← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 95

Sashe 27

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bala yajuya a "sit d'in baya yace "Boss ina muka nufa"?
K'atuwa harara Habeeb ya wulga masa cikin tsawa yace dallah! Malam ka kalli gabanka bara ka iya yi min magana bane sai ka juyo"?
"Sorry Boss Bala yafad'a kaitsaye
Habeeb yaja tsoki saida yagama shan k'anshimsa sannan yafad'awa Bala sunan unguwar su Haleesa Bala yadafe kai yace "Boss tuni na wuce titi da zai sada mu da unguwar yanzu kuma dole sai mu yi round mu koma ainihi hannun mu.
Cike da jin haushin kalamai Bala yace bana son surutu Bala karka dame ni, Bala yagyd'a kai, har suka isa unguwar Habeeb yana zance zuci gani sun iso yakasa koda kwakwara motsi yasa Bala ya yi karanbani kiran sunanshi, "Boss mu iso gidan"
Firgigit Habeeb ya d'ago kamar Wanda yatashi daga bacci yasaki tagwaye numfashin daga bisani yace ina ne gidan"?
"Bala yanuna gidansu Haleesa da yatsashi yace nan ne gidan Habeeb ya zaro golden "eye's nashi tamkar Wanda yaga abin tsoro cikin sark'ewa halshe yace wannan gidan buski shine gidan in-laws d'ina"?
"Kwarai kuwa "Boss shine gidan su aljanarka kasan ranar ni na kawo "Madam sai yanzu nagano fa'idar kawo ta da nayi saboda in katashi zuwa zance ba sai mu sha wahala neman gida, Bala yak'arasa magana had'e da washe hak'ora.
"Habeeb yadafe goshi yana kallon Bala ta k'asan ido jin yakeyi kamar ya shak'e wuyan Bala sai yadaina motsi sannan yasake shi, cike da takaici yace Bala "you are such a fool a rayuwarka ba abunda kasani sai surutu maras amfani, kai yanzu a ganinka na dace da wannan yarinya"?
Bala ya sunkuyarda kai ya Sosa k'eya yace "Boss ina da amsar wannan tambaya amma ina tsoro fad'a saboda banaso ranka yab'aci.
Bala!
"Yes Boss
"ll'l You answer my questions or not"?
"Yes Boss
To kabani amsa na dace da wannan yarinya kuwa"?
Kun dace "Boss tun da ka ga madam ta za6e ta a matsayin matarka to tabbas kun dace saboda ba yadda za'ayi "Madam tayi maka za6en tumu dare amma ka gafarce ni in har na fad'i abunda ya6ata maka rai.
"Numfashin mai matuk'ar zafin gaske Habeeb ya furza yak'ara yadafe goshinshi "oh! My goodness mom she try to kill me" yad'ago ya kalli wata k'atuwar gota wance ke d'auke da ruwan kwatame masu masifar wari yak'ara yadda ganinshi akan Katanga gidan jar k'asa ce duk ruwa sun zaizzaye ta, ya yatsine fuska had'e da toshe hanci, yajuya wurin Bala yace yanzu Bala kana nufi akwai, mutane a gidanan kuma suna rayuwa a ciki"?
"Bala yayi murmushi mai sautin gaske daga bisani yace kwarai kuwa boss suna rayuwa cikin jin dad'i tamkar yanda kake rayuwa.
Habeeb ya galla masa harara yace "ur very stupid Bala taya zakace mutanen da ke rayuwa cikin wannan kango suna jin dad'i tamkar yani"?
Ya furzar da numfashi mai zafin gaske cikin 'kunar zuciya yacigaba da cewa na tabbata daga mai gidan, har iyalinsa idan aka yi masu "Blood test dole a taradda su d'auke da kwayoyin cutar"maleria kalli wannan bala'in da ke kusa dani yanuna 'katuwar gota da ke kusa da su da yatsanshi wallahi ina matuk'ar tausayawa mazauna wannan unguwa.
"Bala ya girgiza kai yace "Boss amfani masu kud'i in har suka ci karo da irin wannan abin tausayi su taimaka"
Habeeb ya yi masa kallon k'asan ido daga bisani ya tabe, baki yace mu yi abunda ya kawo mu "Co's na fara gajiya da zaman wannan wuri mai cike da barazana ga lafiya ta yak'arasa magana yana wani yayatsine fuska"
