← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 95

Sashe 22

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Da wuri Haleesa ta tashi ta yi wanka tana jiran fitowar Masa'ud yakaita airport, saida yagama ja mata rai sannan yace tafito su tafi koda tafito _10:30am_ ta buga gashi flight d'in da zata bi zai tashi k'arfe _11:30am_ sai faman complaints take mishi ya6ata mata lokacin Juwairiyya sai faman dariya take yi gani yadda Halee take zumud'i tafiya saida suka ga tashin jirgin su Haleesa sannan Masa'ud da Juwairiyya suka nufi gida.

```YOBE```

Jirgi na sauka bayan Haleesa tafito batare da 6ata lokacin ba, taja trolley d'inta taxi tashiga tana gani driven taxi d'in yashiga unguwarsu tasaki sanyaya ajiyar zuciya tasaki iska ta furzar tace _Home, sweet Home_ har k'ofar gidansu taxi d'in tayi parking cikin zumud'i ta balle k'ofa tafito, dai-dai lokacin da Hasheem 'kanin marigayi yaya Habeeb yafito daga cikin gida Haleesa ta tsura masa ido da sauri-sauri numfashinta yake fita saboda sai yau ta'kara tabbatar da tsanani kama da Hasheem yakeyi da Yaya Habeeb banbanci su kawai yaya Habeeb yafi shi, tsayi gani yadda take kallonshi yasa yasake mata murmushi yak'araso daf da ita cikin tsokana yace babylove ya akayi ne naga kin wani tsare ni da ido sai kace yau kika fara ganina ke da kika je Lagos a maimako ki waye sai kika k'ara kwaso k'auyanci.
"Ko kwakwara motsi Haleesa ta kasa yi da k'arfi Hasheem ya kira sunanta Haleesa!
Haleesa ta dube shi tayi ajiyar zuciya, kafin ta yi magana mai taxi yace malama sallame ni na tafi Hasheem yace nawa ne kud'inka"?
D'ari uku ne yallabai Hasheem yafito da _N 500_ ya mik'a masa shi kuma ya bashi chaji yadauki trolley d'inta ya wuce gaba tana biye da shi sai tambayoyi yake zuba mata yayinda Haleesa takasa bashi amsar ko d'aya daga ciki da sallama yashiga cikin gidan had'e cewa Ammi fito ga bak'in Lagos da rana tsaka da sauri Ammi tafito daga d'aki tana gyara d'auri d'an kwalinta tana had'a ido da Haleesa mamaki ya baiyana akan fuskarta da gudu Haleesa ta'karasa wurinta ta rungume ta tasa kuka Ammi ta bubbuga bayanta, haba! Haleesa meye kuma abun kuka"?
Cikin muryar kuka mai cike da shagwaba tace Ammi nayi kewarki'
Hasheem da ke gefe ya kyalkyale da dariya yace lallai yarinya nan dad'i ya yi miki yawa ki ce kukan dad'i kikeyi to ni zan tafi anjima zan dawo na kar6i tsaraba na yak'arasa magana had'e da yaficewa.

```3 hour's later```

Haleesa na zaune a d'akin Ammi sai labari madam Hindu take ba wa Ammi, kwarai Ammi ta yaba da kirkin "madam Hindu
Tace duk lokacin da tashigo Yobe zata zo Ku gaisa.
Murmushi Ammi tayi tace Allah yakawo ta lafiya
"Ameen Ammi bara na je na gaida inna mairo ta zari hijab d'inta had'e da ficewa, tana Shiga gidan zainab ta shek'o suka rungume juna sai da aka fara kiran sallah magariba Haleesa ta koma gida bayan ta gama sallah tafito tsakiyar gida tasha iska yaya salman ya yi sallama yashigo, Haleesa ta amsa mishi, ya zauna kusa da ita tana bashi labari Lagos Salman ya kyalkyale da dariya yace Haleesa manya ke da kika yi _1 week_ kacal a Lagos har wani labari za ki bayar
Haleesa ta turo baki tace Allah yaya salman nayi yawo saidai ba sosai ba kuma baka ga gidan da na zauna Allah gidan yahad'u kamar a abroad ae kuwa Salman da kamal suka dinga yi mata dariya Haleesa ta gallawa kamal harara tace gwara ni na je lagos nayi kauyanci kai kuma kamal baka ta6a zuwa ba tak'arasa magana had'e da yi masa gwalo har baffa yashigo gida suna zaune tsakiyar gida suna fira shima ya zauna akayi firar da shi kowane su zuciyarshi cike da tsan-tsan farin ciki sakamako gani yadda Haleesa take annashuwa da nishad'i sai misali k'arfe _11:44pm_ kowane su yanufi d'akinshi Haleesa tasuya kaya zuwa wata 'yar k'aramar vest ta daura zani bisa ta kwanta tana daura kanta bisa pillow ta lumshe idanu nan take face d'in Habeeb Lamido yafara yi mata shawagi a eye's nata da sauri ta bud'e idanuta _"why Habeeb why don't leaves my heart to be in peace"?_
Ba gidanku kadai ba har garin Lagos na baro maka _but you still following me_
Hawaye suka ziraro mata a gefen idanu suka sauka bisa wuyanta, kuka Haleesa tayi sosai daga bisani bacci ya yi awo gaba da ita anan ma bata tsira ba saboda mafalki shi tadinga yi Habeeb ya zamewa rayuwarta karan tsaye.

```BAYAN SATI D'AYA ```

Haleesa da zainab sun dawo daga islamiyya yamma suna tafiya suna fira, tun daga nesa Haleesa ta hango mota kirar _KIA cerato_ a Parke a k'ofar gidansu wani matsananci fad'uwar gaba taji saboda ta ta6a gani Habeeb Lamido cikin irin wannan motar, zainab tace Haleesa bak'i masu kud'i mu ka yi ne na hango had'ad'iyar mota a k'ofar gidanmu"?
Haleesa tad'ago ta dube ta tasauke ajiyar zuciya tace oho! Tafad'a kaitsaye suna k'arasawa k'ofar gida idanu Haleesa suka sauka bisa number motar _Habeeb Lamido 5_ abunda idanuta suka hasko mata kenan tsanani tsoro had'e da tashin hankali suka chukuikuye mata zuciya Wanda hakan ya haddasa mata zaro idanu tanemi yawu bakinta tarasa, a zuciyarta tace na shiga uku me wannan shu'umi ya zo yi a gidanmu..."?

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[17/09 3:01 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```51```
Chapter 22 · 0% Book details