← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 95

Sashe 6

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Habeeb yarik'o hannuta suka nufi gida, sautin kuka ta ne yafito da Ammi daga d'aki tana fad'ar to fitinaniya yau kuma da wace kika zo"?
Ammi na k'arasa fitowa daga d'aki tayi turus, faskarta d'auke da zalla mamaki tace iko Allah ashe tare kuke da ita kuka me take yiwa mutane"?
Yaya salman ne sanarda Ammi abunda yafaru.
yaya Habeeb sai cika yake yana batsawa yanufi bakin famfo yacika _bucket_ da ruwa yakai mata band'aki{bathroom} yasake shiga d'akinta yadauko mata zani ya mik'a mata, ta kar6a saida yaraka ta bakin k'ofar _bathroom_ sannan yadawo yajingina jikinsa da bango jin yakeyi kamar ya rushe da kuka Ammi tace ka ga Habeebu karka nemi ka d'aurawa kanka damuwa domin ba ga ni wannan mutum za ka yi ba mafi alkhairi a tare da kai ka lallashi zuciyarka.
Yaya Habeeb yad'ago ya kalle Ammi da jajaye idanu shi yace babban takaici na bai wuce yadda Salman yake k'ara tunzira ni yak'arasa magana had'e da nuna yaya salman da yatsa.
Yaya salman ya kyalkyale da dariya daga bisani ya tsagaita da dariyar yace Allah ya huci zuciyarka _my in law_ ni kaina da zan ga wannan balarabe da na tayaka dukansa.
Ammi ta tabe baki
inna mairo ce tayi sallama tashigo a rud'e Ammi tasaki murmushi had'e da cewa zainabu takai miki rahoto koh"?
Inna mairo tace bari kawai fatee wallahi da zainabu tasanarda yadda abun yafaru baki ga yadda hankalina yatashi kai wannan mai siffa larabawa bashida imani Allah yasaka miki Haleesa.
Ammi da yaya salman sai faman dariya inna mairo sukeyi gani yanda ta tak'ark'are tana fad'a Haleesa tafito daga _bathroom_ jikinta lullube da d'an kwali _uniform d'inta_ har wani Jan k'afa takeyi ita dole sai tanuna ta maru, a hanzarce yaya Habeeb yanufi wurinta, yarik'ota sai faman sannu yake mata inna tasaki salati tana tafa hannaye sakamako gani idanu Haleesa sunyi kwanci jini tace Amma wannan mutum rashin imani sa a baiyane yake so yayi ya makkata ki, to ta Allah ba tashi ba azzulumi kawai.
Haleesa da ke tsaye tana sharar hawaye sai faman gizo fuskar mai siffa larabawa yake mata, yaya Habeeb yace ki je ki saka kayanki babylove mu je _hospital_ a duba ki Ammi ta zaro ido tace wane irin hosfutal{hospital} Habeebu"?
Kai fa baka rabuwa da d'aukar dame magaji da nishi in banda tsabar tsirfa da ba kai wahala miye na zuwa _hosfutal_ {hospital} gishiri da ruwan masu d'an d'umi-d'umi za'a nema a gasa mata idon shikenan za ta Wartsake.
Yaya salman yak'ara kyalkyale dariya yace Ammi ba hosfutal ake cewa ba _hospital za ki ce_ Ammi ta gallawa yaya salman harara tace Ko ma menene akecewa banga amfani zuwa sa ba.
Haleesa tafito cikin shirita, har yanzu da raguwa kwanci yatsu mai siffa larabawa akan fuskarta yaya Habeeb yace Ammi duba idonta ki gani yadda yayi Ammi ta kya6e baki daga bisani tace dafin hannu ne Habeebu ba wani Abu ba da an gasa mata zai daina.
Yaya Habeeb ya girgiza kai yace ni dai Ammi nafiso mu je asibiti{hospital} Ammi tace Allah ya kiyaye hanya sai kun dawo yaya Habeeb yaja hannu Haleesa suka fice yayinda yaya salman ya Mara musu baya.
yaya Habeeb yashiga cikin gidansu yajawo Babur d'insa Haleesa ta d'ale yaja Babur d'in suka tafi yaya salman yabisu da kallo yana, dariya.
Duk yadda yaya Habeeb yaso su ga likita abun yaci turu saboda lokacin tashin likita aiki yayi dole yanufi wani 'karamin _clinic_ mai 'yar banza tsada bayan an duba ta aka rubuta mata magani, kusan duba takwas da d'ari biyar akayi chaji yaya Habeeb in da Allah ya taimaki Habeeb yana da 'yan kudinsa haka yafito da su ya biya had'e da kar6a magani suka fito daga _clinic_ d'in tausayi shi yayi bala'i kama Haleesa nan take ta ji wani sabon sonshi yana ratsa jinita.
ya tsaya wurin wani mai siyarda lemu da ayaba yasiya mata sannan suka nufi gida.....
[25/08 4:53 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```13```

