← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 95

Sashe 37

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haleesa ta falka daga bacci a gauggauce ta gyara "bedsheet ta jona "burned a "socket ta zuba turare wuta d'akin ya gume da sanyaye k'amshi daga bisani tashiga wanka bata d'auki dogon lokacin ba tafito ta shirya cikin atamfar "Super Sheraton blue da touch in pink ta yi matuk'ar kyau tafito amarya sak batare da ta daura Dan kwali ba ta yane kanta da d'an siriri "veil pink colour tanemi gefen bed ta zauna ta rakka d'an uban tagumi k'ugi da cikinta yake yi yasa babu shiri ta mik'e ta murde handle ta bud'e k'ofa kad'an ta lek'a wayam ta hangon parlour ba kowa a hankali take sand'a kamar barauniya ta dafe da kwakwaso tana kallon tsarin parlour ya yi matuk'ar yi mata kyau "everything's da ke parlour red & yellow colour ne tasauke numfashi a baiyane tace "amazing that's my favourite colour" daga bisani tanemi d'aya daga cikin "Royal chairs d'in da suka k'awata parlour ta zauna tunani take ina za ta nemo abinci za ta sakawa hanjinta tun, kafin yunwa da takeji ta yi mata illah 'kamshi turare "intense men da ta shak'a ya haddasa mata fad'uwa gaba karar "footsteps da taji ana saukowa daga upstairs yak'ara jefata cikin matsananci tsoro cikin d'an k'ank'ani lokacin zuciyarta ta motsa yayin da hankalinta yatashi tasoma fargaba had'uwa da Habeeb Lamido ko wace irin tarba zai yi mata sanye yake ciki "three quarter red colour da white armless shirt k'afarsa rufe cikin white combat boot hannaye shi na zube cikin aljihu wandon fuskarshi a had'e yak'araso cikin parlour a wulaqance ya dube inda Haleesa take zaune ya Ja 'yar siririya tsoka yanemi nesa da ita ya zauna tsawon "4-5 minutes da zaman shi ya d'ago ya kalleta har yanzu kanta na k'asa tana wasa da yatsuta ranshi ya yi mugun b'aci wannan 'yar k'auye tana nufi bara ta gaishe ni ba yafad'a a cikin zuciyarshi Cike da izza yace ke! A rud'e Haleesa tad'ago idanuta suka firfito alama tsoro ke! Ba da ke nake magana ba"?
"Na"am ta Fad'a tsoro shinfid'e a fuskarta kina nufi bara ki zo bane"?
Jiki na rawa ta mik'e tanufi gabanshi tayi tsaye had'e da sada kai k'asa ta k'asan ido yake kallonta kamar Mai rad'a ya furta ba ki iya gaisuwa ba koh"?
Sam Haleesa ba tayi zato jin wannan kalma daga bakinshi ba ta hadiye yawu da kyar tace na iya mana''
Yad'ago eye's in shi yana tsotsa bakinshi kamar mai tsotsa sweet daga bisani ya ja iska kamar Wanda ya ci yaji da sauri Haleesa tadauke kanta da bari kallonshi "tsabar iskanci ne da yacika miki ciki yasa kika kasa gaida ni koh"?
Girgiza kai Haleesa ta yi
"A fusace Habeeb yace you are not dump or deaf so open your bloody mouth & talk to me"
Cikin sarkewa halshe tace dan..Allah.. Yaya Habeeb ka yi hankuri ni banaso fitina
Ya galla mata harara kina nufi ki ce ni ne fitinane lallai kuwa zan nuna miki cewa ni cikkake fitinane, ne ya mik'e tsaye saida ya yi mata kallon wulaqanci yace "Follow me
Haleesa tadafe k'irji ta zaro ido tace na'am"
Ko kallonta bai yi ba yanufi wata k'ofa ta glass cikin sassarfa ta bi bayanshi yana shiga tana shigowa batare da ya dube ta ba yanufi gym mat machine" yasoma motsa jikinshi sai uban gumi yake had'awa yayin da Haleesa tacigaba da tsayuwa jin ta yi k'afafuta sun fara d'auke wuta ta yi nufi ta zauna akan d'aya daga cikin chair's d'in wurin tun kafin d'uwawu ta su kai bisa kujerar yadaka mata tsawa ke! Wa ya baki izzini zama"?
A tsorace Haleesa ta mik'e chak ta yi narai-narai da ido hawaye suka tsiyayo mata wani irin dad'i ya lullu6e Habeeb Lamido sakamako hawaye da yagani sunanta fita daga idanuta, ya wani kada kai cikin d'agawa da nuna isa yace kad'an daga cikin k'anana wulaqanci da kika fara gani daga gareni kafin na fara baiyana miki manya-manya da ke jiranki amma in har kika dinga bin umurni na zan iya rankwata miki saboda ni mutum ne da bayaso shiga harka wani kamar yadda ni ma banaso a Shiga nawa yak'arasa yana Jan iska a zuciya Haleesa tace kai amma guy nan d'an air ne dube yadda yake ja iska kamar Wanda yaci yaji ta sauke numfashi muryarta na rawa tace zan kiyaye da duk wani umurni da za ka dinga ba ni.
