,
"Uhm uhmm Sir dan Allah ina neman taimakon ka ne?"

Kallon ta shima yayi ya ce,
"Ok!"

"Uhm Uhm!"
Sai kuma tayi shiru.

Murmshi yayi ya ce,
"Ki saki jikin ki me zan taimaka miki dashi."

Yai maganar cikin harshen turanci.

Dan sanyi taji ji a ranta da bai mata rashin mutunci ba.

Dagowa tayi suka hada idon. Idon ta Cike Da kwalla kamar zatai kuka. kallon ta yayi yai saurin kawar da fuskar sa. ta ce,
"Sir Assignment nazo nai submitting"

Kallon ta ya tsaya yayi, yana mamakin ta, 'wai Assingment tazo kawo wa."

Asma'u ta ce,
"Sir Kayi hakuri na zo a makare ne."

Ta fada murya na rawa. Hannu ya mika mata kawai.

Jakar ta tai saurin a jiyewa kan kujerar dake gaban table din sa.

Dauko takardar tai a cikin wani littafi ta mika masa.

Amsa yayi ya zubawa sunan ta ido.

*Asma'u Suleiman* rubutun ya kalla yaga kamar computer ce ta rubuta shi.

Sai da ya kai hannu ya shafa ssanan ya kara kallon sunan ya ce
" *Asma'u Husnah* "

Wata faduwar gaba Asma'u taji tai sauri dago idon ta.

Dan duk duniya a wadan da ta sani take rayuwa dasu mutum biyu ke kiran ta da *Husnah* ko su ce, *Asma'u Husnah* sai kuwa yanzu da taji shi ya ambata.

Sunan yai dadi da yadda ya kira ta sai taji kamar Yaa Aslan ne ya kira ta.

Kai kadai ta gyada masa, ya ce,
"Zaki iya tafiya."

Jakar ta ta dauka, ta ce,
"Nagode!"

Ta juya a hankali ta bar office din.

Zainab na hango ta ta mike ta ce,
"Ya dai ya amsa."

Kai kadai ta gyada mata ta ce,
"Muje kar malama safiya ta shiga."

Suka kama hannu suka tafi.

Sai da aka tashi suka fito sukai sallah suka yi wajen Baba da yazo daukar ta.

Munasha ce ta karaso gun da sauri tta ce,
"Hae Babies!"

Da sauri suka juya. Amsa'u ce ta danyi murmushi ta ce,
"Sannu!"

Zainab kuma ta hade rai tana yin gefe.

"Baby an tashi ko ina Yayan ki?"
Amsa'u ta ce,

"Yana nan lafiya."
Munasha ta ce,
"Dan Allah wane irin aiki yake yi ne?"

Asma'u ta ce,
"Likita ne!"

Ido Munasha ta bude ta ce,
"Wow kace gidan ku kwari ne, amman ya dace likita. in kinje ki gaishen dashi."

"Zai ji insha Allah!"
Ta fada tana juyawa.

Munasha ta ce,
"Tnc bye!"

Ta juya kawar ta na bin bayan ta.
Chapter 11 · 0% Book details