← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 95

Sashe 50

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

~~Ammi na zaune tsakiyar gida Haleesa tafad'o kamar daga sama, ta fad'a jikinta tak'ak'ame ta _lafiya ki ka shigo min a firgice daga ina kike"?_
A lokaci guda Ammi ta aikawa Haleesa tagwaye tambayoyi
_Ammi yaya Habeeb na gani a k'ofar gida yana sanye da kayan Ball dama Ammi ana mutuwa adawo ko yaya Habeeb fatalwa ya yi"?_
Mtwww.....Ammi ta ja dogon tsoki cike da jin haushin ta yakice Haleesa daga, jikinta Anyya Haleesa mutuwa Habeebu bata ta6a kwakwalwarki ba"?
Haleesa ta yi duru-duru da idanu hawaye da majina suna ambaliya akan fuskarta Allah Ammi yaya Habeeb na gani tak'arasa magana cikin shasshek'a
Gafara chan shashasha banza da wofi yadda kwakwalwarki ta toshe kina tsanmani kowa haka yake Habeebu yatafi Haleesa bara yata6a dawowa ki sawa zuciyarki salama ki rungume mijiinki kada ki 6ata rawanki da tsalle.
Haleesa ta share hawaye da gefen mayafinta
A k'ofar gida kuma Hasheem na gani Haleesa tashiga gida da gudu zuciyarshi ta tsinke musanmman da ya ga mijinta tsaye ya hard'e hannaye fuskarshi babu annuri, cikin rashin k'uzari yanufi wurin Habeeb a zuciyarshi yana addu'ar Allah yasa Haleesa ba matsala tasamu da mijinta, sallama ya yi wa Habeeb had'e da mik'a masa hannu
Bala ne ya amsawa Hasheem sallama, a maimako Habeeb ya bai wa Hasheem hannu sunyi musabaha sai kawai yad'aga masa hannu da sauri Bala yad'anki hannun Hasheem suka gaisa a mutunce sa6ani Habeeb da ke tsaye k'ik'an yana operating phone d'inshi kamar bai Sam da tsayuwa Hasheeem a wurin
"Jiki ba lakka Hasheem Yajuya yashiga gidansu Haleesa zuciyarshi na aiyana masa Haleesa matsala tasamu da mijinta, da sallama yashiga gidan a firgice Haleesa tad'ago tana kallonshi, tasauke k'arfafa ajiyar zuciya ba shakka yaya Hasheem ne nagani zuciyata tabani yaya Habeeb ne
Tuni Ammi tagano Hasheem ne Haleesa tagani ba Habeeb domin tsanani kama Hasheem da shi yake da Habeeb sai ka kwatar da hankalinka za gano banbancinsu
_Ammi lafiya wannan bak'auya amarya ta zo mana gida"?_
Idanun Haleesa na tsiyaya hawaye ta galla masa harara Ammi ta sanarda shi tabargaza da Haleesa tashigo da ita dariya sosai Hasheem ya yi gaskiya Haleesa Yakamata zuwa wannan lokacin ki fitarda yaya Habeeb daga ranki a dalilin ka sa cire shi daga zuciyarki yasa yafara yi min gizo
''Haleesa ta galla masa harara da jajaye idanunta har da laifinka yaya Hasheem me yasa ka sanya JC d'in da yaya Habeeb yake amfani da shi baya kuma kasan kun yi kama saida yafika kyau tak'arasa magana tana murgud'a baki
Hasheem yarufe baki yana dariya bisa wannan dalili naki zai sa na fasa amfani da JC da raina yakeso"?
Ammi ce takar6e zance ta hanyar cewa rabuda ita kawai Hasheemu tsabar shirme ta ne, ya motsa
Hasheem yana dariya ya mik'e Ammi ni zan wuce gida na ji amfara kiran sallah magariba har ya juya yak'ara dawowa Ammi ba fa Haleesa ita kadai bace tare take da Habeeb Lamido yana k'ofar gida''
A tsorace Haleesa tad'ago sai lokacin ta tuna da Habeeb Lamido nan take gargad'i shi yafad'o mata a rai.
"Ammi ta girgiza kai had'e da cewa Allah yaye miki wannan matsala Haleesa don lamarinki sai addu'a Hasheemu kace da shi yashigo Hasheem yafice a k'ofar gida ya tarar da Habeeb yana alwala da roba ruwan faro Hasheem yadanne zuciyarshi yace "Yalla6ai da ka bari na kawo maka buta
Fuskar nan a had'e yad'ago karka damu abokinaa na gode
Bala ya yi karaf yace ni ka kawo min a matse nake ina so in kama ruwa
Wani mugun kallon Habeeb ya watsa masa da sauri Bala yadauke kai tamkar bai ga kallon da Habeeb yake masa Hasheem yashiga gida bai jima ba yafito sanye da jallabiya hannunshi d'auke da buta ya mik'awa Bala
Habeeb yace abokinaa ina zan sami masallaci mu je na nuna maka yana farko layi watakila don ba ka lura bane da za Ku shigo da ka ganshi
Humm....Habeeb yafad'a a takaice
Ammi ta dube Haleesa tace har tsawon wane lokacin za ki dauka kafin ki dawo mutum"?
