← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 95

Sashe 63

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~~Son, son please wake up don't leave your mother I really need you, please Habeeb wake up, gaba d'aya lissafin brain d'in madam Hindu ya kwance tarasa inda za ta jefa kanta batasan lokacin da tafashe da matsanancin kuka tana girgiza Habeeb da k'arfi ganin take yi kamar Habeeb ya mutu ita kuka Bala kuka ba mai rarrashin wani sai lokacin tunani ya zo wa Bala da hamzari yanufi d'an k'aramin fridge da ke ajiye a d'akin ya bud'e yadauko robar ruwa mai sanyi, ya shafawa Habeeb kamar _5 second's_ da Shafa mishi ruwan yasaki ajiyar zuciya mai k'arfi a hankali ya ke bud'ewa idanu har ya ware su gaba d'aya akan fuskar madam Hindu ya k'ank'ame ta cikin dashashshiyar murya, yace _sweetheart cikina kaina, ki rik'e min kaina zai cire_
Madam Hindu tak'ara rud'ewa ta juya wurin Bala cikin shouting tace _please Bala call doctor saleem immediately_
Jikin Bala na rawa ya yi dialling number Dr saleem daf da asuba Dr saleem ya iso cikin muryar kuka madam Hindu tafara rok'onshi _please Doctor do something to save my son life I don't wants to loose him'!_
''Dr saleem yace calm down madam insha Allah ba abunda zai faru da d'anki batare da 6ata lokacin ba Dr saleem yafara treatment d'inshi ta hanyar daura mishi drip da injections cikin d'an k'ank'ani lokacin bacci ya yi awon gaba da shi madam na zaune a gefenshi tana Shafa sumar kanshi ta mayarda ganinta wurin Dr saleem tace _what's wrong with my son Doctor"?_
Dr saleem ya share zufa da handkerchief ya d'an numfasa daga bisani yace na yi matuk'ar mamaki lokacin da nagano ainihin abunda yake damunshi da farko akwai tsananin tunanin da yake yi Wanda yana daf da jininsa ya hau sai kuma rashin cin abincin Wanda ya janyo masa kamuwa da cutar ulcer.
"Madam Hindu ta zaro ido da alama firgicin a tare da ita ga kuma d'inbin mamakin furucin Dr saleem muryarta na rawa ta maimaita abunda Dr saleem yafad'a _tunani da ulcer_
"With full confidence Dr saleem ya gyad'a kai yacigaba da cewa dole sai ana bashi, kyakyawar kulawa musanman cin abincinsa idan ya falka ki yi k'ok'ari a matsayinki na mahaifiyasa ki titsi shi domin ya sanar da ke abunda yake damu shi a matsayinki na uwa bara ki rasa taimakon da za ki ba shi, ba kuma ki tabbata yana taking medicine d'inshi in time domin na fahimce duka magunguna da na kawo mishi ba Wanda ya yi amfani da shi.
''Madam ta goge hawayen fuskarta, tace na gode Dr saleem.
"You're welcome madam Dr saleem yafad'a yatattara tarkace shi, ya kama gabansa yabar madam Hindu cikin jimami da fargaba.
''Madam tasauke ajiyar zuciya ta juya wurin Bala cike da son jin k'arin haske dangane da ciwon d'anta Bala har tsawon wane lokacin Habeeb yadauka bashida lafiya sannan kuma ina matarshi da ta barka kana jinyarsa"?
''Domin ita ce ta dace ta kula da shi ba kai ba tun zuwa na gidanan duk, da bana cikin natsuwa ta zuciya ta take bani akwai abunda ke faruwa a tsakaninsu.
''Bala ya numfasa ya karkace baki yasoma kwararo wa madam Hindu zance tun kafin boss ya yi tafiya na fahimce akwai abunda ke damunshi, kwata-kwata yadaina cin abincin ranar da yadawo yafad'i cikin yanayi na rashin lafiya sau biyu ina zuwa part d'in Haleesa bana tararda ita rabona da in sakata a idanunna tun washe garin ranar da Imaan tasami hutun makaranta, lokacin da Hannah ta zo za ta tafi da ita na had'u da su a parking space Haleesa ta yi musu rakiya mu ka gaisa to fa tun daga ranar ban k'ara ganinta ba abun ya yi matuk'ar d'aure mini kai ina tashiga ne tsawon wannan lokacin da Boss yake fama da rashin lafiya yak'arasa magana cikin yanayi da ke nuna alhininsa.
