← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 95

Sashe 94

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*washe gari*
Sai around _11:30am_ Haleesa tafalka koda tashi har Habeeb ya yi wanka yashirya, yana zaune kusa da ita murmushi yasake mata ita ma ta mayar mishi da martanin murmushin nashi tasauko daga bed tanufi bathroom ta yi wanka tafito daure da towel Habeeb yatayata ta shirya cikin atamfar super Sheraton ta yi matuk'ar kyau ruwan Lipton kadai tasha Rarrashinta Habeeb yashiga yi haba! Leesa ruwan Lipton ba zai rik'e ki ba ki daure ki cin abinci mai d'an nauyi ko don saboda babynmu.
"Yatsine fuska ta yi kamar za ta yi kuka banaso yaya Habeeb in naci amai zan yi ni dai katashi ka kaini gidan Hannah maybe a can na iya cin abincin tak'arasa magana ciki shagwa6a.
"Da sauri Habeeb yatashi yadauko mata mayafinta suka fice a parlour suka iske Hannah kishingid'e tasha make-up tafito amarya sak cike da farin ciki ta rungume Haleesa cikin zolaya ta dubi yaya Habeeb tace Daddyn twins ina kwana"?
''Dariya Habeeb ya yi ke kuma twins ki ke mana fata"?
"Gyad'a kai Hannah ta yi yayinda Haleesa ta tabe baki had'e da cewa kwaji da shi Habeeb yace wai ina Mus'ab ne ko har yafita ne"?
"Murmushi Hannah ta yi tace yana kitchen watakila karar TV yahanashi jin muryarku.
''Zaro ido Habeeb ya yi me yake yi a kitchen"?
Breakfast yake had'a mana Hannah tafad'a had'e da kallon Habeeb.
Kyalkyalewa da dariya Habeeb da Haleesa suka yi mik'ewa Habeeb ya yi yanufi kitchen d'in yana mai cigaba da dariya tun kafin yak'arasa shiga kitchen ya hango Mus'ab yana tsame chips daga mai cike da tsokana Habeeb yace ango kasha k'amshi gaba d'aya ka d'umama gidanan da k'amshi.
"Mus'ab yajuyo ya dube Habeeb ya d'aure fuska uban me ka zo yi da sanyin safiya a gidana Lamido"?
"Habeeb yak'ara kwashewa da dariya me da wuk'a angon kitchen abincin amarya na zo ci abun mamaki sai na tararrada ango a kitchen amarya na hakince a parlour
[28/12 1:46 pm] aliyujeeddah: Wannan kuma wane irin Sabon system ne"?
"Mus'ab ya gallawa Habeeb harara cike da takaicin yace bansaniba yanzu kafad'a min muqasudin zuwanka gidana karka manta al'adace friends suna yi wa ango rakiya darensa na farko a gidansa sama da k'asa mun nemi ka muka rasa khaleel yakira ka a waya da ka d'aga kira me kace da shi"?
"A yatsine Habeeb yace cewa nayi da shi ni yayan amarya ne ba abunda zan je yi a gidanta.
''Hum.....To yanzu gayamun me yakawo ka"?
"Abincin ango na zo ci ko ba za'a bani bane"? Habeeb yak'arasa magana yana dariya murmushi Mus'ab ya yi yace ka dai anyi d'an iska wallahi karka manta Lamido ni fa in-law d'inka ne bai dace kana mun iya shege ba.
Habeeb yak'ara kyalkyalewa da dariya Haleesa ta dubi Hannah baki bud'e tace kai kamar fa sautin dariya yaya Habeeb nakeji"?
"Tabe baki Hannah ta yi ba kama bace shine watakila yana yi wa my love dariya don yaganshi a kitchen.
