← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 95

Sashe 13

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zuwa wannan lokacin Haleesa ta zama 'yar gida yadda tasake da madam Hindu tamkar ta shekara da sanita, sai misali 'karfe 10:00pm madam Hindu ta kai Haleesa _bedroom_ d'in da za ta kwanta madam Hindu ta dube Haleesa fuskarta d'auke da murmushi tace Haleesa ga d'akin Hannah ki kwanta saboda nasan za ki fi sakewa anan fiye da nawa d'akin ki bud'e _wardrobe_ akwai _sleeping dress_ na Hannah kiyi amfani da su in kina bu'katar wani abu sai ki sanarda ni.
Haleesa tayi murmushi tace na gode mommy
"Madam Hindu tafad'd'a murmshinta tace miye kuma abin godiya Haleesa"?
Ni fa na d'auke ki tamkar 'yar da na Haifa ki kwata ki yi bacci don naga alama agajiye kike sai da safe ta'karasa magana had'e da juyowa Haleesa k'ofa, Haleesa tajuya wurin k'ofa ta Murza _key_ a hankali takarewa d'akin kallo tasauke ajiyar zuciya mai k'arfi gaske, ta bud'e _wardrobe_ta tsurawa Jarin kayan da ke ciki ido cikin zuciyarta tace mai kudi yaji dad'insa yanzu duk tuli tufafi nan na mutum d'aya ne _infact_ yarinya bata ma gida tana school amma ta tara wannan uban kaya, tabe baki tayi daga bisani tajuya _side d'in da jarin sleeping dress suke tad'auki wata cotton night gown_ tasanya tasauka mata har k'asa da alama mai rigar tafita tsayi nesa ba kusa ba, Haleesa ta yatsine fuska a zuciyarta tace in banda kar mommy ta ga nak'i bin umurni ta da ba abunda zai kai ni saka kayan wani, ta kashe wuta ta haye gado bayan tayi addu'a ta janyo _blanket_ ta lullube rabin jikinta sanyi Ac ya ratsata, ta lumshe idanuta ta tsunduma tunani yaya Habeeb yayinda hawaye suka ziraro mata ta gefe da gefe idonta suka sauka bisa wuyanta tsawon lokacin tadauka tana kuka had'e da tunani rayuwata da yaya Habeeb daga har bacci ya kwashe ta.

```WASHE GARI ```

Sai misali k'arfe 7:15am Haleesa ta falka da sauri tafad'a _bathroom_ tayi tsaye tana kallon tsarinsa daga bisani ta karanta rubutu da ke jikin kan famfo ta bud'e na ruwan sanyi tayi alwala tana gama sallah tsawon lokacin tadauka tana yi ma yaya Habeeb addu'a tana shafawa tak'ara komawa bisa gado, tacigaba da baccinta sai _around 11:20am_ tafalka batare da 6ata ba tashiga bathroom tayi wanka tana fitowa ta mayarda kayanta ta D'an Shafa _lotion_ had'e da goga 'yar _powder a face nata_ tadauki _body spray_ mai sanyaye k'amshi tafashe jikinta,ta bud'e k'ofa tafice madam Hindu ta tsinkaya zaune bisa katafare _dining table mai d'auke da 8 chair's_
Tana _breakfast_ Haleesa tak'arasa waje ta madam Hindu nagani ta tasake mata murmushi.......

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S```

Jeeddah Aliyu🌹
[29/08 8:10 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [29/08 6:56 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```® NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```32```

Haleesa ta duk'a ta gaisheta ta hanyar cewa ina kwana mommy"?
Madam Hindu ta mik'e tsaye ta rik'o Haleesa had'e da rungumeta tace lafiya qalau Haleesa ya bak'unci"?
Murmushi Haleesa tayi tace mommy ae na zama 'yar gida
Saida mommy tayi dariya sannan tace da kyau Haleesa 'yar gidana mommy haka nakeso oya zauna ki yi _breakfast_ Janet da ke tsaye a gefen kamar _bodyguard_ da sauri ta ja ma Haleesa kujera ta, zauna daga bisani tayi _saving nata_ ta ajiye mata plate d'in gabanta Haleesa ta dube plate mai d'auke da _chips da fried plantain with source_
A hankali Haleesa take ci abincin nata, tana korawa da _tea mai kauri gaske yaji Ovaltine_ Madam Hindu tariga ta k'arewa don haka ta mik'e tsaye tace Haleesa in kin gama ki same ni a 'karamin _parlour_
Kai kawai Haleesa tad'aga mata saboda ta cika bakinta da _fried plantain_ saida Haleesa ta ji tayi katt tayi gatsi had'e da hamdallah rabonta da taci abinci ta ji ta 'koshi irin haka tun kafin yaya Habeeb yarasu ta mik'e tanufi _parlour_ tararda madam Hindu a zaune hannuta ri'ke da _magazine_ tana dubawa Haleesa tanemi _one star_ ta zauna madam Hindu tad'ago ta dubeta tace har kin gama Haleesa"?
