← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 95

Sashe 61

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

~~k'amshin perfume da ta yi amfani da shi ya ratsa k'ofufi hancin Habeeb baisan lokacin da ya lumshe idanunshi yak'ara matso da ita zuwa k'irjinshi ya matse ta gam Tsigar jikinta ta tashi Yarr! Hancinshi yadaura a gefen wuyanta yana shak'ar k'amshinta tuni Habeeb ya manta suna tsaye ne a compound yafita haiyacinsa, numfashinsa yana fita da sauri-sauri ya kasa daurewa ya ziro hannunshi cikin rigarta da sauri Haleesa ta taka masa birki ta hanyar furta _please yaya Habeeb stopped Imaan is looking at us_
A rikice yadawo hayyacinsa ya tureta daga jikinsa dama hausawa sunce tabarma kunya da hauka ake nad'eta sai kawai ya gallawa Haleesa harara _wannan wane irin sakarcin ne huh"?_
_shine illah auren k'anana yara dube ki wai wasa 'yar 6oya ki ke yi danasani na barki ki fad'i ki karya k'afa ko hannunki naga d'an iska da zai yi jinyarki dallah! Bani wurin in wuce kin yi wani tsare ni da idanu_
A zafafe yak'arasa shiga gida Haleesa ta bi shi da kallon tasauke ajiyar zuciya, tajuya ta hango Imaan zaune cikin flowers tana wasa sai faman tsinko Flowers take tana tarawa a gefenta, Haleesa tak'ara sauke ajiyar zuciya a cikin zuciyarta tace, _thank God_ ashe ba Wanda ya ganmu tanufi wurin Imaan tarik'on hannunta suka shiga cikin gida.
_9:00pm_
Haleesa na kwance a bedroom d'inta ta yi rub da ciki ta d'aga k'afafunta sama ta yi zurfi a tunanin rungumar da Habeeb Lamido ya yi mata d'azu da yamma abun yakasa fita daga zuciyarta duk lokacin da ta tuna da kyakyawar rungumar da tasamu a wurinshi sai ta yi murmushi ta kasa tantance wannan murmushin da take yi na menene ta yi wani juyi tadawo rigingine idanunta a lumshe tasoma fasalta kyakyawar Surar jikinsa ba abunda yafi burgeta a jikin Habeeb Lamido irin lallausar sumar kanshi koda yaushe idaunshi a lumshe suke kamar mai jin bacci da kyar Habeeb ya yi magana batare da ya ja iska ba kamar Wanda yacin yaji, yana yawan tsotsan bakinshi za ka yi tsanmani sweet yake sha in kuma yana magana d'aya-d'aya yake furta harafi sai kace mai bita, Haleesa ta yi murmushi a zuciyata tace _Handsome_ kenan ga kyau saidai mugun hali da miskilancin tsiya, ta mik'e zaune ta k'urawa wall clock idanu _10:09pm_ ta d'an ja tsaki ko kad'an batajin bacci dama Imaan ce abokiyar firarta tun 8:00 o'clock ta yi bacci.

```HABEEB LAMID'O```

Habeeb na zaune a parlournshi yana tura bayanai a system yunwa yakeji kamar 'yan hanjinshi za su tsinke ya rasa dalilin da yasa tun jiya da yacin abincin Haleesa d'andanon abincin yakasa fita daga bakinshi duk abunda yacin sai yaji ba tested yature laptop a gefe yanufi part d'in Haleesa cikin sand'a kamar barawo yak'arasa wurin dining table ya bud'e warmers k'amshin Egusi soup ya buge hancinshi ya cigaba da bud'e warmers yana ganin abunda ke ciki a zuciyarshi yace ba shakka wannan abincin yarinya nan ce ta girka shi yadauki Ledar tuwo semo guda d'aya yasaka cikin plate ya zuba soup a d'an k'aramin plate d'ayan plate kuma zuba farfesun kifi da sauri yakoma parlournshi yana ci yana wani kad'a kai _ashe haka yarinya nan ta kware da girki"?_
_Gaskiya tafi Peter iya sarafa abincin nayi kuskure wulaqanta ta saboda banta6a cin abinci da ya yi min dad'i irin nata ba kuma har abada bara ta6a nuna mata ina jin dad'in girkinta duk ranar da tagano ina cin abincinta ajina da girmana za su zube a idonta ni kuma bara sake da abunda zai rage mini class_