Kamar bai ji abunda tafad'a ba ya yi switch off in machine d'in yasauko yadauki fari towel ya goge gumi fuskarshi har zuwa dokin wuyanshi yajuya yafice Daga room d'in da kyar Haleesa ta ja k'afutata kafin tak'ara sa tuni har Habeeb yarufo k'ofar ta tura k'ofa amma ta ji ta gam tacigaba da tura k'ofar iya k'arfinta har tagaji ta yi tsaye turus wani irin gumi ya tsiyayo mata me Habeeb yake nufi na rufe a cikin wad'annan k'arafe dole tanemi wurin ta zauna a hankali take rera kuka ga wani irin murd'awa da cikinta ya ke yi ta mik'e da kyar gaba d'aya jikinta ya jik'e da zufa tasoma dukan k'ofar da k'arfi had'e da kiran sunan Habeeb tsawon lokacin ta d'auka a haka daga karshe ta sulala k'asa tadafe kanta tasoma tambaya kanta, wannan wane irin aure ne rana farko na a gidan Habeeb na fara fuskantar k'alubali Habeeb yana sane yarufe Haleesa saboda yasan bara ta ta6a iya bud'e k'ofar domin k'ofar da code take using saida 6ata "long time a bathroom duk don ya wahalarda Haleesa ya shirya cikin brown Jean's da yellow t-shirt yasauko k'asa fuskarshi a murtuk'e ya bud'e ta Haleesa nagani K'ofa ta bud'e tak'ara fashewa da kuka Habeeb ya ja tsoki ya yi tafiyarshi tafito tana Jan k'afa ta hango shi a dining area peter yana saving in shi nan take yunwa da takeji tadawo sabuwa wata zuciya tace ki je Haleesa ki cika cikinki saboda bara ki iya cigaba da jure zama da yunwa "with full confidence tanufi table d'in a lokacin har Habeeb yafara cin abinci shi peter ya ja mata kujera ta zauna ya yi mata saving tsanani yunwa da takeji yasa tafara cin Chip's bata ko taunawa sosai take hadiyewa abunda ya yi mugun ba wa Habeeb haushi ya tsane ya ga ana cin abinci haka domin shi komai a yangance yake yi da k'arfi ya jefa spoon in hannunshi cikin plate yature kujera ya yi tafiyashi Haleesa ta bi shi da kallo ta tabe baki saida ta yi narkat sannan ta tashi tanufi cikin "main parlour Habeeb na hakice akan two star fuskar nan a had'e kamar tsoho soja cikin sanyin jiki Haleesa ta zauna a k'asa "rugs carpet ta sunkuyar da kai a fakace Habeeb yake satar kallonta, Haleesa tad'ago da sunan ta sace kallonshi karaf suka had'a ido ya galla mata harara ya kuma k'ara d'aure fuska da sauri ta d'auke idanuta phone in shi ta yi ringing ya yi picking _mtwww....ya ja tsoki look Mus'ab ni fa banaso iskanci in za ka shigo to bissmillah in kuma za ka tsaya munafuci ka ne ka kyalle khaleel ya shigo_ ya yi hanging up
A zuciya Haleesa tace kai wannan anyi masifafe, da kowa masifa ya ke"
Mus'ab da khaleel suka shigo sai fama kyalkyatar dariya suke kowanesu yanemi wurin zama Haleesa ta gaida su cikin tsokana Mus'ab yace Amarya bakya laifi ko kin kashe d'an masu gida murmushi yak'e Haleesa ta yi tak'ara sada kai k'asa Habeeb ya ja tsoki cike da takaici yace sanin kanka ne banida d'a a gidanan bansaniba sai in kai za ta kashe Mus'ab ya yi dariya yace to ae ni ba d'a ka bane a yatsine Habeeb yace wannan kuma matsalar ka ce "Haleesa ta mik'e tsam tanufi bedroom d'inta Mus'ab ya gyara zamanshi yace Habeeb yakamata ka sakawa zuciyarka salama ka, zauna lafiya da yarinya nan domin ni banga wata matsala a tare da ita, Habeeb ya yi tsoki had'e da mik'ewa khaleel tashi mu tafi banida "time in sauraro surutu wannan duk yadda Mus'ab ya so ya lurar da Habeeb amma yak'i bashi had'in kai.
Bayan fitar Su Habeeb Haleesa tafito parlour bata jima da zama ba Hannah tashigo suka bud'e shafi na fira Hannah tarik'o Hannun Haleesa shawara zan baki Haleesa ba wai a matsayina na k'anwar mjinki ba matsayina na k'awarki kuma 'yar uwarki a musulunci Haleesa ki yi hankuri ki bi mijinki sau da k'afa domin samun aljannarki kada ki biyewa ta yaya Habeeb domin shi mutum ne mai wuyar sha'ani a wani gefe kuma yana da matuk'ar saukin kai, Haleesa ta yi murmushi na gode da wannan shawara ta ki Hannah zan yi k'okari na rinjaye zuciyata na bi yaya Habeeb insha Allah ba za'a ta6a samun matsala daga gareni zan bi shi ta yadda yakeso, sai misali k'arfe _2:30pm_ Hannah ta yi sallama da Haleesa.
Chapter 37 · 0% Book details