← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 95

Sashe 85

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

~~Ta bud'e k'ofa tafita da mugun mamaki Habeeb ya bita da kallo ya mik'e da sauri ya bi bayanta a parlour yatarar da ita ta kifa kanta a hannun kujera tana shasshek'a kuka a rikice ya furta _Maryam I'II call you later_ batare da ya jira jin abunda Maryam za ta fad'a ba ya yi hanging up jikinshi na rawa ya zauna kusa da ita ya rungumo kafad'arta, tashiga ture shi in tears tafara magana _don't touch me kai mayaudare ne yanzu nan ka gama tsara ni kana fad'ar I'm the only woman you love shine don wulaqancin da kwarewa da yaudara in front of me kana cheating nawa_
Zufa ta soma tsattsafo wa Habeeb in shock yake kallonta da kyar ya tattaro yawun bakinshi ya yi nassara lalla6o kalma da zai furta mata Leesa please karki d'aga mun hankali akan abinda bakida tabbacin akansa ki yarda da ni nothing between us banta6a son Maryam ba kuma bana tunanin zan so ta.
"Ta galla masa harara baka sonta amma naganka kana, tsotsar bakinta.
Zaro ido yayi karki yi mun sharri Leesa Maryam fa Qanwata ce Kamar Hannah take a wurina me zai kaini da bakinta"?
Cikin murya ta kwashe lokacin da taganshi da maryam a Sokoto yana busa mata ido Wanda har tayi tunani sumbatar ta ne yake yi.
"Dariya sosai Habeeb ya yi gani yadda yake dariya yasa tafashe da kuka mai k'arfi gaske da sauri ya hadiye dariyarshi ya rungume ta yana bubbuga bayanta cikin rarrashin ya sanarda ita abinda yafaru tsakaninshi da Maryam.
"Ba wani photo boyfriend d'inta da za ta nuna maka sau nawa tana kashe min gargad'in akanka.
"A da kenan amma a yanzu yayanki ya yi nassara saye zuciyarta Leesa Maryam yaya salman takeso, saidai Hajiya khareema tak'i amincewa a cewarta 'yarta ba za ta aure talaka ba.
Mamaki ne lullu6e ya Haleesa tad'ago daga jikinshi yaya salman fa kace"?
Gyad'a mata kai yayi yace ni kaina lokacin da ta gwada min pic nashi nayi mamaki, sai take fad'a min wai d'ikin takai shagonshi anan suka had'u har suka qula soyayya da na sanarda ita cewa yayanki ne sosai kunya ta lullu6e ta tadinga rok'ona kada na sanarda ke.
Da kaina naje gidansu wajen Hajiya khareema na rok'eta tabar Maryam ta aure Wanda takeso tun da ta hak'ura da ni da kyar na shawo kanta ta amince a halin yanzu Maryam in-law d'inki ce don haka kidaina kishi da ita Habeeb Lamido naki ne ke kadai.
Yak'arasa magana had'e da d'ago fuskarta halshenshi yasa ya tsotse hawaye kumatunta banaso na k'ara gani hawaye akan wannan kyakyawar fuska.
"Ta yi murmushi had'e da 6oye fuskarta a k'irjinshi.

_some hours later_

Habeeb yana kwance akan kujera Haleesa tana tsaye wajen k'afafunshi ta na Jan k'afafun nashi da k'arfi tana magana cikin shagwa6a ni fa ba zan
yarda ba sai ka goya ni katashi ka goya ni nace tak'arasa magana cikin ihu.
"Habeeb ya mik'e zaune yatsunshi yasa toshe kunnenshi yana dariya ta k'asan ido yake kallonta yace Leesa please ki barni na huta mana ni narasa dalilin da yasa ki ka zama stubbornly"?
"Kukan shagwa6a tasa mishi babu shirri ya duk'a ta dalle bayanshi yadinga zagaye parlour da ita suna kyalkyalar dariya abinsu rayuwa ta yi musu dad'i a koda yaushe za ka, tararda su manne da juna ko kitchen Haleesa tashiga Habeeb yana rungume da ita har ta kamalla musu girki, ita kanta Haleesa wasu lokuta tana mamaki yadda Habeeb Lamido yake haukar sonta.
Cikin kwanaki 3 kacal so da shak'uwa mai k'arfin gaske yashiga tsakaninsu, har basa son dai-dai da 1 second su nisanta da juna.
Chapter 85 · 0% Book details