← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 95

Sashe 91

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dr Khaleesat Haydar tadanno hancin motarta kirar Lexus 2016 model a farfajiyar gidan madam Hindu tanufi parking lot ta yi parking k'afafunta suka Fara fitowa daga bisani gangar Jikinta ta baiyana sanyeta ke da Arabian gown Blue colour ta yi rolling da pink colour veil kwayar idonta na lullu6e da farin gilashi ta bud'e seat d'in baya tadauko briefcase d'inta mai d'auke da kayan duba marar lafiya cikin takonta na k'assaita tanufi cikin gida a parlour taci karo da madam Hindu tana fitowa daga d'akin da Haleesa take ciki madam Hindu ta washe hak'ora ki k'araso daga ciki Dr madam Hindu tak'arasa magana had'e da juyawa cikin d'akin na Haleesa yayinda Dr Khaleesat ta Mara mata baya Haleesa na kwance kamar yanda madam tafita tabarta a kwance Haleesa nagani Dr Khaleesat ta mik'e zaune tana yatsinar fuska, Dr Khaleesat ta nemi kusa da ita ta zauna tayi mata ya jiki daga bisani tashiga watsa mata tambayoyi meke damunki"?
"Jiri da tashin zuciya
tsawon wane lokacin ki ka dauka kina jin wannan yanayi"?
Yau da safe
Yaushe rabonki da ganin period d'inki"?
''Rass.......rasss..... Gaban Haleesa yagad'i tad'ago a rikice tana kallon Dr Khaleesat daga bisani ta sadda kai k'asa cike da jin kunya tace almost 2 months"
Murmushi Dr Khaleesat ta yi ta bud'e briefcase dinta tafito 'yar k'aramar roba ta mik'awa Haleesa tashi ki Shiga bathroom ki yi fitsari a ciki inaso na k'ara tabbatar da abunda nake tunani jikin Haleesa a sa6ule tasauka daga kan gado tashiga bathroom bata jima da shiga ciki ba tafito rik'e da robar mai d'auke da fitsari ta mik'awa Dr Khaleesat "pregnancy test strip Urine Dr Khaleesat tadauko ta tsoma cikin fitsarin ta ajiye a gefe after 3- 5 minutes tadauko yanuna jajaye layi guda biyu alama ce da ke nuna positive Dr Khaleesat tafad'ad'a murmushinta ta dube madam Hindu congratulation! Madam kin yi kusa samun maigida ko kishiya tak'arasa magana cikin dariya.
Masha Allah! Masha Allah! Abunda madam Hindu ke maimaitawa kenan ta rungume Haleesa, tana mata sannu yayinda Dr Khaleesat ta rubuta mata magunguna masu k'ara kuzari da k'arawa abunda ke cikinta lafiya ta mik'awa madam Hindu takarda ta mik'e tsaye had'e da cewa madam ni zan k'arasa gida insha Allah zuwa jibin zan leqa gidan amarya Hannah mu gaisa madam tabi bayanta tana zuba mata Godiya.
''Suna fita Haleesa ta kifa kanta a pillow tashiga rera kuka, tsananin kunya ya lullu6e ta yanzu da wane ido za ta kalli mom saboda mom tasan cewa yau tsawon watani biyu kenan da kafawa Habeeb sharad'in sai gashi cikin wata biyu ya baiyana a jikinta kenan yanzu mom za ta gano tana kula Habeeb duk da gargad'in da take mata akan karta kulashi har sai yacinye Watani 3 kuka Haleesa tashiga rerawa sanadin kuka da ta yi ya janyo mata ciwon kai.