Ya cinye tuwon tass! Har da su sud'e plate daga bisani yanufi bedroom ya zarce bathroom ya yi brush agajiye yafad'a kan bed cikin d'an k'ank'anin lokacin bacci yadauke shi a cikin baccin nashi yafara mafalkin leesa Zaune take a garden tana wasa da ja da farin fure tashagala da abunda take yi a hankali yake sand'a har yak'araso daf da ita ya zauna tana juyowa suka had'a ido tasake masa k'ayatace murmushi shima ya mayar mata da martanin murmushin nata kasa d'auke idanunshi ya yi akanta cikin sigar shagwa6a ta turo d'an k'aramin bakinta mai jefa Habeeb cikin tsantsar sha'awarta _yaya Habeeb wannan kallon fa"?_
Cikin shauk'in so yarik'o hannunta ya jefa yatsanta a bakinshi yana tsotsa kamar yasami lollipop, da sauri leesa ta fisge hannunta ta wani yatsine fuska, Habeeb yadawo kalar tausayi chan k'asan mak'oshi ya furta _please leesa ki barni mana_
Shiru ta yi tana kallonshi da k'arfi yafisgota tafad'o kan k'irjinshi ya matse ta gam ya lalla6o bakinta tsawon lokacin suka dauka a haka daga bisani ta ture shi ta mik'e da gudu tanufi cikin yayinda shima ya mik'e ya Mara mata baya a parlour ya yi nasara kama ta ya d'auke ta chak! Yanufi bedroom da ita yadireta akan bed Daga nan komai yacigaba da wakana.
A firgici Habeeb ya falka daga mafalkin da ya zame masa, jiki gumi ya tsatsafo masa yadafe kanshi da hannayen, ya runtse idanunshi gam! Photon abunda yafaru tsakaninsa da Haleesa yadawo masa da sauri ya ware idanunshi ya ja tsaki cike da jin haushin kanshi ya mik'e yanufi bathroom.
Habeeb wanka ya ke yi yana zance zuci _me yasa duk lokacin da na kwanta bacci sai na yi mafalkin ina saduwa da yarinya nan"?_
_ina da wannan mafalkin nawa zai kasance gaskiya tabbas da ba k'aramin tafiyar da ruhina za ta yi ba_
Jiki ba lakka ya gama wanka yafito har aka yi kiran asuba yana fama da tunanin leesa da yarufe idanu kyakyawar fuskarta yake gani.
********************
_7:00am_
Haleesa na tsaye cikin kitchen tana had'awa Imaan abincin da za ta tafi da shi school tuni ta takatar da peter da Girka abinci da ita da kanta take shiga kitchen ta girka duk abunda ranta yakeso agurguje ta kamalla had'awa Imaan lunch box d'inta tanufi d'akin Imaan tayi mata wanka had'e da shirya ta cikin uniform ta zarce da ita dining area ta ja kujera ta zaunar da ita ta had'a mata tea had'e da chip's Imaan tana gama breakfast Haleesa tarik'on hannunta suka nufi compound suna, fita ta hango Habeeb da Bala a tsaye Habeeb na jefawa karnuka{ police dog's} nama suna Cin kasa k'arasawa parking space ta yi saboda tana jin kunyar had'a ido da Habeeb.
Imaan tadaka tsalle _yeee yau Daddy ya fiddo da Rahul da Rita bara naje mu yi wasa_
Da sauri Haleesa ta taka mata birki ta hanyar furta ke Imaan banaso shirme ke da za ki tafi school me ye gaminki da karnunka karki sake naga kin tsaya a wurinsu ko kinmanta yau za Ku fara test ne"?
Imaan ta girgiza kai Haleesa tace to kama hanya kitafi ga sa'eed driver yana jiranki ta mik'a mata lunch box d'inta Imaan tajuya tanufi wurin Daddynta _Good morning Daddy_
Morning my angel
Cikin shagwa6a Imaan tace Daddy shine saida kaga zan tafi school ka fiddo Rahul da Rita koh"?
Habeeb ya yi murmushi ya shafi kumatunta kin ga my angel banaso rigima kitafi school in kindawo auntynki ta fiddo miki su ku yi wasa.
