Sashe 2
Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yi masa gwalo had'e da cewa ba kai bane kafara
Don ni ne nafara shine kika za ki watsa min ruwan wanke-wanke"?
Turo baki tayi yayin da yaya Habeeb ya yi murmushi mugunta ya sunkuce _bucket_ d'in ruwan gaba d'aya ya kwara mata tasaki mahaukaci ihu had'e da kwalawa Ammi kira wayyo! Ammi kinga yaya Habeeb ya jik'ani da ruwan wanke-wanke, da gudu yaya Habeeb yanufi k'ofar fita ita ma ta bishi da
gudu, tuni ya shige gidansu yabarta labe a zaure tana lek'e sa, daga bisani ta juya cikin gida Ammi ta kalli ta ta tabe baki tace narasa gane tsakani ke da Habeebu waye mashiririci"?
murmushi kawai tayi ta d'auki _basket_ d'in kwanuka takai _kitchen_ tadowa rik'e da tsintsiya ta share wurin da tayi wanke-wanke daga bisani ta cire jak'ak'u tufafi ta ta d'aura zani a k'irji
Ta cika _bucket_ da ruwa kaitsaye bandak'i{bathroom} ta Shiga tayi wanka, ta shirya cikin _dark blue d'in _uniform_ na islamiyya had'e da _whites hijab_ tafito rik'e da jakka mai d'auke da _Al-qu'arni mai girma da saura littafai addini_ ta nufi k'ofar _kitchen_ tace _Ammi na tafi islamiyya_ Ammi da ke ta fama fifita wuta saboda itace basu bushe sosai ba tad'ago tace adawo lafiya sannan karki manta in an tashi isalamiyya ki biya gidan Delu dallaliya ta baki ciko kudina, tajuya had'e da cewa to Ammi amma kuma in bata bani ba na k'arbo abin kudi"?
Ammi tace bansakiba uwar 'yan kaud'i ta fice tana dariya had'e da cewa kai Ammi daga zan yi miki abun kwarai
Kaitsaye gidansu yaya Habeeb tashiga had'e da sallama inna mairo na zaune a tsakiyar gida bisa kujera 'yar tsuguno cikin sakin fuska ta amsa mata, yayin da Haleesa ta durk'usa har k'asa ta gaidata _ina wuni inna"?_
_lafiya qalau Haleesa an fito"?_
_Eh! Inna zainab na ciki kuwa?_
Kafin inna tabata amsa taji muryar zainab a bayata tana cewa ba'a saniba sai yanzu kika damar fitowa"?
Harara ta galla mata tace nima bansaniba in kuma baki tashi tafiya ba, nayi tafiyata inna dai sai faman dariyar su takeyi saboda tasan da kyar ne Haleesa da zainab su had'u ba tare da suyi fad'a ba. sallama sukayi yiwa mata had'e da ficewa daga gidan.....
_DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S_
Jeeddah Aliyu🌹
[24/08 8:51 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [20/08 11:16 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 💝```NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```3```
Suna fitowa zainab tace ke kenan kullum sai kinsa muyi latti kin je kinyi zamanki, kina zuba wanke-wanke soyayya ke da yaya Habeeb bayan kinsan yau muna da _hadda_
Haleesa ta kyalkyale da dariya tace zainab kin Shiga uku a ina kika ganmu muna wanke-wanke soyayya"?
Duk abunda kuke yi ina kallonku ta Katanga saboda turmi na hau ina lek'e Ku, idanu ku ya bud'e da soyayya ko kunya Ammi bakwaji shi kuma yaya Habeeb da yafi ki rashin kunya da ya shigo inna ta tambaye shi dalili jik'ewarshi ba ko kunya yace wai baby love ce ta jik'a ni da ruwan wanke-wanke, ni da inna mu ka bishi da kallo har ya chanzo kaya yafice ba mu daina binsa da kallon mamaki ba.
_umhh_ me zai sa mu ji kunyar Ammi"?
Mu kayi a gaban inna ballatana Ammi, ```NI DA YAYA HABEEB ``` soyayyarmu a jini take ko munaso mu boye ta ba za ta boyu ba kuma ae ba yau nasaba jik'e shi da ruwa ba.
mtss zainab ta ja tsoki tace chan ta matsi muku ni dai ki d'aga 'kafarki saboda yau tafiyar sauri za mu yi sai wani tafiya kike yi kamar kina jin tausayi taka k'asa, duk da Haleesa bata iya tafiyar sauri ba amma dole ta dinga d'aga k'afafuta domin ta huta da masifar zainab
Daga bisani Haleesa tace zainab wane irin _colour_ kaya da yaya Habeeb zai fita ya sanya"?
Saida zainab yatsine fuska daga bisani tace wane irin _colour kaya zai saka a yammaci nan da wuce na ball_ Haleesa tayi murmushi had'e da cewa amma kuma ni cemin yayi shago zai koma.
To yayi miki k'arya saboda haka da kun had'u ki hukunta shi
Harara ta gallawa Zainab had'e da cewa ina ruwanki _NI DA YAYA HABEEB_ ba'a shiga tsakani mu domin duk Wanda yace yashiga tsakani anta da jini rabonsa kunya.
Dallah yi ma mutane shiru da anyi magana sai ki ce _Ni da yaya Habeeb_ sai kace zautata Haleesa ta kyalkyale da dariya had'e da kai ma zainab duka.
Duk lokacin da Haleesa da zainab za su tafi islamiyya dole sai su wuce cikin wata _government primary & secondary school_ anan samari unguwar da ma Wanda suke zuwa daga wasu unguwanni suke buga _ball_ kasancewar filin makarantar yana da girma sosai kuma anan Haleesa takeda tabbaci gani yaya Habeeb d'inta duk yawan samari da ke cike da wurin hakan bai hanata hango shi, ba tasaki gwaron numfashi, da sauri ta bud'e jakkarta tafito da _exercise book_ had'e da _Biro_ ta yagi _paper_ cikin manya harufa ta rubuta ```I LOVE YOU YAYA HABEEB ``` ta linke takarda.
