← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 95

Sashe 52

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

~~I'm sorry yaya Habeeb lokacin da ka Kira ina sallah.
A Canada kuma Habeeb na kwance akan kujera a bakin swimming pool na takatafare Hotel d'in da yasauka ya shafi lallausar suma kanshi idanunshi a rufe yacigaba da magana da Haleesa _ranar Monday Mus'ab zai zo ya kai Imaan school ki shirya mata da wuri_
okay Haleesa tafad'a cikin siririya murya
_I hope ba wani matsala"?_
Haleesa tace nop
_Good Ina Imaan"?_
''Tana parlour tare da Hannah
_okay ki bata waya_
Haleesa ta mik'e da sauri tanufi parlour bara na kai mata
_karki yi hanging up yafad'a a kasalance_
''Imaan zo ki yi magana da Daddy da gudu Imaan ta taso ta k'ar6e wayan daga hannun Haleesa tasoma zubawa Habeeb surutu ''Daddy kasiyo min biscuit da chocolate da elephant da kuma snake.
Murmushi Habeeb ya yi my Angel bara ki bari mu gaisa, ba kin fara wannan lissafi naki da baya k'arewa to naji duk abunda kike so zan siyo miki _promise to me za ki yi karatu sosai banda wasa kinji my Angel"?_
"Yes Daddy I promise you kai ma Daddy karka manta da alk'awalina
"By God great bara manta ba ki gaida aunty Hannah ya yi hanging up.
Imaan ta mik'awa Haleesa wayarta ta kuma Isar da sak'on Habeeb wurin Hannah.
*********************
_4 Day's later_
Haleesa da Hannah na tsaye cikin kitchen Haleesa na yanka cabbage Hannah kuma, tana yanka albasa.
''Imaan tashigo da gudu rik'e da wayan Haleesa aunty ankira wayanki
Da sauri Haleesa ta k'ar6i wayan daga hannun Imaan, ganin sunan yaya Habeeb akan screen ya yi mugun jefata cikin rud'ani hannunta na rawa ta yi "received
_Hello_
Cikin tsawa yace ke! Dallah ki ba wa Imaan waya duk lokacin da na Kira ki sai kinyi wasting time d'ina yak'arasa magana had'e da Jan dogon tsoki.
Jikinta a sanyaye ta mik'awa Imaan waya tace yi ki magana Daddynki ne tajuya tacigaba da aikinta duk abunda ke faruwa Hannah na tsaye rik'e da wuk'a tana, kallonsu.
Ta tayi shiru tana nazari yanayi sauyin fuskar Haleesa alama ce da ke nuna akwai abunda Habeeb yafada mata Wanda yayi sanadi sauyawarta a lokacin d'aya tajuya wurin Imaan da ke ta fama zuba wa Daddy ta surutu.
tace Imaan ki je parlour ki yi waya da Daddy, Imaan tafice tadafa kafad'a Haleesa karki 6oye min Haleesa domin ko kin 6oye min a matsayin shekaru da nakeda su zan iya fahimtar wani abu kinga kenan 6oyewa batada amfani, kuma na tabbata a halin da kike ciki kinada buk'atar abokin shawara.
Ta d'an dakata domin ta ji ta bakin Haleesa
''Hawaye suka cika idanun Haleesa cikin murya da ke nuna tanaso yin kuka tafara magana me zan 6oye miki Hannah''?
Iya sanina kinsan duk abunda ke faruwa tsakanina da yayanki har izuwa yanzu bata chanza zani ba.
''I known Haleesa but kema yakamata ki yi amfani da baiwar da Allah yabaki, ta 'ya mace ki janyo hankalin mijinki zuwa gareki.
A yatsine Haleesa take kallon Hannah daga bisani tace akan wane dalili zan 6atawa kaina lokacin in janyo hankalinshi gareni angaya miki ina sonshi ne"?
''Hannah ta girgiza Kai ko bakya sonshi nasan bara ki so aurenki ya mutu ko za ki so ki shiga layin k'anana zawarawa"?
"Jikin Haleesa ya yi sanyi ta yi shiru tana kallon Hannah had'e da nazari kalamanta daga bisani tace Hannah ya kike so nayi shi da yake d'an namiji bai nuna ra'ayi akaina sai nice zan nuna gaskiya ni bara iya ba ke ni fa ko k'amshin turare yaya Habeeb naji sai gaba na yafad'i tak'arasa magana had'e da murgud'a baki.