"Haleesa ta yi dariya tace in haka ne bari nima na leqa naga dariyar yaya Habeeb kinsan Allah idan yaya Habeeb yana dariya jin nake kamar na hadiye shi saboda yanda take mugun k'ara masa kyau. tak'arasa magana had'e da mik'ewa tanufi kitchen girgiza kai Hannah ta yi tace Allah ya yi miki sauki Haleesa ta mik'e da kyar tabi bayan Haleesa.
Kai,kai Kai, Haleesa tafad'a had'e da zaro ido me nake shirin gani Mus'ab yaushe ka zama chef"?
"Kafin Mus'ab yabata amsa Hannah tariga shi ta hanyar cewa ka ga my love kyallesu kawai ae gwara kai da wani tak'arasa magana had'e da boyewa bayan Mus'ab.
"Katuwa harara Habeeb yadanna mata da wa ki ke"?
Mus'ab yace da kai take ko akwai abunda za ka yi"?
"Wallahi yanzu ina lakad'a mata duka ba ruwana da zamanta amarya, kuma ba abunda za ka iya.
"Mus'ab ya ja tsaki yace za ka iya saboda ba hankali ne yawadace ka ba don haka ja matarka Ku koma parlour duk abunda Ku ke so zan had'a mu Ku ni dai fatana mu rabu lafiya da kai batare d kata6a min lafiyar mata ba.
"Haleesa tarik'o hannun Habeeb zo mu koma parlour my handsome Don ko yak'i ko yaso ya zame masa dole yadafa yabamu, mu ci.
Habeeb ya yi dariya yace haka ne fa my Leesa kinsan Mus'ab kwarare ne a faggen girki cikin dariya suka fice daga kitchen d'in.
Akan 3 seater suka zauna k'afafunta ta daura a cinyoyinshi yana ja yatsunta a hankali Mus'ab yashigo d'auke da k'aton tray a tsakiyar rugs carpet ya ajiye tray kallo d'aya ya yi musu yadauke kai yajuya kitchen ya kwaso plate yayinda Hannah take rik'e da flask mai d'auke da ruwan zafi, Mus'ab ya dube su yace in kun ga dama Ku sauko k'asa Ku yi wa kanku serving Habeeb yarik'o hannun Haleesa sauko k'asa my Leesa na yi miki serving mak'e kafad'a ta yi banacin.
"Habeeb ya yi k'asa da murya haba! Leesa ke fa ki ka ce in mu zo gidanan za ki ci abincin shine dalilin da yasa k'afata ta tak'o gidanan Dan Allah ki daure ki ci ina jin tsoro kada yunwa ta ta6a mana babynmu.
"A shagwa6e tace indan naci amai za yi ni yanzu d'an wake ko shinkafa da mai da yaji nakeso cin.
''Mus'ab ya kalli Hannah suka kyalkyale da dariya Habeeb ya galla musu harara yace lalura ce bata wuce ta hau kan matarka ba.
"Mus'ab yace katashi kashiga kitchen domin zama bai sameka ba.
"Tabe baki Habeeb ya yi to ae ni ba d'an daudu bane irinka yak'arasa magana had'e da dauko phone d'inshi ya kira Ammi ya fad'a mata ta ta yi wa Leesa d'an wake da shinkafa da mai da yaji Bala zai zo ya kar6a yakawo mata gidan Hannah.
"Yana gama waya ya yi wa Mus'ab gwalo had'e da cewa shiga kitchen sai Ku Mus'ab marasa dabara Sabon babi na fira suka bud'e sai sautin dariyarsu ka ke ji a haka Bala yashigo yasame su ya ajiye foodflask d'in hannunshi yanemi kujera ya kame Haleesa nagani d'an wake kamar za ta yi hauka nan take ta zuba a plate tashiga ci shinkafa kuma ta ajiye sai da rana ta cin.
"Anan Habeeb yabar Haleesa suka fita shi da Mus'ab da Bala sai misali k'arfe _8:30pm_ Habeeb ya dawo d'aukar Haleesa.