Haleesa tad'aga kai"
Baki da buk'atar komai"?
Haleesa tak'ara d'aga kai murmushi madam Hindu tayi tace har yanzu da raguwar bak'unta a tare da ke, Haleesa ta sada kai k'asa tana dariya _driven madam Hindu ne yashigo ya rusuna ya kwashe gaisuwa_
Madam ta amsa tana murmushi tace Aderwale ya akayi ne"?
Madam kudin _fuel_ na zo kar6i mota batada _enough fuel_
Madam Hindu tajuya wurin Haleesa tace Haleesa tashi ki je _upstairs bedroom d'ina ki bud'e brown colour handbag a gefen bed akwai kudi ki dauko min bundled d'aya_
Haleesa ta mik'e ta haura _stairs_ a hankali kaitsaye tanufi d'akin "with full confidence ta murd'a handle" kutt! k'ofar ta bud'e 'kamshin turare "intense man da yahadu da sanyi Ac yad'aki hancinta ta lumshe idanuta tsawon 20 second's ta dauka idanuta na rufe daga bisani ta bud'e su ta shak'i k'amshin yaratsa _brain nata_ tasauke ajiyar zuciya sannu a hankali tafara taka 'kafarta idanuta suka hasko mata _brown hangbag colour_ ajiye a gefen _bed_ har ta mik'a hannuta ta zuge zip d'in karaf idanuta suka hango mata shi yana kwance yayi "pillow da hannaye shi yana sharar bacci abinsa, da kallon yanayi baccinsa kasan yana cikin kwanciyar hankali, Haleesa ta murza eye's nata ta kuma rintsi su ta bude tak'ara kallon bed still yana nan yadda tafara ganishi numfashinta ya yi sama yadawo k'asa tadafe k'irjinta a zuciyarta tace tabbas idanu na ba 'karya suke ba babu shakka wannan Handsome ne ya akayi yasan nazo Lagos har yabiyoni"?
Wayagaya masa ina gidanan"?
Ya akayi naganshi akan bed d'in mommy yana bacci"?
anyya kuwa "Handsome ba aljani bane"?
Saboda in banda aljani ba Wanda zai aikata wadanan abubuwan....
[29/08 8:09 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```33```

Wani mashahuri tsoro ya lullube ta jikinta na rawa ta fara ja da baya garin baya-baya 'duwawu ta suka bige _dressing mirror_ kwalba turare yafado ta daki tile's tafashe a razane ya tashi zaune yajuyo ya tsurawa Haleesa _sexy eye's d'insa_ masu matuk'ar tsoratarda mai kallonsu, Haleesa ta'kara firgita ta zare ido kallon-kallon suke yi wa junansu _eye's ball's_ d'inshi masu kama da na magge sukayi masifar firgita Haleesa tsanani tsoronshi ya mamaye ta, tanaso tajuya ta arce na kare amma takasa cikin firgici had'e da gigita Haleesa ta bud'e bakinta ta dagargaje iya k'arfinta ta kwatsama ihu _wayyo Allah aljani wayyo mommy aljani mai idon magge a d'akinki_
Gaba d'aya gidan yadauki amo sautin muryarta tamkar da "microphone takeyi sa da sauri yasaka yatsu zara-zara yatsunshi, doshe kunnenshi, kamar daga sama madam Hindu taji Murya Haleesa tana ihu had'e da kwada mata kira a razane ta take haura _stairs_ idanuta a rufe tashigo d'akin da k'arfi tajuyo da Haleesa tana, facing d'inta har zuwa lokacin Haleesa ihu take tana kira wayyo mommy aljani mai ido magge, girgiza ta mommy tayi da kyar Haleesa tayi shiru yayinda Madam Hindu tace menene Haleesa me kike yi wa ihu"?
Wallahi mommy shine aljani mai ido magge ga shinan zaune akan, bed d'inki, dube idanu shi mommy Allah na magge ne.
Sai lokacin mommy ta kai dubanta bisa bed yana zaune ya langwashe k'afafu shi hannaye doshe a kunnenshi, madam Hindu tayi murmushin mai sauti gaske tace Haleesa kalle shi ki gani ba aljani bane mutum ne.
Ihu Haleesa ta'kara kurmawa cikin zafin rai da tafarfasa zuciya yasauko ya tunk'aro waje Haleesa wance ke ta faman zunduma ihu yadaka mata rikitaciya tsawa _hey! Shut up just shut up!_
Yadda ya yi ihu yahdassawa jijiyoyi Kansa da na wuyanshi tashi fuskarsa tayi jajir alama tsanani bacin rai nan take Haleesa ta hadiye raguwar ihunta, talafe a jikin mommy had'e da chuikuikuye ta
"Madam Hindu ta dinga bubuga bayanta tace Haleesa wannan ba aljani bane d'ana ne sunanshi Habeeeeb......

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[31/08 7:48 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [30/08 12:29 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```34```
Chapter 13 · 0% Book details