Suna isa gida yabata magani tasha ya kuma d'iga mata wanda ake sakawa a ido, yayinda Haleesa sai shagwa6a take zuba masa, ya6are ayaba yasa mata a baki Haleesa ta sada kai k'asa tana ci ayaba a hankali, tana d'agowa ta ga yaya Habeeb ya tsura mata ido yana kallonta tamkar zai cinye ta, tasaki murmushi tace yaya Habeeb wannan kallon fa"?
Yasauke numfashi cikin yanayi na damuwa yafara magana, babylove wannan mutum yacuce ni kalli yadda ya6ata miki fuska yak'arasa magana tamkar zai yi kuka.
Haleesa tace kasaki ranka yaya Habeeb idanu ba ciwo suke min ba.
Ta ya zan saki raina babylove alhali idanu ki suna cikin wannan yanayi"? nayi alqawali duk ranar da idanuna suka ci karo da wannan bak'in azzalimi sai na d'auki munmuna mataki akansa.
Cikin rauni murya tace Dan Allah yaya Habeeb kayi hank'uri ka manta da wannan abu.
Shikenan babylove na hak'ura yafad'a had'e da Jan karan hancita yace ni zan koma shago, cikin sigar shagwa6a turo baki tace a'a yaya Habeeb ni banaso katafi yaya Habeeb yayi murmushi had'e da cewa kin ganki yarinya nan kinaso ki had'a mini _go slow_ a shago Haleesa tayi dariya tace to shikenan tashi katafi amma anjima za ka dawo koh"?
Tun da farin cikina naso ganina me zai hanani dawowa
Tsanani jin dad'i had'e da nishad'i suka lullube zuciyar Haleesa Habeeb ya mik'e yafita ta bi bayansa da kallo.

A kwana a tashi gashi har Haleesa ta kamalla karatu ta, yayinda iyayyensu sai faman shirya-shirye bikin aure su sukeyi, nan da wata d'aya za'ayi bikin burin Haleesa da Habeeb ya kusa cika.

Yammaci ne mai cike da sanyaye iska mai ni'ima bishiyoyi sai faman kad'awa suke suna busa iska mai dad'i gaske yayinda hadari ya had'a kayansa gabass Wanda hakan yake nuna cewa ko kowane lokacin ruwa za su iya saukowa, a cikin wannan yanayi ne Haleesa tafito daga gida Ammi ta aike ta gidan Delu dillaliya tana sanye da _combination_ na _paperless da atamfa red&yellow colour_ da hajib d'inta _red colour_ jikinta na fitarda 'kamshi turare _pink love_ ta yi matuk'ar kyau musanmman yadda ta k'awata fuskarta da murmushi ga kuma yanayi na iska da ke kad'awa sai kawai ta tsinci kanta cikin nishad'i, tana tafiya a hankali wannan d'aya daga cikin 'dabi'a Haleesa da kyar ka ganta tana tafiyar sauri shiyasa sa'idawa ke cewa ta cika yanga kaitsaye ta nufi bakin titi ta tsallaka, shagon su yaya Habeeb ta nufa saida ta lek'a ta ga yaya salman baya cikin shagon sannan tashiga wata budurwa ta hango zaune bisa farar kujerar roba, ta kasa ta tsare sai wani girgiza k'afa take yayinda Habeeb ke zaune bisa tela yana d'ikin Haleesa tasaki murmushi domin tagano mutumi nata ya yi tsiya da sallama tashiga shagon da sauri yaya Habeeb yad'ago ya wanke ta da murmushi, yace _o'oo my baby you look so beautiful muah_
Haleesa ta washe hak'ora kamar gonar auduga, tace _thanks my love_
Daga ina kike"?
Ammi ce ta aike ni gidan Delu shine nace ba zan wuce ba sai na na zo naga tauraro na.
Habeeb yak'ara fad'ad'a murmushinsa yace kai gaskiya kin kyauta babylove da ace kin wuce banga wannan kwalliya ba da kin gama da ni......

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU```

Jeeddah Aliyu🌹
[25/08 8:35 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [25/08 6:46 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```14```

Haleesa ta kyalkyale da dariya tace _umh yaya Habeeb kai dai baka rabo da abin dariya_
Budurwa da ke zaune tana jiran tsanmani ta yatsine fuska da alama tafara k'osawa da surutun Habeeb da Haleesa tace haba Habeeb wannan wane irin wulak'anci ne tun d'azu nake zaune a shagonan sai yawo da hankali kake min gaskiya ni nagaji.
Cikin yanayi na mamaki Haleesa ta juya wurin budurwa, tace dallah! Dakata malama an gaya miki shi bawa ki ne da in fara d'iki ba zai tsaya ya huta ba"?
Budurwa ta zaro ido had'e da cewa ke kuma baiwar Allah daga ina"?
Ba'a saniba Haleesa tafad'a tana murgud'a baki yaya Habeeb yana dariya yace kin ga kareema ki K'ara hank'uri bani nace ki jirani ba"? Insha Allahu ba za ki fita shagonan ba sai da kayanki.
Wane irin na'kara hank'uri Habeeb"? Kalli gari ka ga yadda hadari ya yi bak'i ga kuma unguwa mu da nisa
Haleesa ta tabe baki tace kinsan unguwa Ku da nisa wayace kika kawo d'iki anan"?
Yaya Habeeb na gani Haleesa na k'ok'ari tsokano masa fitina ya mik'e tsaye yarik'o hannuta ya yi k'asa da murya yace zo mu je na rakaki babylove kada Ammi ta ga kin dad'e
Haleesa ta yi murmushi tace yi zamanka yaya Habeeb ka 'karasawa wannan mayya d'ikinta, Habeeb yace _okay baby ki kula da hanya kuma karki jima saboda kinga an fara yayyafi da alama ruwa zai sauko_
Haleesa wance tuni ta juya tasoma tafiya tace to yaya Habeeb.
Tun kafin tak'arasa gidan Delu aka fara ruwa da gudu tashiga gidan Delu bayan ta kar6i aiki da akayi mata, har ta juya Delu ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar Haleesa ki dawo ki jira har ruwa nan su tsagaita sai kitafi ba don ran Haleesa yaso ba ta zauna har akayi kiran sallah magariba ruwan basu d'auke ba tad'ura alwala tayi sallah tana sallamewa bata tsaya yin doguwa addu'a ba ta mik'a had'e da yi ma Delu sallama tafita da sauri.........
[25/08 7:44 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```15```
Chapter 6 · 0% Book details