Haleesa ta sada kai k'asa tarasa amsa da za ta ba Ammi
Wannan ya ba Ammi dama tasoma yi mata fad'a mai had'e da Nasiha daga bisani tace tashi ki je ki yi sallah Haleesa ta tashi jiki a sanyaye Imaan tashigo da 'yar sallama ta Haleesa tariko hannunta
Ammi na ganinta tagane ita ce 'yar Habeeb Lamido
Akan hanyar su Habeeb na zuwa masallaci idanunshi suka sauka bisa symbol na ```Ni da yaya Habeeb tailoring center ``` rubutu ya ja hankalinshi har yatuna da zobe Haleesa da ta ta6a yarwa a Lagos yatsinta, a zuciyarshi yace _Humm..... Wannan Habeeb d'in yana da matuk'ar mahimanci a rayuwa Haleesa ya riga yagama da zuciyarta shine ni kuma mom ta had'ani da ita yaushe na ke da lokacin soyayya da k'aramar yarinya ae sai ajina ya zube_
Ya wani tabe baki a haka suka k'arasa masallaci saida ya jira akayi sallah isha'e sannan yafito, a k'ofar masallaci yatarar da Bala da Hasheem sai kuma salman da yazama ciko na ukunsu suna fira, yadda a kullum abinci Kara tsada yake rayuwa talaka Nigeria tadawo abar tausayi, abunda ya ji Bala yana fad'a kenan Habeeb ya girgiza kai a zuciyarshi yace su Bala an sami abunda akeso kalli yadda ya karkace baki yana zuba yak'arasa wurinsu ya gaisa da yaya salman daga bisani suka dunguma zuwa gida akan hanya Habeeb yake sanarda yaya salman tafiyar Haleesa abuja cikin sigar zolaya yaya salman yace _yalla6ai kace za ka k'ara nisantani da k'anwataa"?_
Murmushin k'arfin Hali Habeeb Lamido ya yi a cikin zuciyarshi yace dama za ka rabani da ita da ka taimakawa rayuwata, a baiyane kuma sai yace mafi yawa hark'oki na nafi yi su a abuja da Lagos ka ga bai kamata ina abuja k'anwarka tana yola ae sai ka zargeni da rashin bata kulawa yaya salman ya yi 'yar dariya had'e da cewa wannan gaskiya ne yalla6ai da haka suka k'arasa k'ofar gida, yaya salman ya yi wa Habeeb iso zuwa cikin gida har k'asa Habeeb ya durk'usa ya gaida Ammi yaya salman yace Ammi ina Haleesa"?
Ammi tace tana d'akinta
Yaya salman yanufi d'akin ya tarar da ita tana sallah yajuyo yace Ammi sallah ta ke yi in tagama ki ce da ita zan kirata a waya saboda sauri nake zan koma shago akwai Wanda yake jirana yaya salman ya sake mik'a wa Habeeb Lamido hannu sukayi musabaha salman yafice
Imaan da ke zaune a gefen Ammi tana ci tuwo tace Daddy Ammi tabani tuwo mai dad'i
Habeeb ya yi murmushin yak'e yace to yi maza ki cinye karki ragewa Bala
Ae kuwa da sauri Imaan ta yaki katuwar loma Ammi na mata dariya
"Shiru-shiru Haleesa bata fito ba yayin da Habeeb yake duba wrist watch d'in ke daure a hannunshi Haleesa kuwa tana gama sallah ta haye mattress ta kwance rub da ciki ganin Hasheem da ta yi yataso mata da tsohu mik'i na rashin yaya Habeeb a hankali take rera kuka
Habeeb yak'ara duba agogo hannunshi ya ga _9:00pm_ ta yi ga shi kuma yanada appointment da manager company shi sun yi da shi za su had'u k'arfe _8:30pm_ duk duniya ba abunda Habeeb ya tsana irin sa6a alk'awali yana matuk'ar girmama lokacin yawan duba agogo da yakeyi ya ankarar da Ammi tace wai wace irin sallah ce Haleesa take yi"?
Da sauri Habeeb yace Ammi bara na duba ta ya mik'e yanufi d'akin a dai-dai k'ofa ya tsaya kamar mai shawara daga bisani ya yanke shawara shiga ya bankad'ala curtain{lubulle} yana shiga idanunshi suka sauka bisa bango d'akin hotuna marigayi yaya Habeeb ne birjik kowane hoto Haleesa ta yi rubuta kalamai soyayya masu zafi a k'asa shi a hankali Habeeb Lamido yake karanta rubutu _I love you yaya Habeeb I can't live without you_
_you are d only men I love live without you is miserable_
_I love you yaya Habeeb more than my own life I will continue to love you for d rest of my life_
Da sauri Habeeb Lamido yadauke idanunshi ya mayarda akan mattress ke! Ya kira Haleesa shiru ko motsi bata yi ba jin yake yi kamar ya narka mata mugun bugu a gadon bayanta, amma yana ji tsoro kada ta kurma ihu Ammi ta ji sannu a hankali yakai hannunshi kamar Wanda zai ta6a kashi ya d'an bubbuga bayanta ke! Bacci ki ka yi ne"?
