← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 95

Sashe 87

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```97```

~~Ban amince ba sai ka yi hak'uri har watani 3 su cika ni kuma nayi maka alqawali koda mom batace nadawo ba zan baka izzini ka zo ka yi mata magana, amma gaskiya yanzu Uhm...Uhm...in fact 2 weeks kawai ka yi.
"Ajiyar Zuciya Habeeb ya yi shikenan Leesa tun da haka ki ka za6a mana amma inason kisani hakan ba k'aramin cutar da ni yake yi ba.
"Ae ba kai kadai yake cutar wa ba nima inajin jiki daurewa kawai nake yi
Hum....fad'a kawai ki ke yi Leesa da rashina yana cutar da ke da ba Ki bijiro da wannan buk'ata ba don haka mu ajiye wannan zance a gefe d'aya domin cigaba da yi sa zai iya 6ata mun rai.
"Murmushi Haleesa ta yi da yafi domin nima ba amincewa zan yi da buk'atarka ba.
Wannan kuma ke ta Shafa ni nasan yadda ki ke sona "you can't live without me za ki gaji da shirme ki ne kidawo gareni.
''Oho!..tun da kasan da haka miye na wani dauko zance"?
Lumshe idanu ya yi kamar ba za yi magana ba daga bisani ya shafi sumar kanshi, saboda inasonki Leesa, nisanta daga gareki zai iya haddasa mun gagarumar matsala.
''Nima inasonka yaya Habeeb so da baki ba zai iya misalta shi ba amma kasani ba zan dawo gare ka ba har sai nan da wata uku.
"A tak'aice duk yanda Habeeb yaso ya shawo kan Haleesa cikin sauk'i abin ya fask'ara ta tsaya kai da fata ita lalle-lalle sai yacika watani 3 ko za ta dawo gidanshi daga karshe ma sai suka rabu baran-baran kawanensu ya aje waya a fusace.
"Hannah da ke kwance a gefen Haleesa ta kwashe da dariya lovebirds ya haka ashe za Ku iya fad'a da junanku"?
Mtsww.....Haleesa ta ja tsaki Hannah yayanki Zuma ne sai da wuta har abada ba zai daina wannan d'abi'a nashi na sauri d'aukar abu da zafi ba.
"Tabe baki Hannah ta yi tace ae ba zai daina ba saboda a jininsa yake.
Ae kuwa yana tare da aiki Haleesa tafad'a had'e da make kafad'a.

```HABEEB```

Yana gama waya da Haleesa ya ji a ranshi zai nisanta kanshi daga gareta har wa'adin da ta deba masa yacika a washe gari ya tattara kayanshi ya yi kaura zuwa Lagos har yadira a Lagos bai nemi Haleesa ba yayinda ita ma bata nemi shi ba su dole fushi suke yi da juna.

_5 day's later_

Habeeb yagaji da shan k'amshin sa yakira Haleesa a lokacin tana zaune a parlour ita da Hannah madam kuma tafita she's always busy saboda lokacin bikin Hannah da yakarato.
''Saida wayar ta yi kusan tsinkewa sannan Haleesa ta d'aga adak'ile tace _Hello_
"Leesa kina mun wulaqancin ko don kinga ina sonki ne"?
_sarkin korafi ae ka jira mu gaisa kafin kafara kwararo min k'orafin naka"?_
Haka ma za ki fad'a"?
_Nop...kawai naga dacewar hakan ne amma in bakaso gaisuwa nawa sai na rik'e abina_
"To ki rik'e abarki banaso kin damu da ni ne da har za ki gaida ni"?
_Hum....ni kuwa na damu da kai_
''Kin damu da ni miyasa ba ki nemi ni ba"?
_saboda kana fushi da ni kuma iya sanani bansan nayi maka laifi ba_
"Murmushi ya yi yanzu dai na d'auki laifina tun da gashi na kira ki sai kuma ya canza zance, ta hanyar cewa Leesa nayi missing naki fa Allah da kyar nake iya bacci.
Dariya Haleesa ta yi my handsome Don kenan ko za ka zo ne mom tafita daga ni sai Hannah ne kadai a gida"?
"Iska ya ja kamar ba zai yi magana ba daga bisani yace ke ni fa ina Lagos tun washe gari da ki ka 6ata mun rai na baro abuja.
''Shikenan ka yi wa kanka
"Habeeb ya yi dariya bani kadai na yi wa kaina ba ke ma kinyi wa kanki, saboda kin yi missing gani kyakyawar fuskata.
_Uhm....kamar yanda kaima ka yi missing gani kyakyawar fuskata ba_
"Zancenki ba karya Leesa ke kyakyawa ce ga kyau fuska ga kuma kyau hali shiyasa duk lokacin da na tuna da ke sai na godewa ubangiji da albarkace ni da samun ki.
Ajiyar zuciya Haleesa ta yi yayinda Habeeb yacigaba da kwararo mata zazzafan kalaman soyayya daga bisani yake sanarda ita gobe Imaan za ta dawo Haleesa tadinga ihun murna saboda ta yi kewar Imaan ba kad'an ba gani yanda take ihu yasa yace ke in gama ihunki anjima zan kira ki kafin Haleesa tak'ara magana har ya yi hanging up.

_washe gari_

Maryam tadira garin Abuja tare da Imaan kyakyawar tarba Haleesa da Hannah suka yi mata kasa sake jiki ta yi sai wani d'ari-d'ari, take saboda kunyar Haleesa take ji musanman in ta tuno da yankar k'auna da ta yi wa akan Habeeb sai gashi kuma za ta aure d'an uwan Haleesa da kyar Haleesa ta shawo kanta tasaki jikinta suka sha hira Hannah na tsokanar maryam ta hanyar cewa kishiyar Haleesa ada matar yayan Haleesa a yanzu kwanan Maryam 2 a abuja ta juya Yola.
Tsakanin Habeeb da Haleesa saidai su yi waya yini Haleesa take bata fito parlour ba tana d'akin k'unshe tana zuba wayar soyayya da Habeeb a kwana a tashi asarar mai rai gashi har Habeeb ya yi cinye watani 2 daga cikin watani 3 har tsawon wannan lokacin Habeeb bai tako k'afarsa Abuja ba a bisa alqawalin da yadaukawa kanshi ba zai k'ara zuwa inda Haleesa take ba har sai wa'adin watani 3 sun cika.
Lokacin bikin Hannah yak'araso wannan yasa madam ta tattaro su Haleesa suka nufi garin Yola saboda anan za'a gudanarda shagalin biki.
Chapter 87 · 0% Book details