''Hannah ta yi dariya tace ni kuma me ye laifi na da kike murgud'a min baki daga ke har yaya Habeeb bara Ku ta6a iya gujewa k'addarar da ''Allah ya yi nufi akanku duk wannan noke-noke za Ku gama ne kudawo kan hanya.
''Haleesa ta tabe baki kanki akeji na fahimce cewa bakida aiki yi shiyasa kike yunk'uri cusa mini d'an uwanki ba kuma zai ta6a samun matsayi anan wuri ta nuna k'irjinta da yatsa.
"Hannah ta girgiza kai bata k'ara cewa da ita komai ba tacigaba da yanka albasa.
******************
_1 week later_
Around _2:00 o'clock_ na dare flight d'in su Habeeb yayi landing sa'eed ya zo ya yi picking nasu da yake part d'inshi yanada tazara da na Haleesa har washe gari batasan yadawo ba.
"Tun da asuba Haleesa ta falka bata k'ara komawa bacci ba saboda za ta shirya Imaan zuwa school _7:20am_ ta gama shirya Imaan
"Haleesa ta dube imaan tace bara naje na dauko miki launch box d'inki.
Imaan tace aunty ba ki bani Chocolate ba
Na saka miki a schoolbag d'inki''
a kitchen ta tararda Peter yana had'a breakfast peter ina lunch box d'in Imaan''?
Ya nuna mata da yatsanshi da sauri ta sunkuce lunch box d'in ta kuma rik'o hannun Imaan tanufi compound da ita saida suka kai parking space Imaan tasa rigima tana magana had'e da bubbuga k'afafu a k'asa _Allah aunty ni yau bara je school uncle Ezekiel duka na yake yi_
''Haleesa ta dafe goshi tasoma rarrashinta haba imaan a kullum za ki tafi school sai mu zo mota kike saka rigima kinga shiga mota Ku tafi zan kira uncle Ezekiel a waya ba zai dake ki ba kinji"?
Cikin jin dad'i Imaan ta daka tsalle sa'eed na ta fama yi musu Haleesa ta bud'e mata k'ofa oya zo ki shiga kada ki yi latti Imaan tashiga mota sa'eed ya ja _bye bye aunty ki had'a mini chocolate cake kafin nadawo_
Haleesa na dariya tace _bye babynaa zan had'a miki ke kuma ki yi karatu sosai_
Saida ta ga motarsu tafita gate sannan tajuya cikin gida.
Duk abunda ke faruwa tsakanin Haleesa da Imaan Habeeb Lamido na tsaye a balcony da ke sama yana kallonsu idanunshi na kan Haleesa har ta6acewa ganinsa ya ja iska had'e da lumshe ido.
''Haleesa na shiga parlour taci Karo da Hannah sanya da sports wear's ke nake jira mu fita exercise
Haleesa tabe baki bacci nakeji bara iya zuwa ba
Wane irin bacci Dan Allah ki zo mu je banaso "fat ya yi miki yawa kada yaya Habeeb ya auro 'yar shila.
Mtww...Haleesa ta ja tsoki had'e da shigewa bedroom da kyar Hannah ta ciyo kanta ta amince suka fita compound bayan sun gama jogging suka nufi wurin snooker tun da suka fara buga wasan Hannah ce take winning saboda Haleesa ba iyawa ta yi ba in ta daki ball da stick sai ya yi tsalle yafad'i Hannah ta kwashe da dariya.
Habeeb yadawo daga jogging Bala na biye da shi tun daga main gate ya hango Haleesa da Hannah kaitsaye yanufi wurinsu Hannah nagani shi, ta washe hak'ora tuni Haleesa ta nemi natsuwarta rasa sai gumi ke tsatsafo mata.
Yaya Habeeb saukar yaushe"?
_Jiya da dare yafad'a chan k'asan mak'oshi_
Haleesa tasauke ajiyar zuwa wance ta janyo hankalin Habeeb yasoma yi mata kallon da ta tsana......

Jeeddah Aliyu🌹

[16/11 7:04 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```71```

_this page is dedicated 2 u *Firdausi Sodangi* thanks 4 the love & care_
Chapter 52 · 0% Book details