_14 minutes later_

Madam Hindu ta turo k'ofar d'akin Haleesa tashigo hannunta rik'e da ledar magani d'ayan hannunta d'auke da robar ruwan Faro da glass cup jin motsinta yasa da sauri Haleesa ta rufe idanunta, madam ta zauna kusa da ita Haleesa, Haleesa tashi ki sha magani, a kunyace ta tashi madam ta balle tablets d'in ta mik'a mata ta tsiyaya ruwa a cup tabata batare da Haleesa ta dube ta ba kar6i ruwan tashanye maganin.
"Kwanta ki yi baccinki saboda kina buk'atar hutu madam tafad'a had'e da mak'ewa tsaye Haleesa ta kwanta sannan madam tajuya tafita.
''Haleesa nagani madam tafita tararume Hijab tasaka ta zura bathroom slippers ta bud'e k'ofa a hankali ta leqa parlour, tak'arewa mutane da ke parlour kallo taga madam Hindu bata cikinsu wuf.....ta yi tafito tanufi k'ofar fita cikin sauri tanufi gate ta bud'e k'aramar k'ofa tafita tana tana k'arasawa titi ta tare mai adaidata Saida tashiga suka d'auki hanya sannan tafad'a masa sunan unguwar da za ta je.
"Tun daga shigarta unguwarsu tafara cin karo da abun mamaki _Ni da yaya Habeeb tailoring center_ yadawo babban shago painting shagon kadai abun kallo ne bata k'ara shiga rud'u da firgitarwa ba saida takai k'ofar gidansu daga gidansu har na su margayi Yaya Habeeb ya sauya, a rikice tafito daga adaidaita tasaki baki da hancinta tana kallon gate d'in gidansu jin an turo k'ofar yasa takara ware idanunta sosai taga mai fitowa addu'a take yi a zuciyarta Allah yasa iyayyenta ba siyarda gidajensu suka yi ba kamal tagani yafito yana ganinta yadaka tsalle ya rungumeta muryarta na rawa tace kamal me ke faruwa ne naga sauyi a gidanmu da na baba Audu"?
"Kamal ya yi dariya yace aunty Haleesa ki sallame mai adaidaita ki barshi tsaye sai lokacin Haleesa ta tuna da bata fito da ko fika ba ta mayarda ganinta ga hannun kamal, N500 tagani rik'e da hannunshi tace kamal ban fito da k'udi ba ko za ka iya biyanshi"?
Kamal yajuya yanufi wajen mai adaidaita ya biya shi kud'inshi sannan yadawo wajen Haleesa, wance ke tsaye da d'ibin mamaki lullu6e da ita muryar kamal ce ta yi nasara dawowa da ita natsuwarta.
"Duk wannan sauyin da ki ka gani aikin yaya Habeeb ne.
"Zaro ido ta yi wane yaya Habeeb ka ke nufi"?
Yaya Habeeb d'inki mana
Hum....kamal kana k'ara jefani cikin rud'ani yaya Habeeb Lamido nake nufi shine ya gyara mana wannan gyara da ki ke gani ba ma wannan kadai ba ya ba wa yaya salman aiki company shi ya bashi gida da mota wai za'a dinga cirewa cikin salary shi, ya gyara _ni da yaya Habeeb tailoring centre_ ya zuba Kwararin mad'inka ya kuma biyawa Baffa, Ammi ,Baba Audu da inna mairo makka sai kin Shiga cikin gida za ki ga yanda ya gyara miki d'akinki.
"Har kamal yadasa aya a zancenshi Haleesa na kallonshi baki bud'e Kamal yace aunty Haleesa ki Shiga ciki ni zan tafi Inda Ammi ta aikeni.
"Jikinta a sanyaye tashiga gida ta yi sallama shiru ba Wanda ya amsa kaitsaye tanufi d'akinta duk da taga sauyi tare da d'akin hakan bai hanata gane shi ba ta murd'a handle k'ofar ta bud'e tashiga tsaye ta yi tana k'arewa d'akin kallo everything's dake cikin d'akin red & yellow colour ne a hankali ta mayarda idanunta kan bed Wanda aka qawata shi da bedsheets red & yellow ga wasu teddy bear's jere akan gado murmushi ta yi tanufi bed d'in ta kwanta tad'auki teddy guda ta rungume a k'irjinta
[25/12 1:40 pm] aliyujeeddah: "Ta lumshe idanu tashiga tunanin Habeeb Lamido nan take wani irin sonshi yak'ara samun mafaka a zuciyarta ta k'udiri anniyar kyautata masa za ta guji duk wani abu da zai 6ata masa rai saboda yanzu tak'ara amincewa da irin soyayyar da yake mata ta bud'e idanu da sauri tadauko wayarta ta rubuta mishi text.
_my handsome Don narasa Kalmar da zan yi amfani da ita domin na gode maka saidai zan cigaba da yi maka addu'a ubangiji ya baka masauki a gidan aljanna Firdausi ina mai maka albishir Imaan ta yi kusa samun k'ani ko k'anwa tsananin kunyar mom nakeji yasa na fito batare da saninta ba a yanzu haka ina gidan Ammi. Thanks for everything's tauraro naa_
Ta tura masa ta gyara kwanciyarta tasoma hango irin soyayyar da za su zuba in takoma gidan Habeeb a haka bacci yasud'ad'o ya sace ta.

"Ta6angare madam Hindu kuma tana fitowa daga d'akin da Haleesa take ta lalla6o digit d'in Habeeb ta danna masa kira, yana d'agawa ko gaisuwar shi bata tsaya amsawa ba tace duk abunda ka ke yi ka ajiye ka zo inason ganinka yanzu nan tana k'arasa magana ta hanging up.
Chapter 91 · 0% Book details