← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 95

Sashe 15

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Late Alhaji Majeed lamido haifafe garin Adamawa jahar Yobe, ne sanane mai kudin da yayi tashe tun duniya tana zaune qalau, marigayi Alhaji majeed lamido ya mutu yabar tarin dukiya da 'ya'ya bila adadin rankatakan family majeed lamido babu talaka domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga gurin mahaifinsu Muhammad lamido yana d'aya daga cikin 'ya'ya marigayi majeed lamido mahaidiyarshi su biyu kacal ta haifa tarasu, a lokacin da majeed lamido ya mutu aka rabawa 'ya'ya shi tarin dukiyar da yabar musu a matsayin gado tun lokacin da aka raba musu gado muhammad yaduk'ufa wurin juya dukiyar shi ba abunda yasaka a gaba sai neman kudin Wanda a cikin d'an k'an'kani lokacin ya gawurta yayi fice ya yiwa sauran 'yan uwanshi zarar, Muhammad lamido ya mallaki "companies dama arewa da kudanci Nigeria yana da gidanje sayarda man fetur bila adadin shine mamallaki Majeed Lamido Airlines yana da hannu jari da dama a companies na k'asashe waje yana da gida a Abuja da Lagos tsanani neman kudin Muhammad yasa yad'auki dogon lokacin batare da ya aje iyalin ba, burin Muhammad shine ya aure mace mai matuk'ar kyau garin neman duniyarshi ya hadu da Hindu a Egypt tun daga lokacin da daura idanushi akanta yadauki son duniya yadaura mata kasancewarta kyakyawa Hindu ita ce 'ya ta farko wurin iyayyeta sai k'annanta biyu maza Ahub da Ansar da farko da ta gabatarda Muhammad a wurin iyayyeta k'in amincewa sukayi da shi acewarsu bak'ar fata ne saida takai ruwa rana da su sannan suka barta ta aure Muhammad, saida Hindu tayi shekara bakwai da aure sannan tasami cikin Habeeb cikin Hindu na da wata tara chin ta haifi Habeeb daga ita har Muhammad suna matuk'ar son Habeeb tamkar numfashinsu suna nuna masa gata shiyasa Habeeb yatashi a sagarce babban matsala Habeeb rashin magana da farko iyayye shi sun dauka ko kurma ne sai daga baya suka fahimce cewa, tsabar miskilanci ne yayi masa yawa, Habeeb bashida, aboki koda yaushe za ka tararda shi manne da mommy shi ba, abunda Habeeb yasani daga Daddy shi sai mommy shi duk wannan gata da Habeeb yasamu Muhammad da Hindu basuyi sake da karatunshi Habeeb yanada 10yrs a duniya Hindu tak'ara haihuwa tasami 'ya mace mai suna Hannah.
Habeeb na gama primary school Muhammad yatura shi Egypt wurin iyayyen Hindu yayi karatun secondary school d'inshi a lokacin da ya gama secondary school yadawo Nigeria D'an zaman da yayi a Adamawa kafin yatafi university shak'uwa mai 'karfi tashiga tsakaninshi da salma 'yar k'ani Alhaji Muhammad da suke uba d'aya, salma ta girmewa Habeeb da kusan 3-4yrs duk lokacin da salma taga Habeeb sai tayi ta tsokanarshi ta hanyar kira shi da suna kurma ko mai idon magge tun Habeeb baya kulata har yadawo bashida friend in ba salma ba tsanani sha'kuwar da Habeeb yayin da salma ta karanci halaye Habeeb shiyasa k'awance su yadaure, a lokacin da Alhaji Yusuf majeed lamido zai tura salma da''yan uwanta karatu a London salma na bawa Habeeb labari shima yayi tsalle yadira yace sai _Oxford university London_ zai yi karatun degree d'inshi kaitsaye Alhji Muhammad ya amince Habeeb da salma da kuma saura 'yan uwata suka d'aga London.
watani suka wuce shekaru suka shud'e cikin nasara Habeeb da salma suka kamalla karatun degree d'insu suka dawo gida Nigeria.
Yayinda Muhammad ya mik'a ragamar alhakin kula da dukiyarshi a hannu Habeeb, tun daga lokacin Habeeb yadawo tamkar ya shi baisan komai ba sai neman.
Kwatsan Alhaji Muhammad yatashi da rashin lafiya kwanasa biyu a hospital yarasu Hindu da Habeeb sun shiga tashin hankali, saida basuda yadda za suyi illah suyi hank'uri gani yadda aiyuka suka yiwa Habeeb yawa yasa Hindu take tayasa, kula da wasu _companies_ nasu gudun kada su duk'ushe sunan madam yasamu asali ne a duk lokacin takai ziyara a company sai kaji _worker's_ suna kiranta da madam shikenan sunan yabita.
Madam Hindu mace ce mai sauki kai ga ri'kon Addini, tanada matuk'ar tausayi tana tsanani son 'ya'yanta musanmman d'an gaban goshi Habeeb akanshi za ta iya 6atawa da kowa shima Habeeb abin haka yake a wurinshi yana matuk'ar girmama mommy shi yana so duk abunda takeso yana taka tsan-tsan da duk wani abunda zai 6ata mata rai.....
[02/09 6:59 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```37```