Tasaki murmushi mai sauti da sauri zainab tajuyo ta kalleta, ta wani tabe baki,Haleesa kuma ta kawarda fuskarta ta cigaba da kallon tauraro da ke haska zuciyarta karaf suka had'a ido yasake mata kyakyawa murmushi taji wani ni'imatace sanyi yaratsa tun daga tafin k'afarta har izuwa kanta ta lumshe idanuta dai-dai lokacin da aka shuro masa _ball_ cikin kwarewa had'e da kwarin guiwa ganita ya shuri _ball_ d'in ae kuwa sai cikin raga 'yan _team_ d'insu suka d'auki ihu had'e da sowa Haleesa batasan lokacin da.....
[20/08 11:44 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```4```
Tace _yeee datz my yaya Habeeb_ da sauri zainab ta taro ta ta hanyar fisgo hannuta, tace kinyi hauka ne _Haleesa?_ ke da kike bisa hanyar zuwa islamiyya miye had'eki da taya 'yan kwallo ihu"?
In tsautsayi ya gita _Allah_ ya jefo mallam faruq yaji kina ihu a hanya ba ruwanshi da shauk'in soyayya ne ya d'ebe ki dukan tsiya zai yi miki.
Duk wannan sarhi da zainab takeyi hankalin Haleesa na wurin yaya Habeeb tana k'are masa kallo sanya yake da _JC_ blue colour da gejere wando k'afafusa sanye da takalmi _ball_ yaya Habeeb ba dogo bane kuma ba za'a kira shi gajere ba yana da _round face_ mai d'auke da d'an siriri gemu na gayu {saboda ba za'a kira wannan gemu da suna na sunnah ba} yana da idanuwa saidai basuda girma sosai hanci sa yana da tsayi ya kuma d'an bud'e fatar jikinsa _chocolate colour ce_ yana da tarin suma akanshi irin wance gayu zamani suke bari.
Cikin gudunsu na 'yan kwallo yanufo wurin Haleesa da zainab, da sauri Haleesa chafki hannu zainab ta rik'e gam yana k'arasowa wurin daf da su Haleesa ta sada kai k'asa yaya Habeeb ya gallawa zainab harara yace ke dai zainab kin shiga tara kullum sai kin sa babylove tayi latti sai na raba muku, jam'iyya sannan za ki yi hankali.
Zainab tayi dariya had'e da cewa ae ni da ka taimake ni domin a lokacin za ka gano tsakani ni da ita waye yake sanya wani latti.
Yaya Habeeb ya lek'a fuskarta yace _babylove d'azu kika jik'ani kamar shuka koh"?_
Haleesa d'ago fuskata cikin muryar shagwaba wance ita kanta batasan lokacin da tayi ta ba saboda in tana gaba yaya Habeeb susucewa takeyi tace, yaya Habeeb kalli yadda kayi zufa, yaya Habeeb yayi murmushi yace wannan zufa lafiya ce tace ko ta wahala ba haka kawai ka dinga wahalarda kanka ga shi ni kuma bana kaunar abunda zai wahalarda da kai.
karaf zainab tace dallah malama wuce mu tafi, da sauri Haleesa ta mik'a masa takarda hannuta, da cikin zumud'i yaya Habeeb ya kar6a yace _love letter"?_
Haleesa ta lumshe idanu had'e da d'aga masa kai yace _thanks my love_ zainab ta tabe baki tafisgo hannun Haleesa da k'arfi tace zo mu tafi _Juliet_ in har na biye miki za mu kai mu iya kai gobe anan kina kallon _Romeo_ ba tare da kin gaji ba.
Yaya Habeeb yace ke banaso iskanci ki ja min ita a hankali kada ki ji mata ciwo, zainab ta taro baki had'e da cewa to so kake yi mu k'ara yi latti a dake mu.
A dakeki dai domin ita ba Wanda isa yata6a ta, zainab ta kalle Haleesa suka kyalkyale da dariya zainab tace kinji wani sabon fi'eli koh"?
Haleesa tayi murmushi had'e da cewa yaya Habeeb kenan yana matuk'ar ji da ni tamakar tsoka d'aya a miya kamar ance Hal tajuya yaya Habeeb yananan tsaye Inda suka barshi yana, kallonsu ya d'aga takarda da ta bashi ya sumbace ta had'e da mannata a k'irji daga bisani ya bud'e takarda idanu shi suka hasko masa abinda Haleesa ta rubuta cikin d'aga murya yace ```I love you too Haleesa ``` da sauri ta rufe fuskarta zainab tace soyayyarku na matuk'ar burgeni Haleesa narasa gane tsakani ke da yaya Habeeb wayafi son wani"?
Haleesa tayi murmushi daga bisani tace zainab kenan ni kam ina da tabbaci son da nake ma yaya Habeeb yafi Wanda yake mini ina tsanani, son yaya Habeeb tamkar yadda uwa takeso d'anta duk buguwa numfashina, yana bugawa ne tare da kwayar son yaya Habeeb in har narasa shi tabbas rayuwata za ta tagaryara zan shiga k'unci mafi muni a rayuwa, ina sonshi wallahi zainab ina tsanani son yaya Habeeb soyayyarshi za ta iya jefani a kowane irin hali tak'arasa magana hawaye na zuba daga idanuta.....
```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S```
Jeeddah Aliyu🌹
[24/08 8:51 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [24/08 7:16 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love❣_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```6```