← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 95

Sashe 25

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ki daina ya6o d'an uwanki a wurina saboda hakan bashida amfani a tare da ni, zainab tarik'o hannu Hannah tace tashi mu je kiyi alwala Hannah ki kyale Haleesa saboda a halin yanzu bata cikin haiyyacinta batare da Hannah ta furta uffan ta bi bayan zainab bayan madam ta gama sallah tanufi gadon Ammi inda Haleesa take kwance tadinga rarrashinta har tayi nassara shawo kanta tadaina kuka, sai misali k'arfe _8:20pm_ madam Hindu tabaro gidansu Haleesa.

```9:30pm```

Madam Hindu na kishigid'e a had'ad'e parlour yayinda Hannah take zaune a gefe tana chat a "phone d'inta, Habeeb ya yi sallama had'e da shigowa parlour kaitsaye yanufi kujera da madam Hindu take zaune ya zauna kusa da ita had'e da daura kanshi a kafad'arta, ya wani narke sai kace 'karamin yaro madam tashafi sumar kanshi cikin kulawa tace da alama _son_ ka kwaso gajiya ga shi inaso zan yi magana mai matuk'ar mahimmanci da kai"?
"Don't worry about me mom ba wani gajiya a tare da ni da bara nayi fresher up nadawo mu yi magana ya mik'e tsaye cikin tsokana yace Allah yasa kud'i ne za ki bani domin nasanki da kyauta tun da na shigo parlour nan naga fuskarki shinfid'e da farin ciki naji a jikina babba kyauta za ki yi min ni kadai batare da Hannah ba
Hannah ta kyalkyale da dariya tace kai yaya Habeeb Sam baka rabo da abin dariya to abunda yafi kud'i ne mommy za ta baka
Murmushi yayi yana shafar sumar kanshi da gaske ne sweetheart za ki bani abunda yafi kud'i"?
Haka ne son ka je ka yi wanka kadawo ka ji babbar kyautar da zan baka.
"Your wish is my command sweetheart yafad'a had'e da juyawa ya haura upstairs Hannah tace wannan kyautar "special ce mu biyu za mu raba batare da yajuyo ba yace karya ki ke yi yarinya ni kadai mom za ta ba.
Mom kina gani yaya Habeeb zai amince da za6inki kuwa"?
Ajiyar zuciya madam ta yi daga bisani tace bana tunani zan same matsala daga wurin Habeeb saboda tun yana yaro ba mu ta6a samu sa6ani ra'ayi duk abunda nakeso shima yana sonshi, so bana tunani akan wannan za'a same matsala, kuma da bakinshi ya sha fad'a min cewa na nemo mishi mata kin ga kenan fad'uwa ce ta zo dai-dai da zama.
Habeeb na shiga bedroom ya cire kayan jikinshi yasaka rigar wanka {bathrobe} yashiga bathroom bayan yafito daga wanka, farar jallabiya yasanya yafice daga bedroom d'in madam da Hannah na zaune inda yabarsu a zaune, tun kafin ya zauna yace Hannah ki je kitchen ki dauko min "soya milk mai sanyi Hannah ta mik'e tanufi kitchen yayinda ya mayarda ganinshi wurin mom yace "sweetheart ga ni nadawo madam ta yi murmushi tace son lokacin ya yi da za ka aje iyali domin zamanka haka bai dace ba
"Hannah tadawo hannuta rike da kwalin soya milk had'e da "handle glass cup ta mik'a masa harara ya galla mata yace bara ki iya zuba min bane"?
Hannah ta yi murmushi ta bud'e murfi kwalin soya milk d'in ta zuba masa a cup ta ajiye kwalin bisa stool ta koma wurin zamanta ta zauna yayinda madam tacigaba da cewa a dalilin haka yasa na nemo maka yarinya mai hankali da natsuwa babban abunda yak'ara Jan hankalina agareta kyakyawar tarbiyya da ta ke da ita.
Tun lokacin da madam tafara magana Habeeb yake kallonta had'e da snipping d'in soya milk d'insa, gani ta dasa aya a zanceta ya yi d'an bazawari murmushi kamar mai rad'a yace mom kina nufi aure za ki yi min"?
Kwarai kuwa _son_ nagaji da gani ka haka domin basan har wane tsawon lokacin za ka dauka kafin ka nemo wance ka ke so shiysa, na nemo maka wance ta dace da kai kuma na tabbata za ka so ta.
Numfashi yasauke yace mom wacece wannan yarinya da kike ta faman zuzutawa"?
Haleesa k'anwar Juwairiyya matar masa'ud manager ita ce yarinya da na za6a maka kuma nasan za ka yaba da za6i na.
Habeeb ya zaro ido soya milk d'in da ya kur6a baisan lokacin da yahadiye ta da k'arfi ta sark'e shi yafara tari kamar ranshi zai fita madam da Hannah sai faman sannu suke masa da kyar tari ya tsaya yad'ago jajaye idanushi yasauke su bisa fuskar mom d'in tashi cikin yanayi na tashin hankali yafara magana mom duk wad'anan ababbe da kika lissafa akan wannan yarinya ni ba ko d'aya da nagani a tare da ita asalima banta6a gani, mahaukaciya irinta ba wai ina kushe za6inki bane mom ki yi bincike akanta kafin ki yanke hukuncin aura min ita yak'arasa magana tamkar zai fashe da kuka.
"madam Hindu ta gyara zamanta had'e da rik'o hannunshi "Son Haleesa batada matsala duk wani bincike da addini ya yarje ayi kafin anemi aure nasa ayi min akanta da iyayyeta kuma, gaba d'aya su sun same kyakyawar sheda a wurin jama'ar gari....