Habeeb farin ne tass skin d'inshi har wani ja-ja takeda yanada tsawo sosai har wani d'an rangwafawa yayi fuskarshi, na dauke da dogon hanci yanada manya idanu eye's ball d'inshi kamar na magge sumar kanshi bak'a wulik yanada saje a gefen kumatu shi sai wani d'an siriri geme kamar na _2face_ duk lokacin da yayi murmushi kumatushi da k'asan geme shi na lotsawa{dimple} Habeeb bashida fa'ara ko kad'an koda yaushe fuskarshi a murtuk'e take da kyar ka ga Habeeb ya yi dariya, shiyasa mutane da dama suke masa kallon a matsayin mai girman kai.
Matsala ta farko da salma tafara fuskanta tun dawowarta _Nigeria_ shine rashin takameme mijin aure mutum d'aya ke so ta da aure shine salis saida matsalar salis shaye-shaye ba abunda baya sha a dangin kayan maye, duk da kasancewa salma kamila zama London bai chanza mata, kyawawa dabi'u ta ba salma akwai addini Sam bata wasa da lukutan sallah salma fara ce irin farin Fulani Adamawa gajeriya ce batada tsawo ko k'adan akwai hips da manya boobs tanada k'iba sosai wance mutane da dama suke tsanmani ko salma bazawara ce batada hayaniya akwai hank'uri ta iya zama da mutane, duk da wad'annan kyawawan halaye na salma amma tarasa dalilin da yasa mijin aure yagagareta.
A dalilin wannan matsala ta salma yajanyo mata matsananci bak'in jini a wurin iyayyeta daga haj khareema har Alh Yusuf kullum cikin yi mata gorin suke shiyasa k'annanta suka rena ta.
Salma kwance a room d'inta abin duniya yataru ya yi mata yawa ita kanta a yanzu tana buk'ace da abokin rayuwa a halin yanzu takai mataki da ba za ta iya kare kanta dalilin da yasa wata rana ta kira Habeeb domin yabata shawara cikin shasshekar kuka ta kwashe irin wulaqanci da take fuskanta, daga wurin haj khareema da k'annanta tafad'awa Habeeb, har ta dasa aya Habeeb na kallonta daga bisani yasauke ajiyar zuciya cikin sigar rarrashi yafara magana, hank'uri za ki yi aunty salma komai ya yi farko yanada 'karshe da ina da magani magance wannan matsala taki da tuni na nemo shi duk da haka zan cigaba da tayaki addu'a har Allah ya kawo miki k'arshe wannan matsala salma tace na gode Habeeb, dama na kira ne domin na sanarda kai zan amince na aure salees saboda nima a yanzu ina da bu'katar aure salma ta'kasara magana had'e da rushewa da kuka da sauri Habeeb yarik'o hannuta, yace please aunty salma karki amince da aure salees saboda hakan zai iya haifar miki da matsala Sam bai dace da ke ba.
To Habeeb ya zan yi"?
Hank'uri za ki yi salma"
Ba zan iya ba Habeeb hank'uri na ya'kare banaso na jefa kaina a halaka, a kullum shekaru na 'Kara yawa suke in kuma kana gani salees bai dace da ni ba to kanemo min mijin aure.
Habeeb yasauke gwaron numfashi tsanani tausayi salma ya kanainaye shi, cikin rashin mafita yace shikenan aunty salma ki bani _time_ zan kawo miki Wanda yafi dacewa da ke, salma tayi murmushi had'e da cewa shikenan Habeeb na gode da wannan taimko naka agareni.
Dare ya yi Habeeb yakasa bacci sai faman juyi yake tsanani tausayi salma yahana shi bacci, ya kuma rasa Wanda zai nemo ya aure salma, tsawon lokacin yadauka yana nemawa salma Mafita daga karshe yasaki murmushi.
Washe gari kaitsaye Habeeb yanufi gidan su salma yana shiga gidan ya hadu da ita a compound za ta fita, bayan sun gaisa yace aunty salma na nemo miki miji amma bansan ko za ki amince da za6i na salma tayi murmushi tace Habeeb kenan ae ni na gaya maka banida za6i......

````DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[04/09 3:34 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [04/09 8:20 am] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```38```
Chapter 15 · 0% Book details