← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 95

Sashe 39

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri-sauri Haleesa ta sauke numfashi ta hadiye yawu Habeeb yak'ara dank'e yatsunta yana wani lumlumshe idanu "am sorry baby bara k'ara fita na barki ke kadai kinji"?
Haleesa tayi murmushi yak'e tasada kai k'asa zuciyarta cike da mamakin Habeeb lalle Habeeb Lamido cikakken d'an duniya ne, kallo d'aya tayi mashi ta gano duk abin da yakeyi mata"pretending ne, muryar imaan ce ta katsi mata zance zuci "Daddy aunty Maryam tace "new mommy da ka kawo min 'yar talakawa ce bata dace da kai ba kum..."shut up Imaan bana hanaki irin wannan surutu maras kan gado ke fa da bakinki ki ka ce kinaso na kawo miki "new mommy ba"?
"Imaan ta gyad'a kai
Duk ranarda na K'ara jin irin wannan magana a baki ki bara k'ara siya miki "Ice cream
Rau-rau da idanu Imaan ta yi kamar za ta yi kuka tace, "Daddy na daina Habeeb ya shafi cheek in ta ya juya wurin Maryam da ke tsaye tana fama da tafarfasa zuciya ya dank'ara mata harara mai dauke da gargad'i ya mik'e tsaye ya sunkuce Imaan ya dube Haleesa yace baby in kin sallame visitors in ki ina jiranki a sama bai jira amsar da Haleesa za ta bashi ya haura upstairs cikin d'aga murya Maryam tace kadawo da imaan tafiya za mu yi batare da yajuyo ba yace za ki iya tafiya Co's imaan tadawo gidan ubanta
A tsoroce Maryam tace wannan wane irin d'aye hukunci ne yaya Habeeb"?
Cikin isa da tak'ama yace saboda ni nake iko da imaan
Maryam tak'ara harzuk'a Duk tsawon wannan lokacin da imaan ta dauka a tare da mu baka ta6a nuna kanada iko da ita sai yanzu ba yadda za'a yi muna raye imaan ta zauna a hannun kishiya uwa in har kai baka sonta to mu munasonta matuk'ar ka ga imaan ta zauna a gidanan ka tabbata cewa ka rataya mini igiyoyi aurenka Inda har hakan bata kasance ba wallahi imaan bara ta zauna a hannun wannan 'yar Matsiyata, Habeeb ya bud'e baki da d'ibin mamaki yana kallonta cike da takaici yadawo cikin parlour ya sauke Imaan yanuna Maryam da yatsa yasoma magana cikin b'aci rai banaso iskanci banza da wofi maryam har ni za ki fadawa magana banza zai fiye miki alkhairi ki tattara k'afafu ki ki bar min gida tun kafin ki kaini bango nayi miki rashin mutunci nasha Fad'a miki bana sonki na tsane ki da yake ke dak'ik'iya ce kin kasa gane hakan zeely ta janyo hannun Maryam tace zo mu tafi Maryam sannu-sannu bata hana zuwa saidai ajima ba'a kai ba lokacin na zuwa da za kiyi fatali da gwannati 'yar Matsiyata ki mulki yaya Habeeb son ranki "Habeeb yak'ara harzuk'a yanufi wurinsu da gudu suka fice daga parlour da Ku tsaya na nuna mu Ku yadda za Ku yi mulki na 'yar Matsiyata nan da Ku ka rena tafi Ku daraja da k'ima a wurina'yan iska tarkace tsiya marasa tarbiyya, kuma duk ranarda na k'araji d'aya daga cikinku ta kira matata da suna 'yar Matsiyata dai na gwaje mata baki Haleesa ta tsura masa ido tana mamaki yadda kalamai nan suke fitowa daga bakinshi yana juyowa suka had'a ido ya watsa mata harara ke! daina kallona kin wani tsareni da idanu sai kace mayya da sauri ta sada kai k'asa yak'araso daf da ita saida yak'are mata kallon wulak'anci ya ja tsoki ke! Ina son ki bud'e fakanfakan kunneye ki masu kama da na zomo ki saurare abunda zan Fad'a miki domin banaso asami akasi ki ce baki fahimce abunda nake nufi duk magana da Habeeb yakeyi Kai Haleesa na sunkuye tana murza zobe yatsanta saida yaja iska sannan yacigaba da cewa ina matuk'ar son imaan banida buri da yawuce naga rik'o ta yadawo hannuna musanmman da na fahimce irin rik'o sakainiya kashi da akeyi mata a duk lokacin da na je ganin Imaan raina na matuk'ar sosuwa a yadda nake tararda ita Sam bata samu kyakyawa kulawa gaba d'aya tarbiyyar ta na