Kafin Bala yabashi amsa kamal yafito daga cikin gida janye da keke sa, da sauri "Bala ya balle k'ofar mota yafito, ya tsayarda shi, yaro ko maigidanan yana ciki kuwa"?
"Eh yana nan"
Dan "Allah ka yi mana sallama da shi"
"Toh kamal yafad'a yajingine keke sa ya juyawa cikin gida, Bala ya koma wurin mota ya bud'ewa Habeeb k'ofa ya yi k'asa da murya yace "Boss yakamata kafito kafin maigidan yafito Habeeb ya tsuke fuskar ya zuro k'afafu shi k'asa daga bisani gangar jikinshi tafito daga cikin mota, yajigina jikinshi a jikin mota ya yi "crossing hand's d'inshi akan k'irjinshi kamal yafito yace gashinan fitowa'
"Toh madallah na gode aboki na Bala yafad'a had'e da rik'o hannun "kamal, ya sunan ka"?
Sunana kamal"
Kamal amma kai k'ani Haleesa ne saboda naga kun yi kama saidai tafi ka kyau.
Kamal ya yi murmushi yace "Eh yayinda Bala yacigaba da cewa Haleesa tana ciki kuwa"?
"Eh tana ciki'
Har Bala ya bud'a baki da niyar yak'ara watsawa kamal wata tambaya Habeeb yadaka masa tsawa "shut up Bala wai kai me ke damunka ne"?
"Bala ya waro idanu had'e da furta "sorry Boss' a zafafe Habeeb yace "sorry for ur self next in ka k'ara yi min irin wannan shisshigi you ll'l be fired Yak'arasa magana had'e da Jan tsoki yayinda Bala yak'ara shiga firgici, kamal da ke tsaye yana kallon iko Allah har yajuya sai yaji tak'o tafiya Baffa sai kuma, yaja ya yi domin yanaso yasan wannan balarabe daga wance duniya yafito.
Malam Usman yak'araso da sauri Bala yace barka da fitowa yayinda Habeeb yad'an rusuna yace ina wuni"?
Lafiya qalau sannuku da zuwa saidai kuma ban sheda Ku ba"?
Bala yajuya ya sace kallon "Boss d'in shi "Habeeb yad'aga masa gira sannan yajuya wurin Malam Usman yace sunana Bala wannan kuma yalla6ai Habeeb shine Wanda yake neman 'yar wurinka, dama mu zo ne mu gaidaku mu kuma nemi izzini gani Haleesa.
"Har Bala yadasa aya malam Usman yana gyad'a kai daga bisani yace masha Allah yajuya wurin kamal yace kamal shiga gida ka kira babanka Audu, yazo mu yi bak'i bayan shigar kamal gida da kamar "5 minutes" sai gashi yafito tare da malam Audu bayan sun gaisa da Habeeb duk wani tambayoyi da yake zubawa Habeeb Lamido Bala ne yake bashi amsa, saboda gogan naku ko dogon motsi bayaso yi, daga bisani malam Usman ya yi masa iso cikin zaure gidan kamal yadauko tabarma ya shinfid'a mishi, cike da kyakyami Habeeb ya dosana duwawo shi akan tabarma yayinda, malam Audu yacigaba da tambayoyi nashi Bala na bashi amsa, malam Audu ya gansu da amsoshi da Bala yabashi saboda haka suka mik'e tsaye a lokacin d'aya shi da Malam Usman Bala yafito da "bundle na 'yan N1000 na dubu d'ari ya mik'awa Malam Audu yace malam ga wannan asiye goro, cike da mamaki mal Audu da mal Usman suke kallon kud'in da ke hannun Bala mal Audu ne ya yi yun'kuri katsiwa Bala hamzari ta hanyar furta Mun gode kwarai Allah yasaka da alkhairi amma ba za mu kar6i kud'inku ba yana k'arasa magana yafice yayinda Mal Usman ya kira kamal yace zo ka shiga da su ciki su, gaisa da Amminku daga haka bai k'ara furta uffan ba yafice daga zaure..

Jeeddah Aliyu🌹
[02/10 3:22 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [02/10 1:40 pm] J: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```Dedicated```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```57```
Chapter 27 · 0% Book details