Sashe 46
Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
zip d'in rigarki a bud'e"?_ _ko kinaso ki nuna min wannan abun ya Shafa mole in bayanta"?_ _Ko kuma colour din brazier da kika saka ki keso nagani"?_ Haleesa tarasa bakin magana sai fama girgiza kai take Abunda yak'ara harzuk'a Habeeb yadaka mata tsawa ke! Bara ki bud'e baki ki bani amsa ko sai na yi miki wulaqanci"? Cikin rawar murya Haleesa tace duk abubuwa da ka lissafi banida manufa da su kawai zip d'in ne yak'i rufewa tak'arasa magana had'e da sunkuyar da kai "Habeeb ya yi shu'umi murmushi yad'ago fuskarta yace karki yi min k'arya Co's nasan duk wannan abu da ke yi kina yi ne saboda ni kuma kin yi a banza domin ni ba burgeni za ki yi, yafisgo ta da k'arfi ya murd'e hannayeta da hannunshi d'aya yasaka d'aya hannunshi ya rufe mata zip yadaura bakinshi dai-dai kunnenta ya rad'a Mata wannan ya kasance na farko na karshe da zan K'ara ganin zip d'in rigarki a bud'e ya wulgar da hannunta da k'arfi ya duk'a ya kwashe file's d'in da ta zubar yafice Haleesa ta zauna k'asa dabass tadafe saitin zuciyata da ke barazana fita daga k'irjinta saida ta share tsawon _10 minutes_ ta na jiyar zuciya da gangar jikinta daga bisani ta mik'e jiki a sa6ule tafita tun kafin ta k'arasa saukowa ta idanuta suka hasko mata Habeeb tsaye yabawa k'ofa baya hannunshi guda cikin aljihu wandonshi d'aya hannu yana rike da waya ya kara a kunnenshi, a nutse tashiga parlour Bala da Imaan na zaune Imaan nata zuba masa surutu yana dariya Bala yace amarya kina fama da surutu Imaan koh"? Haleesa ta yi murmushi Habeeb ya kamalla wayar da yakeyi fuskar nan a had'e yace Bala tashi mu tafi in ka biyewa Imaan za Ku kai gobe tana zuba batare da tagaji bakinta Sam baya ciwo Bala ya yi dariya yasauke Imaan yayin da Imaan tasaka rigima "Daddy zan bi ka "Habeeb yarik'o hannunta my angel office zan tafi ki zauna ki taya aunty hira zan siyo miki ice cream kinji"? Imaan ta washe hak'ora "Daddy hadda chocolate da teddy da Ku....da sauri Habeeb ya katsita my Angel irin wannan lissafi ba ko numfasawa to naji duk abunda kike so zan siyo miki "Uncle Bala karka manta da goriba na Bala ya yi dariya yace to babyn Daddy insha Allah ba zan manta ba tak'ara juyawa wurin Habeeb Daddy yaushe za ka fiddo min Rahul da Rita mu yi wasa Habeeb yatafe goshi surutu Imaan yafara kai shi bango ya sumbace kumatu ta yace Bala mu tafi yajuya da kyar Haleesa ta iya sarafa halshenta ta furta _adawo lafiya Allah ya tsare_ Ya juya ya galla mata harara da sauri tadauke fuskarta. Kamar jira take su fita ta mik'e tanufi dining table tacika tumbinta Imaan tadame ta da surutu _aunty Dan Allah ki kunna min cartoon_ Haleesa ta chanza mata channel zuwa Nickelodeon Imaan tadinga ihu Haleesa na dariya shirme ta daga bisani Haleesa ta kwanta a 3 sitter kwakwalwarta tasoma yi mata backward d'in abunda yafaru tsakaninta da Habeeb a haka baccin ya sace ta, Imaan ta d'auki katuwar tissue tadinga yagewa tana zubarwa ta wargaza wata kyakyawa flowers da ke sama stool ta yi daidai da remote cikin d'an k'ankani lokacin ta sauyawa parlour kamanu yayin da Haleesa batasan abunda take aikatawa sharar baccinta kawai take. Habeeb na fita direct gidan madam Hindu yawuce yana shiga parlour gidan house maids {'yan aikin} suka dinga kwasan gaisuwa, ya amsa adak'ile ya dube yarinye a yatsine yace mom fa"? Tana sama tafad'a cikin rawar murya a natse ya haura stairs cikin sand'a yashiga d'akin madam Hindu na tsaye gaban dressing mirror tana fesa turare taciki mirror ta hango shi yana zuwa ya yi hugging nata yadaura kanshi a kafadarta _Good morning sweetheart_ Madam Hindu ta yi murmushi _morning son me yafito da kai da sanyi safiya nan"?_ Habeeb yak'ara narkewa kamar Imaan cikin shagwa6a yace _just to see you sweetheart are you not happy"?_ Madam Hindu ta girgiza kai son baka girma abunda ka ke yi ko Hannah da take Auta bata yi shi yasake ta ya zauna a gefen bed nafi Hannah matsayin a wurinki domin ita gidan wani za tafi ni kuma _Ina tare da ke_ Murmushi madam tayi ta ajiye kwalba turare ta zauna kusa da shi _ina Haleesa da fatar ba wata matsala a tsakaninku"?_ Ras-ras gaban Habeeb yafadi nan take yafara tunani k'arya da zai sharawa madam ya Wani karkace kai yace.......