wurin 'yar aiki Imaan na buk'atar wance za ta maye mata gur6i mahaifiyarta da tarasa, dalili da yasa lokacin da mom ta yi min tallarki na amince zan aure ki, ina fatar za ki rik'e Imaan da amana sai lokacin Haleesa tad'ago tasauke ajiyar zuciya, cikin sanyi murya tace insha Allah zan bawa Imaan kyakyawa kulawa bara ka ta6a samu na da aikata ba dai-dai a gareta ae d'a na kowa ne yadda zan kula da 'yar da na haifa haka zan kula da ita tak'arasa magana had'e da sada kai k'asa "Habeeb Lamido ya ja wawa tsoki ya wani zare idanu ke! Ba dai ni kike tunani zan miki ciki har ki haihu"?
A tsorace Haleesa tak'ara d'agowa tasauke "eye's ball d'inta akan fuskarshi yadda ya murtuk'e fuska ya yi mugun kad'a anta cikinta cike da takaici yace kidaina yaudara domin ni ba abunda zan tsinta a jikinki yanuna jikinta da yatsa shi yana yatsina yacigaba da cewa na mafalki ma da kike samu da ina da yadda zan datsi shi da tuni na taka miki birki da fatar kin fahimce inda na dosa"?
" Batare da Haleesa ta fahimce abunda yake nufi ba ta gyad'a kai ya tabe baki had'e da cewa ki bani aro hankalinki na karato miki dokoki zaman gidana idan kika kiyaye su za ki ji dad'i zama da ni doka ta farko na tsani k'azanta shiyasa bana sha inuwa d'aya da k'azami in har bakida tsafta ki fara koyo in kuma kinada sai ki k'ara bisa ga wance kike da saboda ni mutum ne mai tsanani kyakyame gaske doka ta biyu ya zame miki dole duk wani abu da kika yi amfani da shi ki mayarda shi a muhallinsa hatta da "toothpick yana da muhallinsa a gidanan, sai kuma doka ta uku dole ki girmama ni domin ni mutum ne mai matuk'ar so girma daga yau za ki dinga gyara mini sitting room da kuma bedroom dole ne kullum ki wanke mini bathroom amma ban amince ko "Noodles ki dafa da sunana, da sauri Haleesa ta dube shi fuskarta d'auke da d'inbi mamaki yak'ara zare mata shegu idanunshi masu masifar tsorata ta kidaina mamaki domin ba ki kai matsayi da ki za ki dafa mini abinci shi ma gyara rooms in da kika ji nace kidinga yi min ba wai kin Kai matsayin shiga d'akina bane kawai banaso kidinga cinye min abinci a wofi sai ki kiyaye dokoki da na shinfida miki domin shine kwaciyar hankalinki a gidanan ya sunkuce Imaan suka haura upstairs yabar Haleesa sake da baki hawaye masu masifar zafi suka wanke mata fuska tasaka bayan hannunta ta goge, bayan "10 minutes da fitar Habeeb sai gashi yadawo yana rik'e da hannun Imaan jin karar footstep in shi yasanya Haleesa tajuya yasauya kaya zuwa dark blue Jean's da white shirt ya sha stocking da belts mai tambari D&G ko kallon gefen da Haleesa take zaune bai yi ba yafice yayin da Haleesa ta bi su da kallo haka tacigaba da zama a parlour tana sak'e-sak'e kiran sallah magarib ne ya mayarda ita bedroom in ta ta yi wanka had'e da alwala ta yi sallah tana gama sallah tasoma lazimi har akayi kiran sallah isha'e ta mik'e ta gabatarda sallah bayan tagama sallah tanufi "dressing mirror ta yi simple make up tasanya yaloluwa night gown pink colour ta fashe jikinta da designer perfume ta tufke gashin kanta da k'ato ribbon pink colour kaitsaye tanufi downstairs parlour peter ta hango a dining area yana jera abinci a table tanufi wurinshi peter na ganinta ya rusuna ya gaida ta cikin sakin fuska ta amsa masa ya ja mata kujera ta zauna cikin gur6ataciya hausar shi yace mah me za'a zuba miki"?
Haleesa ta yi shiru daga bisani tace zan yi serving da kaina za ka iya tafiya Peter yajuya yafice ta bud'e warmers pounded yam ta zuba had'e da egusi soup ta sha smoked fish tana ci tana gyada kai alama abinci ya yi mata dad'i bayan ta cika cikinta tanufi parlour ta kwanta akan 3 star tasoma tunani wance irin rayuwa za ta yi da Habeeb Lamido.

_9:00pm_
Chapter 39 · 0% Book details