A firgice Haleesa ta mik'e zaune rigarta ta yaye cinyoyinta suka baiyana ta ja baya ta jigina a bango ta yi duru-duru da jajaye idanuta
Habeeb ya kafa wa cinyoyinta ido take ya tuna da mafalki da yata6a yi ya ja iska yayin da Haleesa ta kafe shi da ido yad'ago yana tsotsa bakinshi kamar mai tsotsa sweet kallon ido cikin ido su ka yi wa junansu Haleesa ce tafara d'auke idanunta saboda bara ta jure cigaba da kallo eye's ball d'in shi yana mata kwarjini matuk'a a zuciyarta tace ina mamaki wannan d'abi'a ta yaya Habeeb sai dinga Jan iska kamar Wanda yaci yaji ga wani tsotsa baki da yake kamar mai sha sweet kuma da alama wannan d'abi'a ta bi jikinsa amma fa wannan d'abi'ar tashi tana burgeni kuma tak'ara masa kyau kai Habeeb Lamido kyakyawa ne ajin farko "Habeeb Lamido yak'ara yadda ganinshi akan jela gashin kanta da ke reto a bayanta a cikin zuciyarshi yace _ashe yarinya nan 'yar duniya ce hadda attachment take sakawa na tsani mace mai saka gashin doki_
Ya ja tsoki yak'ara murtuk'e fuska ke ki tashi mu tafi mana gaba d'aya Haleesa ta rikice jikinta na rawa ta d'auki mayafinta yana gaba tana biye da shi a bakin k'ofar Ammi ya tsaye ya yi mata sallama yaciro bundle na 'yan N1000 ya ajiye mata yafice da sauri domin yasan halin Ammi za ta iya cewa bara ta k'ar6a ba Haleesa tadauke imaan wance tuni ta yi bacci Ammi tak'ara gargad'i Haleesa ta bi mijinta sau da k'afa a k'ofa gida Haleesa ta tararda Habeeb da baffanta suna fira ta runsuna ta gaida baffa a gurguje tashiga gidansu marigayi yaya Habeeb ta gaida inna mairo zainab ta yo mata rakiya sai fama tsokana ta take yi ita ma kyautar kud'i Habeeb ya yi mata Ya kuma bata bundle gudu biyu yace bayan yatafi ta ba wa baffa da baba Audu domin yasan matuk'ar ya basu da kanshi bara su k'ar6a ba Bala ya bud'e musu k'ofar mota Haleesa ta zauna a seat d'in baya tana rungume da Imaan tun lokacin da suka d'auki hanya sanyi Ac ya ratsa Haleesa tafara gyagyadd'i a k'ofar gidan Alhaji bashir manager Bala ya yi parking Habeeb yafice yanufi cikin gidan yabar Haleesa da Bala a mota Bala yana ta zubawa Haleesa surutu tun tana bashi amsa har bacci ya yi nasara d'auke ta sai misali karfe _10:30pm_ Habeeb yafito daga gidan Bashir manager a lokacin tuni Haleesa ta yi nisa da bacci "Bala ya dube Habeeb yace Boss mutane nan naka gaba d'ayansu sun yi bacci
Habeeb ya mak'e kafad'a alama I don't care har suka isa gida Haleesa batasaniba tana ta sharar bacci Bala ya yi parking Habeeb yafito dauke Imaan daga jikin Haleesa yasoma tayar da ita ke tashi mu iso gida Haleesa ta yi wani juyi ta gyara kwanciyarta
Bala yayi karaf yace Boss yadda ka ga amarya ta gyara kwanciyata za Ka iya kai gobe kana tayar da ita bata tashi ba kawo Imaan na shiga da ita ciki ka dauki Haleesa Habeeb ya galla masa harara angaya maka ni d'an dako ne da zan d'auke ta"?
boss ba fa yau kafara daukarta ballatana nace abun zai zo maka banbarankwai
Cike da jin haushi Habeeb ya ja tsoki ya sunkuya yadauke Haleesa ya ji kamar yadauki Imaan Sam bata da nauyi a parlour ya shinfid'e ta bisa 3 sitter ya karbi Imaan yakaita bedroom Bala ya yi masa sai sa safe yafice Habeeb ya yi tsaye yana kallon Haleesa nan take ya kudurta wani Abu a cikin zuciyarshi yasaki murmushi mugunta...........
Chapter 50 · 0% Book details