← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 95

Sashe 48

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

~~Ya dank'i hannunta kaitsaye yanufi dining table ya ja kujera ya zaunar da ita, yayin da Haleesa ta ke rarraba idanu takasa boye mamakinta
ya bud'e food flask yadauki plate ya zuba white Rice saida ya yi kusan cika plate ya zuba tomato stew akai ya kuma lullu6e stew d'in da had'in con slow ras-ras gaban Haleesa yafadi sakamako kwalba "Bama cream da taga yadauko ya dube ta ya sake haske ta da tsadade murmushi spoon 4 ya zuba na Bama cream ya ja kujera da ke facing d'inta ya zauna yana mai cigaba da murmushi mugunta k'amshin Bama cream kadai da Haleesa tashak'a yafara hautsine mata 'yan hanji tashin zuciya ya turnuke ta, hawaye suka cika mata idanu saboda ta hal6o mugunta da Habeeb yakeso yi mata
Tana kallo yana juya abinci da spoon ta yadda Bama cream zai gauraye abinci yace _yauwa Amarya Habeeb Lamido yau da kaina zan yi feeding naki kinsan me"?_
Bai jira jin ta bakinta yacigaba da cewa banaso sweetheart ta zargeni da rashin baki kulawa, shiyasa na yi decided yau da kaina zan cika miki tumbinki
Hawaye suka wanke mata fuska cikin tashin hankali tace _yaya Habeeb banaci Bama cream amai yake sani ka tausaya min karka tilassata ni cin shi_
Tak'arasa magana tana mai goge hawaye da bayan hannunta
Ya zare mata ido ya wani murtuk'e fuska Allah ba ki isa ba kice bara ki ci abunda nakeso tun da kika shigo rayuwata bakida za6i dole sai abunda na za6a miki yaciko spoon da abinci yanufi bakinta _oya bud'e baki_
Yaya Habeeb banaso zai sakani amai tafad'a cikin marairaice murya
Ranshi a b'ace ya galla mata harara ya mik'e ya dank'o bayan wuyanta za ki bud'e bakinki ko sai na tsinka miki mari
Haleesa tak'ara rud'ewa _wayyo Allah wuyana you're hurt Me yaya Habeeb please have mercy on me_
Ba zan taba tausaya miki saboda ke kika fara Shiga gona ta, alfamar d'aya zan miki ki ci abinci nan
To ka sakeni zan ci
Yasake ta ya koma ya zauna spoon d'aya yabata tafara kakari Amai ke! Karki sake ki yi min amai anan wuri yak'arasa magana cikin shouting"
Tsanani tsoro ya lullu6e ta batasan lokacin da ta hadiye abincin tsabar mugunta irin na Habeeb sai yaciko spoon yadank'ara mata a baki, a wahalce ta ke hadiyewa
Yaya Habeeb zan sha ruwa tafad'a cikin rawar murya
Mugun kallo ya watsa wuta za ki sha ba ruwa ba dallah! Malama bud'e baki saida ta cinye fiye da rabin abinci sannan ya kyale ta tashi ki b'ace min da ganin in yaso ki je ki amayar da 'yan hanjinki ba abunda yadame ni Burina yacika na daura miki abunda bakyaso wannan kad'an daga cikin hukunci da zan dinga yi miki a duk lokacin da kika karya mini doka tashi mana yadaka mata tsawa ta mik'e a firgice ta kwasa da gudu tanufi bedroom d'inta agigice ta afka bathroom tafara kwara amai, saida ta amayar da abinci da taci duka ta cire kayan jikinta tasakarwa kanta shower tsawon lokacin ta d'auka ruwa na sauka akanta ta kashe shower ta daura towel tafito ta zube akan bed tafashe da kuka mai cike da k'unci _me na yi wa wannan d'an taliki ya za6i ya dinga kuntatawa rayuwata"?_
_ashe dama haka rashin so yake"?_
Wani irin ciwo kai yarufe ta da kyar take iya bud'e idanuta
Ta mik'e zaune ta share hawaye fuskarta ba komai Habeeb Lamido zan cigaba da yi maka biyayya akwai lokacin da zan ci riba biyayya da na yi maka tun da narasa yaya Habeeb nasan na yi bankwana da farin ciki
Ta 6angare Habeeb yana ganin Haleesa tafice daga gudu ya ja tsaki yafara zance zuci, narasa dalilin da yasa a duk lokacin da na kalli yarinya nan nakan ji tsanarta na k'ara tasiri a zuciyata ya lumshe idanu mik'ewa ya yi yadauki Imaan suka fice daga gidan.
Chapter 48 · 0% Book details