"A washe gari Habeeb da Haleesa suka koma Abuja suka bud'e Sabon shafi na soyayya kamar za su cinye junansu, in fita Habeeb ya yi suna manne da waya idan kuma ya yi tafiya adaddafe yake gama abunda ya je yi yadawo, musanman yanzu da cikin Haleesa yashiga wata na 6 ya yi girma sosai.
Haleesa na kwance akan 3 seater Imaan na matsa mata k'afafunta Habeeb yashigo yana waya hannunshi yasa yadauke kanta ya zauna ya aza kanta bisa cinyoyinshi yana gama waya ya kira sunanta Leesa!
"Na'am
"Tafiya Lagos yakamani amma ina gani ba zan wuce _1 week_ ba.
"Bata fuska Haleesa ta yi kamar za ta yi kuka ni gaskiya my handsome Don banaso wannan tafiya da ka ke yi sanin kanka ne duk lokacin da ka yi tafiya ba wani baccin kirki nake yi ba.
"Ni ma Leesa ba so tafiya nan nake yi ba banida yanda zan yi ne ba zan wuce _1 week_ ba zan dawo kinji"?
"Shikenan Allah yadawo da kai lafiya.
"Ameen Leesa naa.

_3 months later_
Haleesa tana kitchen tsaye hannunta rik'e da wuk'a tana gyara kankana Habeeb yashigo ya rungumeta ta baya ya zura kanshi ta kafad'arta yabata peck a kumatu mai ciki sarkin kwad'ayi me ake had'a mana ne"?
"Fruits salad ne tun safe na tashi da kwad'ayinsa.
Zare jikinshi ya yi daga nata ya yi tsalle ya haye kitchen cabinet d'an Sam mini kankana nan naganta jajir da alama za ta yi zak'i harararshi ta yi tadauki yanka guda d'aya tasaka mishi a baki yana tauna yana lumshe idanu.
"Haleesa tace da zak'i koh"?
Gyad'a kai ya yi eh! Saida kin fita zak'i ina gani zak'in hannunki ne ya shafe ta shiyasa ta yi zak'i.
"Girgiza kai ta yi had'e da murmushi tana gama had'awa tasaka ice block Habeeb yadauka mata, bowl d'in suka nufi parlour in tayi spoon 1 tasakawa Habeeb suna gama shan fruits salad marar Haleesa tafara murd'a tun tana cize lebb'e sai gashi tadawo wash..... Wash... Bayana marata a rikice Habeeb yad'ago ta Leesa ko haihuwa ne"?
"Da kyar Haleesa tace ita ce saboda randa na ke a duniya banta6a jin masifar ciwo irin wannan ba.
"Da k'arfi Habeeb yashiga kwadawa yarinye kira sai gata tashigo Imaan tana biye da ita ki je bedroom d'in Leesa akwai trolley brown colour ki bud'e ki dauko kayan baby za mu tafi hospital.
"Cikin d'an k'ank'anin lokacin sai ga yarinye tadawo d'auke da medium size na trolley Habeeb yadauki Haleesa yafice tun kafin yak'arasa compound yashiga kwallawa Bala kira yi maza Bala ka dauko mota da gudu Bala yanufi parking lot yajanyo mota Habeeb yasaka Haleesa ya dubi yarinye yace kin saka kayan a mota"? Eh nasaka a seat d'in gaba.
"Shikenan ki d'auki imaan ku koma cikin gida sai mun dawo
Bala yafizgi mota yanufi gate maigadi ya bud'e musu gate suka fita.
_Some hour's later_
Haleesa tasauka lafiya tasami bouncing baby boy mai kama da Habeeb, farin ciki wurin Habeeb ba kama hannun yaro bayan drip d'in da aka sa ma Haleesa yak'are akayi discharged nata suka yo gida, washe gari suka bi flight zuwa Yola ranar suna baby yaci sunan mahaifin Habeeb Abdulmajeed suna kiranshi da Haleel.

_6 years later_
Chapter 94 · 0% Book details