← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 95

Sashe 32

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jiki a sa6ule tak'arasa fita Wannan karo ma Bala ne yafito daga cikin mota yak'araso wurinta "Barka da fitowa ranki yadad'e"
Yauwa Bala ya gida"?
Lafiya Qalau ya hidimomi biki"?
Shiru Haleesa ta yi had'e da sada kai k'asa gani yadda ta yi yasa Bala ya yi murmushi yace ba fa ni kadai bane tare nake da "Boss'
Wani fad'uwa gaba Haleesa tak'ara ji tsanani tsoro ya lullu6e ta tamkar mai ciwo hak'ora ta bud'e bakinta tace Bala kace da shi yak'araso ciki ranar ma da na tsaya da shi a k'ofar gida saida Baffa ya yi Fad'a "Bala yace okay ba matsala bara na yi masa magana Bala yanufi wurin mota ya bud'e k'ofar da Habeeb yake Zaune fuskarshi ahad'e ba bu annuri ko misk'arazairatil a tare da shi da alama zuwan sa na dole ne "Boss tace ka shigo daga ciki saboda Baffanta bayaso tsayuwa a k'ofar gida"
A harzuk'e Habeeb ya ke kallon Bala daga bisani yace banida buk'atar shiga gidansu don haka za ka iya bata dalilin zuwa na gidansu"
Ka yi hank'uri "Boss ka daure ka k'arasa daga ciki karka manta ko yanzu kafin mu zo gidanan irin Fad'a da Madam ta dinga yi ta nuna 6aci ranta k'arara a dalilin rashin waiwaye Haleesa da ka yi Yakamata ace ka danne duk wata k'iyayya da ka ke yi mata saboda saura d'a k'ank'ani lokacin ta zama mallaki ka in tashigo gidanka kana da iko yi mata duk abunda ka ga dama ba bai hanaka saboda ikonka ce.
Habeeb yadage gira sama yana duban Bala cike da gansuwa da kalaman Bala yasaki tsadade murmushinsa mai narkar da Zuciyar 'yan mata
Haleesa nagani Bala na musu-musu da baki da alama magiya ya ke yi wa Habeeb haushi ya turnuk'e ta ta juya cikin gida tana shigawo ta ci karo da Ammi sai kawai tace Ammi Key's d'in d'akin yaya Salman za ki bani batare da Ammi tace da ita komai ba tashiga d'aki tadauko mata Key's ta mik'a mata a sanyaye Haleesa tak'ara juyawa k'ofar gida tana fita taci karo da su a bakin k'ofar shigowa Zaure ba shiri ta taka birki had'e da sunkuyar da kai Kallo d'aya Habeeb Lamido ya yi mata ya d'auke kai tsawon "5-6 minutes suka dauka a tsaye daga bisani Haleesa tanufi d'akin yaya salman ta bud'e k'ofa tajuya batare da ta bari sun had'a ido tace "Bissimillah! Banza Habeeb ya yi kamar bai ji abunda tafad'a "Bala yace Boss ka k'arasa daga ciki bara na je na fito da kayan da ke cikin mota Wani tsuke baki Habeeb ya yi kamar mai tsotsa "Sweet ko mai shiri d'aukar selfie ya yi kici-kici da fuska, yajuya ya kalle d'akin yaya Salman Wanda tuni Haleesa ta tsofa a ciki tana jiranshi ya ta6e baki yanufi d'akin batare da yacire "cover shoe d'in k'afarsa kawai yadanna kai Haleesa na Zaune akan kujerar roba kanta na sunkuye tana wasa da yatsu hannunta ''Ba don sani daraja da sallama da ke ita a musulunci da ba yadda za'a yi ya yi mata sallama"
"Assalamu Alaikum" yafad'a chan k'asan mak'oshi''
"Batare da Haleesa tad'ago kanta ta amsa mai masa da cewa "Wa'alaikum sallam warahmatullahi wabarakatih...''
Habeeb ya kya6e baki a zuciyarshi yace ka ji su Al-Sheikh za ki yabawa aya zak'i ta in kika shigo hannuna 'ya nema mai kai Kamar dunk'ule "cabbage' ya ja ya yi tsaye Haleesa bata ce da shi ga wurin zama hakan ne yasa yacigaba da zance zuci tana nufi bara tace na zauna ba amma bara naga iya gudun ruwanta kafin na wanke mata allonta saboda naga kanta na hayak'i.
A fakace Haleesa tad'ago ta sace kallonshi yana nan tsaye k'ikan hannaye shi zube cikin aljihu wandoshi da sauri ta d'auke kai a zuciyata tace tofah wata sabuwa inji 'yan caca shi wannan mai tsawo kamar fol waya yana nufi bai ga wurin zama bane ko kuma duk cikin, salon tsabar kwarewa da wulak'anci ne amma bara nace ya zauna a karo na biyu da tasake d'agowa amma bata dube shi ba tace "please have a seat''
Zaro ido ya yi daga bisani ya gyatsine fuska kamar ya ga "cockroach a zuciyarshi yace "Humm! I can't believe this Illiterate girl she known how to speak English''
Ya dube kujera da ta nuna masa da yatsanta akwai tazara tsakaninta da wance ta ke Zaune yafito da "handkerchief fari kal daga gaban aljihu "black colour coat d'in da yake sanye da ita ya shinfid'a akan kujerar sannan ya zauna ya yi crossing legs nashi yafito da "phone in shi yafara buga "game in crush candy''