"Imaan ta zaro ido kamar taga abun tsoro _Daddy aunty Haleesa tsoronsu fa take yi ranar ma mu je garden da ta gansu da gudu takoma cikin gida tadinga fad'a tana cewa shi wannan yaya Habeeb komai so yake yi yanzu yarasa abunda zai yi kiwo sai bak'ak'en karnunka sai nace da ita aunty ba fa sunansu karnunka ba sunansu R........_Imaan ta hadiye raguwar kalamanta sakamako katsinta da Habeeb ya yi my angel wannan labarin naki basan tsawon lokacin da zai d'auka kafin naji karshensa ki bari sai kindawo daga school ki k'arasa mun kinji"?
Imaan tad'aga kai sa'eed driver yarik'o hannunta suka nufi parking space
''Bala ya kyalkyale da dariya Habeeb ya galla masa harara Bala ya hadiye dariyarshi yace "Boss Imaan tana mugun burgeni saboda surutun nan nata.
Habeeb ya tabe baki yace ae dole ta burge ka saboda halinku d'aya
Bala washe hak'ora yace ni fa boss mamaki nake yi kai ga magana wuya take maka kuma ka tsanin yawan surutu sai gashi Allah yabaka 'ya mai bala'e surutu kamar Aku{parrot}
Habeeb ya ja tsaki yace _"Allah ya shiryeka Bala_
Bala yace ameen boss yau za'ayi ruwan sama har da k'ank'ara saboda ka yi min fata nagari da alama amarya tafara canza ka yak'arasa magana yana dariya
''Tsawon lokacin Habeeb yad'auka yana kallon Bala daga bisani ya girgiza kai, yace tun da kagama surutun naka daga ciki har da yi mun sharri sai ka tattara rahul da Rita ka mayarda su d'akinsu karka d'aure su kabarsu a sake kuma ka tabbata ka rufe musu k'ofa.
"Bala yace angama boss ae tun da na fahimcin amarya tana tsoronsu bara yi sake da za su fito su tsorata maka ita.
Habeeb ya yi murmushin takaicin yajuya yasan muddin yacigaba da tsayuwa Bala zai iya haddasa masa bugawar zuciya direct parlourn Haleesa yadosa bata ciki tana bedroom ya yi tsaye a tsakiyar falon yana k'are masa kallo _very neat_ sai k'amashin turaren wuta ke tashi karaf idanunshi suka hasko masa dining table da sauri yanufi wurin ya yi serving d'in chip's had'e da sauce na cabbage da carrot ya ji anta da k'oda dai-dai lokacin da Haleesa taddano kai parlourn ta hango abunda Habeeb
Yake yi da sauri ta la6e tana lek'onshi tana kallonshi har yashige part d'inshi Haleesa ta yi murmushi ta kad'a eye's ball d'inta lallai Habeeb lamid'o d'an rainin hankali ne ko ya manta da kirarin da ya yi kada na kuskure na dafa ko da noodles da sunanshi sai gashi na kama shi yana satar mun abinci daga yau bara ka k'ara ganin abincin ballantana har ka sata
"ta yi murmushin mugunta tun daga ranar Haleesa da tayi girki take zube abinta cikin warmers takai bedroom da, Habeeb yasud'ad'o yacin mai dad'i yatarar da dining table wayam!
Duk lokacin da Habeeb Lamido ya zauna bashida aiki sai tunanin Haleesa kuma baya iya cin abincin kowa sai nata yadda peter ya jera masa abincin haka zai dawo yadauke saboda ko kallon bai ishe ba cikin d'an k'ank'ani lokacin Habeeb yafara fita hayyacinsa, ganin yadda sha'awar Haleesa na neman kassara shi ya tattara kayansa ya haura Germany a tunaninshi in ya nisanta da ita zai manta da duk wani abu da yashafe ta baisan cewa hakan ba abunda zai k'ara masa sai d'inbin damuwa, da tunani kuma yak'i ya amince da soyayya Haleesa ce ta kama shi ba sha'awa ba.
*****************
```GERMANY```
Habeeb yana zaune a wani had'ad'en wurin hutawa kallon d'aya za ka yi masa kagano yana cikin damuwa yadda zuciyarsa ke azalzalarsa akan ya kira Haleesa ko muryarta za ta rage masa damuwar da yake ciki zuciyarsa na bugawa Ya yi dialling number ta.
Haleesa na zaune Imaan tayi pillow da cinyoyinta kiran Habeeb yashigo wayarta ta zaro idanu gabanta na fad'uwa ta yi picking................
Chapter 61 · 0% Book details