← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 95

Sashe 49

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_9:30pm_
Haleesa na zaune a main parlour ta yi zurfi cikin tunani, Habeeb yashigo duba d'aya ya yi mata yadauke fuska _sannu da zuwa yaya Habeeb_
"Habeeb ya mata wani mugun kallo mai k'unshe da tsana ya ja tsoki ya haura sama Haleesa ta tabe baki ta nan zaune har yadawo yadda ya bar ta haka yadawo ya tarar da ita
Ranshi a 6ace yadaka mata tsawa ke!
Tad'ago a tsorace
Wai ke wace irin bagidajiya ce"?
Haleesa ta hadiye b'acin ranta ta kud'iri aniyar Zata yi hak'uri ta shanye wulaqancinsa
"Ke ba magana nake da ke ba kin wani tsare ni da idanunki masu kama da na mujiya narasa wace irin k'addara ce ta hau kaina na aure ki ba ki da amfani a rayuwata, na tsane ki bana k'auna na bud'e ido na ganki daga yau karki kuskure na sake ganinki a main parlour kidinga zama a parlour ki tashi ki bani wuri
"Haleesa ta mik'e tsam tanufi part d'inta ta haye bed ta k'undudune cikin blanket tana kukan zuci bacci ya k'aurace wa idonta da rufe ido fuska Habeeb Lamido take gani b'akin ciki da b'aci rai suka lullu6e ta komai ya dagule mata kanta ya dau zafi tana mamaki irin wannan zazzafa k'iyayya da Habeeb yake nuna mata sai kusan asuba baccin ya yi awo gaba da ita.
********************
_1 week later_
Tun daga lokacin Haleesa ta datse duk wata hanya da za ta had'a ta da Habeeb sai ta tabbata yafita sannan ta ke Shiga part d'inshi ta gyara masa suna ciki wannan yanayi yasami urgent call daga Canada a wani company da yakeda hannun Jari"
Haleesa na zaune a falonta tana tsifewa Imaan kai Habeeb, yashigo fuskarshi a had'e da sauri ta d'auki mayafinta za ta lullu6e jikinta saboda rigar da ke jikinta transparent ce rabin k'irjinta a bud'e bata manta da wulaqanci da ya yi mata ranar da yaganta da transparent night gown shiyasa ta yi wa kanta k'iyamunlaili tun kafin ya ci zarafinta
Ta yi mugun ba Habeeb Lamido haushi da k'arfi yaficike mayafin ya jefar
Haleesa ta yi galala da baki tana kallonshi
Ya dube imaan yace
Imaan tashi ki je room d'ina akwai chocolate akan bedside ki d'auka
jikin imaan na rawa ta mik'e tafice da gudu yak'arasa kusa da ita yadaura k'afarshi akan kujera da take zaune yad'ago fuskarta daf da ta shi numfashinsa yana sauka akan fuskarta k'amshinsa ya baibaye ta ya tsareta da manyan idanunshi "eye's ball d'inshi masu kama da na magge suka k'ara jefa Haleesa cikin rud'ani ya matsi mata baki ya ja iska duk ranar da ki ka sake ganina ki ka rufe, wannan busashe k'irji naki sai na yi miki wulaqanci ko mata kirki ba su ishe ni kallo ballatana ke mai kirge dangi yak'arasa magana had'e da Jan tsaki ya dungure mata kai cikin isa da tak'ama yanemi 2 sitter ya k'ame ya yi crossing legs d'inshi saida yagama shan k'amshi yafara magana a yatsine _zan yi tafiya gobe in da akwai abunda ki ke buk'ata you should tell me_
Haleesa ta yi ignoring nashi saboda batasan abunda za ta ce da shi
_ina magana da ke kin yi shiru yana d'aya daga cikin abunda yake k'ara mini tsanarki_
Tad'ago da kyar kamar za ta fashe da kuka muryarta na rawa tace bana buk'atar komai
Ya tabe baki gobe mom da Hannah za su wuce Abuja na yi magana da mom za ki bi su da fatar ba ki manta da dokoki da na shinfid'a miki"?
"ki tashi yanzu ki had'o kayan Imaan da ke bedroom d'ina har ta mik'e tsaye yadakatar da ita oh! I forgot to tell you chef peter da direba da zai dinga kai Imaan school tomorrow morning za su wuce so that ki had'a takarce ki su wuce miki da shi saboda a flight za Ku tafi