''Madam ta mik'e tsanm..... Batare da tace da Bala komai ba tanufi part d'in Haleesa cikin Sa'a tana murd'a handle k'ofar ta bud'e ta kutsa kai tun kafin tak'arasa shiga parlourn, ta hango Haleesa zaune akan _2 seater_ k'afutata na zube akan kujerar tana yanke farce jin k'arar bud'e k'ofa yasa Haleesa ta d'ago _4 eye's_ tayi da madam Hindu rass!....gabanta yafad'i da sauri ta mik'e tsaye ta d'an sace kallon wall clock da ke manne a falon _9:07am_ jikinta yafara rawa tsoro ya baiyana k'arara akan fuskarta da kyar ta furta _sannu da zuwa mom_
Saida madam Hindu takai zaune sannan ta amsa mata ba yabo ba fallasa.
''Tun daga nan Jikin Haleesa ya yi sanyi nan take zuciyarta yaba ta cewa akwai abunda yake faruwa a sanyaye ta duk'a cikin girmamawa tace _ina kwana mom''?_
_lafiya amma ba qalau ba_
furucin madam Hindu yak'ara tsorata Haleesa cikin sark'ewar halshe tace me ke faruwa mom''?
''Wannan tambaya ta Haleesa tak'ara harzuk'a madam Hindu har takasa controlling temper ta cikin zafin rai ta rufe Haleesa da fad'a _ke wance irin mutum ce Haleesa mijinki bashida lafiya tsawon kwanaki uku kuna gida d'aya ace baki saniba wannan wane irin sakarcin ne"?_
''Wannan ya tabbata mun da cewa baki Masan menene Kalmar miji take nufi ba, ballatana ki San yadda ake kula da shi, dalilin wannan sakacin naki gashinan d'ana ya kamu da cutar yunwa, wallahi idan wani abu yasame d'ana Haleesa har abada bara taba daina ganin sakaci da laifinki ba koda ace Habeeb ya yi miki wani laifi bai kamata ki yi masa horo da yunwa ba tak'arasa magana tana huci.
''Tun lokacin da madam Hindu tafara wankewa Haleesa allonta Haleesa take wuk'i-wuk'i da idanu tsananin mamakin zafafa kalaman madam Hindu suka hanata tabuk'a komai.
Shiru Haleesa ta yi tarasa abun fad'a sai kawai tafashe da kuka madam Hindu ta girgiza kai ta mik'e a zafafe tace wannan kukan da ki ke yi bashida amfani zan iya danganta shi da kukan dad'i domin in Habeeb ya mutu bakida asara nice da asara domin ni ce narasa d'a madam Hindu na k'arasa magana tafice daga falon tabar Haleesa na kuka kamar ranta zai fita, haushi da tsanar Habeeb Lamido suka cukuikuye mata zuciya a yadda takejin zafi na kwarara a zuciyata Kamar ta had'a kayanta tabar mishi gida dama yasha fad'a mata saboda mom ya aureta a halin yanzu mom ta tsaneta, har tana danganta da laifin da batada masaniya akai tana cikin wannan halin Hannah tashigo
ta zauna a gefenta cikin sanyin murya tafara magana, Haleesa yanzu nan mom ta kira ni a waya ta zayyane mun abunda yafaru nayi matuk'ar mamaki yadda mom takasa gano laifin yaya Habeeb, jira nake yaya Habeeb yafarfad'o na fallasa shi a gabanta in yaso ta tantance tsakani ke da shi waye mai laifi.
''Haleesa ta share hawaye fuskarta tace Hannah banaso, ki sanarda mom komai dangane da zaman mu da yaya Habeeb, a hali yanzu zuciyata tariga ta bushe na dau alwashi sai na azantarda ruhin d'an uwanki da soyayya ta mai tsananin zafin gaske na yi amfani da ita na rama duk wani cin kashi da ya yi min sai na nunasa masa cewa ba kowace Mace ake wulaqantawa ba sai gwanmace kid'a da karatu.