Haleesa ta cika ta yi dam! Me wannan mutumin yake nufi me ye laifinshi Haleesa ke yakamata ki fara gaida shi abunda d'ayan 6angare Zuciyata yace da ita kenan......."ina Wuni yaya Habeeb"? tafad'a cikin sark'ewa harafi"
"Ignoring nata ya yi saida d'auke almost 3-4 minutes sannan yace da ban Wuni ba kya gani saida ya furzar da zazzafa iska yacigaba da cewa ke! Wai me yasa a duk lokacin da na zo gidanku sai kin yi "Wasting time in na"?
Numfashi da Haleesa ta sauke yafi a kirga da kyar ta iya controlling in "temperature' ta Co's wannan karo guy nan yakawo ta k'ul tace am sorry Yaya Habeeb wallahi.....
"Shut up please don't give me that fucking excuse yak'arasa magana had'e da cigaba da buga game in shi girgiza kai Haleesa ta yi cike da takaici tafara zance zuci na Shiga uku ni Haleesa wannan wane irin aure ne zan yi"?
"Very slowly yafara magana Kin d'auki kanki Wata tsiya sai kace ana sonki sai wani jiji da kai kike ko kin manta kina gaban Habeeb Lamido ne Wanda ba ya gajiya da furta miki kalma ```Tsana``` amma da yake ke Heartless ce har Wani Jan aji kike yi na kuma San duk wannan abu da kike yi kina yi ne don ki burgeni ni mutum ne kaifi d'aya ban ta6a sauya ra'ayi na musanmman akan abunda nace banaso don karki yi tsanmani in na aure ki wata rana za ki same gur6i a zuciyata tun daga lokacin da kika shigo rayuwata na nemi farin cikina narasa bana sonki wallahi na tsane ki tsanar da bara ta6a gushewa daga Zuciyata yak'are magana had'e da Murmushi.
Tun lokacin da yafara magana kai Haleesa yana sunk'unye a k'asa hawaye na bi kumatu ta, Habeeb ya mik'e tsaye hannunshi guda yana ciki aljihu yanufi inda Haleesa take Zaune daf da ita ya tsaye yad'an rankwafa yace ke!
A firgice ta d'ago tasauke ganinta akan fuskarshi k'asa jure kallon tsanar da yakeyi mata ta yi ta sada kanta k'asa.
Murmushi jin dad'i Habeeb yasaki sakamako hawaye da yagani akan fuskar Haleesa yace you hears all what's am saying right"?
K'asa magana ta yi kawai tad'aga masa kai cikin isa da tak'ama yacigaba da cewa "Don't you think is too early ace kin fara zubar da hawaye ki"?
"Is better ki share hawaye ki saboda bai kamata kifara zubar da su tun yanzu domin ina da buk'ata su a gida na Haleesa tacigaba da share hawaye ta masu masifar Zafi da k'ona Zuciya.
"Habeeb ya ja tsoki had'e da cewa kina da aiki yarinya ya yi dialling number Bala yak'ara a kunnenshi "Hello! Bala wai me kike yi ne da har Yanzu ba ka k'araso ba"?
"Boss ina k'ofar gida nufina na dan ba Ku wuri za ka fi jin dad'i sakewa Ku sha fira
Kai! Banaso shirme banza da Wofi na baka _3 minutes_ ka shigo ko nayi maka abunda ba kayi tunani ba yana k'are magana ya yi hanging up"
Haleesa ta sa gefen hijab d'inta ta goge hawaye ta "Bala yashigo had'e da sallama yadire wani k'aton kwali had'e da farar Leda Habeeb ya dube Bala yace na ba ka "5 minutes kayi Mata bayani abunda ke ciki ni ina k'ofar gida kuma karka sake ka wuce time d'in na ba ka yaficewar shi batare da ya dube inda Haleesa take Zaune.
Bala yace ranki yadad'e dama "invitation card's ne mu kawo miki ga kuma waya nan akwai sim card a ciki had'e da numbers in "boss duk abunda Ku ke buk'ata Ke da k'awaye ki a lokacin biki sai ki kira "boss gobe insha Allah Zan zo na fita da Ke 'kawayeki Ku kai wa 'yan uwa da abokai arziki katin gaiyyata
[11/10 7:01 pm] Jeeddah Aliyu🌹: Har Bala yadasa aya a zance shi Haleesa bata ce komai ba gani ta yi shiru yasa yace ranki yadad'e kin yi shiru ba ki ce komai ba"?
Saida tasauke Numfashi daga bisani tace Zai fi kyau kayi min Serving in number domin bana tunani zan iya "calling in wani''
"Bala d'an murmusa yafito da Biro daga gaban aljihu shi ya rubuta number shi akan kwalin da yashigo da shi ya yi mata sallama yafice.
Saida Haleesa ta share tsawon "10 minutes kafin tashiga cikin gida kaitsaye tashiga d'akin Ammi ta ajiye kwalin hannunta bata ce da Ammi komai ba ta nufi d'akinta.

```WASHE GARI ```

Tun misali k'arfe 10:30am Bala ya zo yadauki Haleesa da k'awaye ta suka tafi raba "invitation saida suka share kwana ki 3 suna raba invitation tun safe in suka fita sai da yamma lis suke dawowa.

```ON TUESDAY ```
Chapter 32 · 0% Book details