← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 95

Sashe 26

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tsawon lokacin Ammi da Zainab suka share suna kallonta daga, bisani Ammi ta nunata da yatsa cikin murya mai cike da gargad'i tafara magana ke! Haleesa karki mayarda mu tsofafi banza mana a gaban matar nan kika ce kin amince da aure d'ata, a bayanta idota za ki dawo ki ce bakya sonshi ke tsoro shi kike ji to in ma bacci kike yi kiyi gaggawa ki falka domin wannan shirme naki mu bara mu dauke shi ba ai bakin alk'alami yariga yabushe ke kika amsa da bakinki kina sonshi ba wani ne ya yi miki dole ba kowa yana miki murna Habeebu yatafi ga kuma wani Habeebu yadawo, shine za ki tsiro da wani sabon tsirfa to ahir d'inki babban farin cikin mu Haleesa kindawo da walwala da farin cikin da kika rasa birjirewa wannan aure tamkar kinyi butulci da musaya da Allah ya yi miki kuma karke sake na 'kara jin wannan zance yafito daga bakinki, saboda ina tausaya miki in Baffa ki ya ji wannan tatsuniya ba zai yi miki da kyau ba.
Haleesa ta rushewa da kuka tace ni fa na amsawa mommy ne kawai don ina ji kunyar na dube tsabar idonta nace banaso gudan jininta, amma azahirin gaskiya bana sonshi kuma bana fatar ya maye min gurbin yaya Habeeb nariga nasakawa raina narasa yaya Habeeb rashin na har abada tak'arasa magana had'e da rushewa da wani sabon kuka.
Ammi ta girgiza kai tace kin yi wauta Haleesa da kika amsawa Hajiya Hindu kinaso d'ata, a gaban baffanki domin shi mutum ne da bayaso magana biyu don haka ki rungume 'kaddara sai ki yi 'ko'kari ki danne zuciyarki tafara sonshi Ammi na'karasa zance ta tafice daga d'akin tabar Haleesa da Zainab kowane su da abunda yake sa'kawa a ranshi, Zainab tarik'o hannun Haleesa ta yi k'asa da murya Haleesa karki yi haka ya alkhairi yana binki ke kuma kina neman ki guje masa a tunanina za ki fi kowa Murna da farin cikin, shigowa wannan Habeeb d'in a rayuwarki, da k'arfi Haleesa tafincike hannuta daga rik'o da zainab ta yi mata cikin k'unar zuciyar tace da kesan waye Habeeb Lamido da baki furta min wad'anan kalamai Zainab ta tabe baki daga bisani tace ta za'ayi nasan waye shi batare da kin sanarda ni ba"?
Haleesa taja gwaro numfashi, Habeeb Lamido mugu ne bashida tausayi shine mutumin da driver shi ya watsa mana ruwan kwatame shekaru biyu da suka wuce ya kuma zabga min mari har gudu biyu.
A firgici Zainab ta zaburo idanu bud'e cikin sark'ewar halshe tace I can't believe kina nufi mai siffar labarawa shine Habeeb Lamido"?
Kwarai kuwa shine kuma ba wannan ne kadai had'uwa ta da shi nan take ta kwararu wa zainab had'uwarta da Habeeb da kuma irin furucin da ya yi akanta, tacigaba da cewa ya kike tsanmani zamanmu zai kasance"?
Zainab ta yi ajiyar zuciyar tace dama haka tasha faruwa k'iyayya ta rikid'e ta koma soyayya ni dai gaskiya ina supported d'in wannan al'amari Allah yasanya alkhairi wata k'atuwar harara Haleesa ta gallawa zainab yayinda zainab ta kwashe da dariya ta mik'e tsaye cikin sigar tsokana tace sai da safe Mrs Habeeb Lamido Haleesa ta kai mata duka tafice da gudu cikin yanayi na jimami Haleesa ta koma ta zauna ta rafka tagumi hawaye masu cike da k'unar zuci suka wanke mata fuska.

```BAYAN KWANA BIYU ```

Yammaci ne sakaliya yanayi gari kamar akwai hadari sai iska akeyi mai matuk'ar dad'i gaske, madam Hindu na kishigid'e a "parlour ta hannuta rik'e da newspaper Habeeb ya yi sallama yashigo yanemi kusa da ita ya zauna kallo guda za ka yi masa ka hango tsantsa damuwa da take shinfid'e a fuskarshi, cikin kulawa madam tajuya wurinshi hannunshi ta rik'o me ke faruwa ne son naga kamar kana cikin damuwa"?
Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba daga bisani ya numfasa kamar mai ciwo hak'ora yace "nothing mom"
Sam madam bata gansu da amsa da yabata domin tadana yak'ini musanbabin damuwar tasa, duk bai wuce zance aure ita ko "this time around ba za ta d'aga masa k'afa kawai sai tayi murmushi tacigaba da cewa ina fatar wannan shiri da ka yi na tafiya gidansu Haleesa ne in baka mata ba yau ne muka yi alqawali da kai za ka je"?
"Habeeb ya lumshe ido game da 'kan'kame yatsun hannu mom ya yi k'asa da murya yace "please mom ki d'auke min tafiya nan bara iya ba tun da na amince da aure banga wani amfani zuwa na ba yak'arasa magana tamkar zai fashe da kuka.
"Madam ta yi murmushi had'e da cewa haba Habeeb bansanka da magana biyu ba naga cewa tuni mun gama wannan zance me yasa za ka dawo da hannu agogo baya, katashi katafi Allah ya yi maka albarka.
"Ba yadda Habeeb ya iya dole ya mik'e tsaye cikin sanyi murya yace sai nadawo mom"
Adawo lafiya ka gaida ta batare da yak'ara furta uffan yafice daga parlour yayinda madam ta bishi da kallo.
Yana fita Bala P'A ya shek'o da gudu yanufo wurinshi yace "Boss fita za mu yi ne"?
A kasalance Habeeb yafurta kalma "eh Bala yanufi "parking space yajanyo mota kirar "mercedez benz c class" ash colour kafin Bala ya bud'e masa k'ofa ya bud'e da kanshi yashiga Bala yaja mota maigadi yabud'e gate suka fice daga gidan.......

Jeeddah Aliyu🌹
[30/09 2:39 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love story_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

*Dedicated to Shehu Aliyu family's*

Note:- _Alhmdullilahi naji sauki sosai ina mik'a godiya agareku masoya na na gode da addu'arku Wanda suka kirani da Wanda ma basuyi min yajiki ba na gode sosai Allah yasaka da alkhairi na gode_

```56```
Chapter 26 · 0% Book details