Cikin muryarta mai sanyi tace _toh_ tafice yayin da Habeeb ya bi ta da kallo Half gown ne sanyi a jikinta mai spaghetti hands idanushi suka sauka bisa hip's d'inta, da sauri yadauke kai ya ja iska had'e da lumshe idanu ohh! Gosh ashe baby nan mai zafi ce "she has Good body structures ya lashe lips d'inshi ina ma yanda jikinta yakeda zafi ace tana da gurbi a zuciyata, ina ma auren soyayya mu ka yi ya ja tsoki cike da jin haushin kanshi to wai me zai sa na dinga wasting time d'ina ina wannan tunani tun da ba sonta nakeyi ba asalima a tsarina banaso k'aramar yarinya yaushe wannan kwaila za ta iya da ni"?
Har Haleesa tadawo janye da trolley d'in Imaan yana zaune da waya a hannunshi yana buga game, ke! Ya kirata batare da ya dube ta very slowly yake magana kamar mai ciwo hak'ora ki shirya ke da Imaan za mu fita unguwa kuma karki bata min lokacin ta amsa masa a sanyaye tana shiga bedroom ta daka tsalle _yeee yau zan fita na shak'i iskan duniya tun da na zo gidanan ko k'ofar gida ban ta6a zuwa ba_
A gurguje ta shirya cikin Arabian gown orange colour da ado white stone's ta gyara fuskarta ta feshe jikinta da turare mai sanyi k'amshi ta yi rolling da d'an siriri white veil"
Imaan ta shigo da gudu _aunty Daddy yace ki yi sauri_
Jikinta na rawa ta sauyawa Imaan kaya suka fito main parlour yana tsaye a tsakiyar parlour yana ganinsu yafice Haleesa na rik'e da hannun Imaan ta Mara masa baya zuwa parking space
Bala na tsaye yana jiransu ya washe hak'ora yace
_Barka da fitowa amaryar Boss yau za'a fita evening show'?_
Murmushin yak'e Haleesa ta yi Habeeb ya ja tsaki ya bud'e seat d'in gaba ya zauna Bala ya bud'ewa Haleesa da Imaan seat d'in baya tun lokacin da suka d'auki hanya Bala ke ta fama zuba yayin da Habeeb ya yi banza da shi wani kyakyawan gate suka nufa Imaan tasa ihu _Daddy yau bara fita gidanan sai mom ta biyani gyad'a na da ta zubar_
Habeeb ya yi murmushi mai sauti yadauke ta yanufi cikin gida Haleesa na biye da shi har cikin parlour Hannah ta taso da gudu ta rungume Haleesa _amarya yaya Habeeb oyoyo_
Habeeb ya haura sama yabar su a parlour
"Humm....Hannah 'yan mata mommy ae ni na yi zato kin koma school
_ina nan ba idan na je bari kawai na matsu na gama karatu nan aure nakeso_
Haleesa ta zaro ido da tsanani mamaki take kallon Hannah
"Me ye haka amarya yaya Habeeb"?
Kafin Haleesa ta bata amsa tafisgo hannunta zo mu je ki gaisa da in-law d'inki kada tafara nuna miki halin uwar miji suka kyalkyale da dariya Haleesa tace kai amma wallahi Hannah bakida kirki, sai na gayawa mom abunda kika ce
"Madam na hakice akan 3 sitter Habeeb na kwance ya yi matashi da cinyoyinta su Haleesa suka shigo har k'asa Haleesa ta duk'a ta gaidata cikin fara'a ta amsa ta ture kai Habeeb d'agani magge sarkin son jiki Habeeb ya kwa6e fuska
"Madam ta janyo Haleesa ta zauna a gefen ta Nasiha ta shiga yi musu Kan Haleesa na sunkuye daga bisani madam tace Son tashi Kai Haleesa ta yi bankwana da su Ammi shiru ya yi kamar ba zai tashi ba ya mik'e madam da Hannah su ka yi musu rakiya har wurin mota Bala ya ja mota suka nufi unguwar su Haleesa Bala ya yi parking a k'ofar gidan su Habeeb ya dube ta a yatsine saura kuma in kin Shiga gidanku ki manta da mu a k'ofar gida
Batare da Haleesa tace da shi komai ba ta bud'e k'ofa tafita tana fitowa idanunta suka hasko mata Yaya Habeeb sanye cikin kayan ball ya tunk'aru ta fuskarshi d'auke da murmushi nan take kwakwalwa Haleesa ta d'auki zafi _dama ana mutuwa a dawo tambayar da tafara aikawa kanta_
"A lokacin d'aya tsanani tsoro da rud'ani suka lullu6e ta numfashinta yafara k'okari barin jikinta yana daf da yak'aroso wurinta ta kwaso da gudu tashiga zaure gidansu duk abunda ke faruwa Habeeb Lamido na tsaye a jikinsa mota yana kallonsu..........

Jeeddah Aliyu🌹

[13/11 7:17 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```68```
Chapter 49 · 0% Book details