← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 95

Sashe 88

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ranar yau ta kasance ranar da za'a yi kamun Hannah su Haleesa manyan k'awaye amarya ansha makeover,ta yi matuk'ar kyau tayi fari tass kamar kata6a skin d'inta Jini ya zubo ga wata 'yar uba 'kiba da tayi ita kanta tana mamakin wannan 'kiba da tayi sai ana washe gari daurin aure Habeeb yadira a Yola lokacin da ya Kira Haleesa ya sanarda ita ya iso ta yi mishi girki mai dad'i zai zo anjima ya ci a rikice tace Dan Allah _my handsome Don_ ka yi hak'uri karka zo saboda banaso mom tagano akwai wata alaqa tsakanina da kai za ta d'auke ni maras kunya.
ran Habeeb ya yi matuk'ar 6aci gani yake yi duk wannan abun da Haleesa take yi tana yi ne don ta k'untatawa rayuwarshi ya tana matsayin matarshi sannan za ta haramta mishi zuwa inda take a bisa wani banza dalilin nata a harzuk'e yace wai Leesa mekika d'auki kanki ne huh"? Ko don kinga ina hauka sonki ne shiyasa ki ke mun yanda ki ka ga dama"? Idan ki ka dama in watani 3 suka cika karki dawo gidana ki cigaba da zamanki wajen sweetheart ki gani zan mutu ne ko zan yi rai batare da ya jira abunda za ta fad'a ba ya kashe waya.
"Haleesa ta yi sororo da waya a hannu tarasa mafita takasa
zaune takasa tsaye bakin rai mijinta takeso gani kamar yanda shima yake da Muradin so ganinta watani biyu kenan rabonsu da ganin Juna.
"Ta rafka tagumi jikinta ya yi mugun sanyi kuka takeso yi amma tana tsoro kad'a wani ya ganta tana kuka ya tambaye dalilin kukan nata saboda gidan cike yake da 'yan biki tana cikin Wannan halin Hannah tashigo tadafa kafad'arta what's wrong Mrs Lamido naga kamar kina ciki damuwa"?
''Ajiyar zuciya Haleesa ta yi NI DA YAYA HABEEB ne yanzu nan muka gama waya kinsan halinshi na sauri d'aukar zafi akan abu qalilan ya isheshi fushi tacigaba da ba wa Hannah labari abunda yafaru a tsakaninsu.
''Tsaki Hannah ta ja yakamata zuwa wannan lokacin Haleesa ki daure ki ba wa mijinki dama ya zo ya ga mom ki koma gidanki kisani duk wannan horo da mom take yi wa yaya Habeeb tana yi ne saboda ke da kin furta kin janye sharad'in naki shikenan nan take za ta amince ki koma amma wannan zaman da ki ke yi anan amfani me yake qara ki da shi"? ba za ki gane kinyi wauta ba sai natafi na barki mom ba zaman gida take yi ba za'a barki gida daga ke sai Housemaid ki bi umarnin mijinki ko don saboda aljannarki kitashi yanzu nan ki shirya kitafi wajen mijinki in kin je can! Kya masa girki duk da nasan ba girki yakeso ba kawai dai yafake da sabara ne ya harbi barewa tak'arasa magana tana dariya.
"Haleesa ta rausayar da kai gefe d'aya to in ba girki yakeso ba me yakeso sarkin fassara"?
''Dariya Hannah tayi Oho! Ni ma bansaniba amma na tabbata amsar wannan tambaya tana bakin _handsome Don_
Mtcww....Haleesa ta ja tsaki ke dai kin zama 'yar iska wallahi tun kafin mu kai ki gidan Mus'ab kin lalace.
"Hannah tak'ara kyalkyalewa da dariya
Hannunta Haleesa tarik'o Hannah please kidaina wannan dariya kinemo min mafita.
"Hannah ta kad'a eyes ball d'inta mafita guda d'aya ce kitashi mu je na yi dropping d'inki wajenshi in yaso Ku nemawa kanku mafita
[21/12 8:10 pm] J: Idanu Haleesa ta zaro cab! da sake wai ayi wa mai dame d'aya sata gaskiya Hannah ba zan iya ba so ki ke mom tagano, ta dinga yi min kallon marar kunya da kawaicin.
"Harara Hannah ta zabga mata wai ke da kin bud'e baki sai kice kunya, kunya shin wai yaya Habeeb ba mijinki bane ko kuma zuwa wajenshi da za ki yi ya sa6awa mahalicinki"?
"A sanyaye Haleesa ta girgiza kai Hannah tak'ara jefata cikin rud'ani ba tunani za ki yi ba kitashi mu tafi, Hannah ta katse Mata hamzari.
Haleesa ta mik'e tsaye to amma kuma Hannah ta ya ki ke gani zan fita gidanan har nadawo batare da tasani ba kina gani har tambayarta nayi zan tafi na gaida su Ammi tace na jira har agama Shagalin bikinki.
''Hannah tace karki damu ni nasan abunda zan yi har ki dawo batare da mom tasan kin fita ba.
"Haleesa ta kad'a kai tanufi trolley d'inta taciro Riga da skirt na Swiss lace red colour mai touch d'in white tacire kayan jikinta tasanya lace d'in rigar ta yi tight d'inta musanman k'irjinta tajuya wajen Hannah tace Hannah dubi yanda k'irjina, yaciko nifa wannan k'iba yafara damu na tak'arasa magana tana yatsina.
''Hannah ta kyalkyale da dariya tace yarinya kinsame lafiya.
Tsaki Haleesa ta ja wane irin lafiya"? Haka kawai mutum yadinga kumburi kamar flour tana magana ne had'e da fesa perfume ta zari white veil d'inta I'm ready mu tafi koh"?
Hannah tace Yeap! Ta wuce gaba Haleesa na biye da ita direct parking lot suka nufa Hannah ta kwadawa sa'eed driver kira da gudu sa'eed yak'araso key d'in wace mota ne hannunka"?
"Na Kia cerato ne"
"Okay bani key d'in
Ciro key d'in daga aljihunshi ya yi ya mik'a mata ta kar6a tanufi wajen motar Haleesa ta bud'e k'ofa tashiga Hannah ta yi wa motar key ta ja suka nufi gate maigadi ya bud'e musu gate suka fice.
"Hannah tajuyo ta dubi Haleesa tace gobe insha Allah nima zan bi sahunku ba za k'ara yi mun wani gani-gani ba tak'arasa magana tana murgud'a baki.
"Tabe baki Haleesa ta yi had'e da cewa Allah ya shirye ki Hannah banta6a gani amarya mai zumudin aure irinki ba kafin Hannah ta bata amsa phone d'in Haleesa ya yi ringing.
"A kasalance ta bud'e purse d'inta taciro wayar gani Wanda ke kira yasa tasaki sanyaye murmushi ta yi receiving call takara a kunnenta ta yi shiru tana murmushi.

_HABEEB_
Chapter 88 · 0% Book details