[22/09 4:08 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```54```

A matsayina na mahaifiyarka ba yadda za'ayi na za6a maka abunda zai cutar da kai Haleesa na matuk'ar bani tausayi kai kanka in ka ji labari rayuwarta za ka tausaya mata, nan take madam ta zayano masa labari rayuwa Haleesa tacigaba da cewa _son_ nasan kana da kyakyawar zuciya da tausayi dalilin da yasa ka aure salma kenan Haleesa ta cancanta ka tausaya mata ka aure ta domin tana buk'atar kulawa ka yi tunani halin da 'yarka kwara d'aya tal take ciki ka gano cewa kana buk'atar Haleesa a tare da kai amma tun da bakada ra'ayi akanta ba zan tilassa ka ba saidai basan ta wace hanya zan bi domin ba iyayyeta hank'uri"
Cikin sark'ewa halshe yace akoda yaushe banida za6i da ya wuce naki sweetheart duk abunda kike so nima ina sonshi akan wannan bara mu ta6a samu sa6ani ra'ayi, farin ciki na shine na kasance d'a mai biyayya a gareki don haka na amince da za6inki ni kuma haka tawa k'addara ta take bara ta6a samu za6ina.
Tsanani tausayi farucinshi Yakama madam amma kuma ba taji za ta, iya chanza ra'ayinta akan Qudirinta"
parlour ya yi tsit kamar ba masu numfashin a ciki baka ji komai sai 'karar sautin tv madam ce ta yi yunk'uri kawo karshen shiru nasu ta hanyar fad'ar Allah ya yi maka albarka Habeeb biyayya da kake min kai ma Allah yabaka 'ya'ya da za suyi maka fiye da wance ka yi min.
_Ameen sweetheart_ yafad'a had'e da kwantawa akan cinyoyinta ya lumshe idanu.
A hankali madam ta ke shafar sumar kanshi cikin lafazi mai sanyi ta kira sunanshi Habeeb!
"Humm! Yafad'a a kasalance.
Banaso wannan al-amari yadauki dogon lokacin, saboda haka ka Ware _time_ ka je gidansu Haleesa ku fahimce juna ka kuma gaida iyayyeta, daga bisani na sanarda da Alhaji bello su Kai kud'in gaisuwa.
Har madam ta dasa aya idanushi na lumshe, yace kina nufi zance zan je"?
Kwarai kuwa ko ba za ka iya zuwa bane"?
Ni na isa nace bara iya zuwa saidai kunya nakeji tun da na zo duniya banta6a tsayuwa da wata 'ya mace da sunan zance Allah kuwa sweetheart kunya nakeji yak'arasa magana yana yatsine fuska.
Madam ta yi "dumm! Tana shafar gashi kanshi daga bisani tace ka daure my son ka je ta hakan ce za Ku fahimce juna kuma iyayyeta za su fi gansuwa su gano cewa da amincewarka za ka aure 'yarsu.
Habeeb yak'ara ya mota fuska da alamu yashiga sark'ak'iya da kyar iya bud'a baki yace shikenan mom in nasame lokacin zan je'
Wane irin in kasame lokacin son kawai gobe ka je
A kid'ime Habeeb ya mik'e zaune yace mom gobe fa kika ce"? Gaskiya gobe "I don't have time but I promise you next week zan je
"Next week ya yi nisa son" ranar Saturday kana free saboda weekend ne ba aiki ka yi k'ok'ari ka je
Tamkar zai fashe da kuka yace na ji
Madam ta yi murmushi had'e da shafar gefen fuskarshi da bayan hannunta tace Haleesa yarinya ce tagari za ka ji dad'i zama da ita.
"For God sake mom kidaina wannan magana haka nan nace na amince zan aure ta cigaba da maimaita zance yarinya nan za iya haddasa min "headache yana k'arasa magana ya mik'e tsaye Hannah ta kyalkyale da dariya tace yaya Habeeb zan yi maka "escort na kware da iya tsara zance kaitsaye zan tsara maka ita nan take ta zurma a kogin sonka.
Wawan tsoki Habeeb ya ja cike da haushi had'e da takaici ya haura upstairs a zafafe ya murd'a handles yashiga bedroom yafad'a bisa bed yasaki huci bakinshi na fitarda iska mai masifar zafi hannaye shi ya daura ya yi pillow ya 'kurawa ceiling ido tamkar yana karanta wani abu a wurin daga bisani yasauke numfashi mai karfin gaske, yafara zance zuci lallai yarinya nan sai ta yi "regretting na shigowa rayuwa ta saboda tarasa masoyinta don kawai ina da sunanshi shine take bibiya na har ta yaudare mom da ladabi ta na karya tayi sanadi da mom ta had'ani aure da ita wallahi sai ta yi danasani sani na a rayuwa domin ba zan ta6a Maye mata gurbi tsoho masoyinta sai na had'a ta da hawan jini sai na wulaqantata irin wulaqanci da bata ta6a gani a rayuwarta.
A 6angaren Haleesa kuwa tana gani madam Hindu ta tafi tasake bud'e sabon babi na kuka Ammi ta watsa mata kallon mamaki tace Haleesa kukan me kike yi"?
Haleesa ta mik'e zaune tana shar6e hawaye tace wallahi Ammi banaso Habeeb Lamido ba zan iya zaman aure da shi har abada ba zai ta6a maye min gurbi yaya Habeeb asalima ni tsoro shi nake ji.
Ammi da zainab suka yi sororo suna duban Haleesa duba na rashin fahimtar inda kalamai ta suka dosa.

Jeeddah Aliyu 🌹
[30/09 2:48 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [28/09 10:45 am] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```55```
Chapter 25 · 0% Book details