Cikin tsananin farin ciki Hannah tarik'o hannun Haleesa tace tun farko abunda nake nuna miki kenan Haleesa ki ka k'i bani had'in kai da yanzu zance yasha banban, yanzu tashi mu tafi ki ba wa mom hak'uri nasan yadda mom takesonki bara ta iya cigaba da fushi da ke kuma duk bak'ak'en maganganu da mom ta zuba miki ki rubuta su tass....ki yi wa d'anta tanadin su Haleesa ta zaro ido tace Hannah bakida kirki yayanki ne fa
''So what's Hannah tafad'a had'e da kad'a eye's ball d'inta karki manta Haleesa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne don haka duk lokacin da yaya Habeeb yashiga hannunki karki raga masa ki tabbata kin sauke masa wannan miskilancin da yake tak'ama da shi.
Haleesa ta cize lips d'inta na k'asa ta kad'a kai tace bari kawai Hannah Allah yakai damo ga harawa.
Ameen 'yar uwa zo mu tafi kada mom tak'ara hayewa.
"Direct bedroom d'in Habeeb suka wuce mom na zaune kusa da shi ta rafka tagumi yayinda Habeeb ke ta sharar bacci, Hannah ta zunguri kafad'ar Haleesa nan take Haleesa ta yi pity face ta zube gaban mom tarik'e hannun mom ta marairace murya _Dan Allah mom ki yi hak'uri nasan na yi kuskure amma insha Allah bara ki sake kamani da koda kwatankwacin irin wannan laifi_
tak'arasa magana cikin muryar kuka madam Hindu tasauke ajiyar zuciya tad'ago Haleesa suka nufi parlour tasoma yi mata nasiha daga yau Haleesa karki sake sakacin sake ragama abincin mijinki a wurin ku-ku lokacin da peter yake yi min bayani tun zuwanki gidanan shi yake yi wa Habeeb girki ba ki ji yadda raina ya6acin ba amma yanzu komai yawuce ki tashi ki Shiga kitchen ki Samar mishi abunda zai cin domin Dr saleem yace da ya falka abashi abinci
''Da hamzari Haleesa ta mik'e tanufi part d'inta Hannah ta Mara mata baya.
_15 minutes later_
A hankali Habeeb yake bud'e idanunshi har ya ware su gaba d'aya, k'ok'ari yake ya mik'e zauna da sauri mom ta taimaka masa, ya zauna tasaka masa pillow a baya ya jingina jikinsa, duk ya rame ya yi k'ashin wuya.
''Sannu son ya ka ke jin jikin naka"?
Da sauki mom yanzu dai ina son na yi wanka na rama sallah da ke kaina.
Da sauri mom ta mik'e bara na kira Haleesa ta taimaka ma, batare da ta jira jin ta bakinshi ba tafice, Wani irin dad'i ya ratsa sassan jikin Habeeb ya kwarara a zuciyarsa, ya lumshe idanu, jin karar bud'e k'ofa yasa da sauri ya bud'e idanunshi yasauke su akan fuskar Haleesa, tasake masa k'ayatace murmushi, sannu yaya Habeeb ya jikin naka"?
''Saida ya ja iska yafesar sannan yace da sauki ki taimaka ki had'a min ruwa zan yi wanka
Batare da tace komai ba tashiga bathroom ta cika masa bathtub da ruwa masu d'an d'umi-d'umi har tafito yana nan yadda ta barshi muryarta tace tadawo da shi daga tunanin da ya afka _yaya Habeeb na had'a ruwan_
"Chan k'asan mak'oshi ya furta na gode yana bin bango yashiga bathroom Haleesa ta bi shi da kallo ya yi matuk'ar bata tausayi ashe akwai abunda zai sa yaya Habeeb ya yi laushi, ta yi murmushin mugunta ta gyara masa bed ta feshe d'akin da freshener tana tsaye har yafito daga wanka ya zauna a gefen bed yana mata kallon k'asan ido wani irin abu yakeji yana ratsa jinin jikinsa can! Ya yi gyaran murya daga bisani yace........
Chapter 63 · 0% Book details